← Book details Tmw Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 83

Sashe 51

Tmw Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Abba baya nan sai dai ya kirasa ta waya, Umma ce ta kirasa tace in bai tafi ba ya dawo tana son ganinsa.
Da sauri ya koma bangarenta ta na zaune inda ya barta.
Shima sai ya koma ya zauna inda ya taahi Lokaci d'aya yana fad'in"Umma lafiya kuwa?
Kai Tsaye Umma tace"Daman saboda na yi maka mgana ne, kana ganin bai kamata matarka ta can zariya ta dawo nan da zama ba? Gani na yi kai ma ya kamata ka Huta zirga zirgan zai yi maka yawa kaje can kazo nan."
Sadiq ya yi shuru kafin yace"Zata dawo Umma, ammh ba yanzu ba."
Cikin mamakinsa Umma tace"Bangane ba? To meyasa?
Kai Tsaye yace"Saboda ta na karatu, ammh ta kusa gamawa, nima ina Tunanin in tagama ta dawo nan da zama ko can inda na ke aiki."
Umma da sauri tace"A'a ba can ba, nan din dai, in can ka ke so sai dai ka tafi da sultana."
Kallon Umma ya yi, sai dai bai yi mgana ba kad'a kai kawai ya yi kafin yace"to Umma shikenan."
Ita kuma tace hakane saboda bata son su Asim din su yi nesa da ita.
In suka koma Abuja ai sai ta Dade bata gansu ba, kuma yanzu yadda take kaunar yaran nan bata jin ko iyayensu suna da iko a kansu yadda take jin tana da shi.

Daganan Shima gida ya koma sai dai yana ta auna mganar Umma, ya Fahimceta Saboda su Asim ne, shima kuma yana Tunanin haka Siya ta fara zama Gusau in ya samu Ma'aikatansu sun saka hannu a takardan ba su Loan gida da Mota shi sai ya karb'i na gida duk wata za'a rika cirewa a albashinsa.
Gwara dai ya fara natsuwa waje daya shi kanshi ya gaji da duk bayan sati yana Hanyar Zariya ko hanyar Gusau.
Ya kamata ya natsu waje daya ko shima ya samu cikakiyar natsuwar da ya ke fata.
Har daki ya bi Sultana ya yi mata sallama ta na kwance, ko dago kai batayi ba ta amsa masa kamar bata son ta yi mgana.
Shi kuma bai damu kansa ba ya ijiye mata kud'i saman Side drower d'in gadon da ta ke kwance ya ficewarsa lokaci daya yana girgiza kansa, shi a tarihin zamansa da Siya ba tab'a masa irin wannan ba, shi fa a zamantewarsa da Siya sai dai shi ya ji kunya in ya yi mata laifi ammh ita bata taba yi masa laifin da yaji ta bata masa rai ba.
Sai dai abunda ba'a rasa ba, na zamantakewar yau da gobe.
Share Tunaninta ya yi saboda Tuki zai yi kada taje Tunanin ya yi masa ya kara samun matsala.
Kafin ya tashi sai da ya kira Siya ya gayamata zai kama hanyar Abuja cikin yanayin mganarta tace"Assadiq yau da rana kuma zaka tafi?
Kai Tsaye yace"Zan shiga Office da wuri ne Siyata."
Bata damu sai ta kara jin wani Dalili ba, ta shiga yi masa addu'an fatan isa lafiya har ta na kara masa gwarancin su Asim.
Kafin su yi sallama haka ya Dauki hanya cikin Farinciki tuni ya shafe Tunanin Sultana ballatana Sakarcinta.
Sai bayan mangriba ya isa Abuja Abba ya yi ta kiransa yana hanya sai da bayan ya natsa ya yi sallah yaci abinci sannan ya kira shi suka yi mgana.
Bayan nan ya kira Siya ya gayamata ya isa, itama ta na ta kiranshi yace bai Sauka ba.
Umma kuma daman tana tare da Abba domin yaji muryanta Lokacin da suke waya.
Sultana ma ya kirata Saboda ya fita hakkinta kira Biyu sai ana uku ta Dauka tana wani cin mgana shi dai bai Tsaya nuna ya gane fushi ta ke yi ba yace mata ya isa lafiya.
Kawai Ok tace ta kashe wayarta sai ya yi Sororo a fili ya Furta"Yarinyar nan ta yi nisa."
Danne bacin ransa kawai ya yi saboda hakane ma sai kawai ya Kira Tahir ai sai yaji Tahir na amfani da wayar. sabodq yakuresa yasa ya yi ta kara kiransa wajen sau biyar duk bai gama wayar ba, wajen awa daya sannan sai gashi ya Biyo kiran Sadiq din yana Dauka yace"Wai lafiya ka ke ta min kira ba daga kafa?
Sadiq yace"Allah ya baka Hakuri ai bansan ka fara Serious Soyayya ba ne."
Sai Tahir ya yi shuru bai yi mgana ba, Sadiq ya sha Mur kafin yace"Ina taya ka Murna, sannan barka iyayen yara za su huta da tsabar yaudaran musu ya'ya da ka dinga yi a baya."
Tahir ya yi dariya kafin yace"To nagode, kasan komai Time ne nima ina ji a jikina Lokacin da zan yi aure ya kusa in sha Allahu."
Sadiq na dariya yace"Eh lalle to Ameen."
Daganan suka cigaba da Tattaunawa kan lamarin na wani Lokaci kafin su yi sallama.
A ran Sadiq yana jinjinama wannan yarinyar da ta iya sace zuciyar Tahir farat daya haka akanta ne kawai yaji Tahir ya nuna cewa lokacin da zai yi aure ya kusa.
Tunda ya koma kullum da Safe in ya Kira Siya itama Sultana zai kirata yaji Lafiyanta.
Ko da bazata amsa dakyau ba, shi dai daman Saboda ya Fita hakkinta ne.
Ranar alhamis da ya kirata da daddare bayan sun gaisa ya ke kara mata Tunin inda Siya zata sauka.
Kai Tsaye Sultana tace"Ni fa na gayamaka bani da masaukinta a gidana, kuma duka kayan da ke cikin gida nawa ne naga ba Dakin da bakomai a ciki ballatana kace na Sauketa aciki."
Mamakinta ya kara kamashi Saboda Haushi sai kawai yace mata"Sulatana ki yi duk abunda ki ke so, lokacin ki ne."
Daga haka ya katse wayarsa, Sai ya kira Big sis ya so ya fad'a mata abunda ya Faru tsakaninsa da Sultana ne sai kuma ya fasa a ransa yace ai shi Namiji ne shi zai Dauki matakin da ya Dace.

Kawai sun yi mganar sai ranar lahadi zai zo gusau tunda sai Ranar asabar zai je zariya ya kwana washegari ya Dauko Siya su taho tare.
Duk da Surayya sun yi waya da Hasiya ammh bata nuna ma Sadiq ba Tunda wannan kuma sirrin su ne ita da Matar kaninta kamar yadda shima kanin nata akwai sirri a tsakaninsu sun yi mganar Umma har ya gayamata abunda Umma tace masa Ranar da zai koma.
Surayya ta yi dariya kafin tace"Ai Umma na kaunar yara nan ina jin nan gaba ana yayesu zata kwace muku su."
Shima cikin dariyan yace"Sai mu bata, ina fatan mu samu wasu kafin a yaye sun."
Surayya tace"Kai Sadiq, gwarne ka ke so Hasiyan ta rika yi?
Yana yar dariya yace"Matar so fa ita ke gwarne kin manta ne Big sis.!
Ta hararesa kamar yana ganinta kafin tace"Bansani ba sai ka fad'amin."
Sai ya kwashe da Dariya ta na tayashi.
Sun yi mgana Sosai akan Umma Surayya ta nuna mai su cigaba da addu'a in sha Allah Umma zata dawo yadda suke so.
Daman har da zugan su Sajida kuma yanzu ta daina Biye musu.
Sultana me suke samun nasaran yi mata Famfo son ransu.
Shi fa Daman Sadiq ya sani Abubuwan da Sultana ta ke yi ba Wayonta ba ne.
Shifa har mamakin Sajida ya ke yi, matar nan ko shed'an in ya ganta sai ya sara mata wajen Tsabar Munafunci.
Duk zai kyalesu yanzu daman ya yi musu iyaka da matarsa su je ita kuma ta Biye musu su kaita su barota shi dai in ya gaji da tarata ya Faceta har Abada ta facu kenan bazai maida Dattin abunda ya fitar a hancinsa ba.
kamar yadda yace Ranar asabar da misalin sha daya na Safe ya dira a Zariya ya iskeni na yi masa kyakyawan Tarba kamar yadda na Saba ni da ya'yana.

********
Chapter 51 · 0% Book details