← Book details Tmw Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 83

Sashe 71

Tmw Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bayan wata daya, tuni Sajida ta fita Idarta yanzu ba matar Yusuf bace ita.
Abunda ta ke tunanin bazai Faru ba sai gashi ya faru ta na cikin Layin zawarawa.
Ta yi kuka kamar ranta zai fita ba mafita karshenta ma ranar da ta fita Idda aka Daura ma Yusuf aure da Budurwa yarinya karama
Sakeena ta kirata ta na fad'a mata kamar Zuciyarta zata Buga haka take ji.
Abba kuma yace abunda ta zab'ar ma kanta kenan Allah ya ba da sa'a.
Umma ma tace shiyasa akace zaman lafiya ai yafi zama dan sarki.
Saboda Halin da ta ke ciki yasa ta koma ta na zuwa gidan Sultana ta yini, ko da ba ta nan ta na makaranta ita da Naja ita ke zama a gidan ta na yi mata girki..saboda acan Umma bata sakar mata Fuska kwata kwata bata jin d adin zaman gidan.
Ga shi Sultana ta yi ta mata wukalanci da gadara ita mai gida duk ta shanye.
A watan da Sadiq yazo ya iske Sajida a gidansa sai da ya yi mamaki.
Sai yaji kuma ta bashi Tausayi Kuma wannan ai ba girma ba be ki koma kina bin matar kaninki.
Shiyasa da kansa ya samu Umma ya yi mata mgana.
Ya lallasheta da Kaddara ne bawa bai isa ya sauya ta ba.
Yace Sajida ta koma gida ta zauna gaban Umma ya kuma Dauki kudi 10k ya bata tare da ce mata in tana Bukatar wani abu ta kirashi.
Naka naka ne, duk abunda Sajida ta yi masa yayarsa ce kuma shi ba Murna ya yi da Farko ba.
Yaji dad'in yadda Allah ya nuna mata Ishara ammh bai taba Tunanin Yusuf zai rabu da Sajida haka ba ya Dauka na gargad'i ne daga baya zai maidata.
Shi kanshi yaji mata rashin dadi sosai.
Sai ga Sajida na kuka a gaban Sadiq kunyar duniya duk ya kamata.
Ko sadiyan da suke had'a waje tare da ita ba ta tsinana mata komai ba.
Kowacce na gidanta ta rike aurenta ita kuma ta na zawarcin da ta ke ganin kamar da gangan ne in mace ta zama bazawara ko auranta ya Mutu.
A baya tana ganin abun Fahari ne A gareta tana ganin Hasiya kamar wata ba mace ba tunda Sadiq ya aureta a matsayin bazawara.
Tafiyar Sadiq a satin Sajida ta kusa yi ma Sultana dukan tsiya.
Wata ranar laraba ne sultana ta dawo makaranta sai ta Biyo nan gida.
Daman nan take sauke gajiyanta.
Umma bata nan ta na shashen Innani ita da Mama.
Sajida ne kadai a falon Umma ta na zaune tana gyaran kumbunanta na kafa.
Da farko da ta shigo sun gaisa har ta Dauki Ummi hannun Naja.
Ita kuma taje ta zubo musu abinci ruwa ne tace Naja ta shiga kitchen ta Dauko musu.
Bayan la'asar haka sai aka yi baki Siyama tazo da yan'uwan mijinta su gaida su Umma da Innani.
Daga bangaren Mama suka zo bangaren Umma.
Ga mama ga Umma a wajen, wata cikin yayar Baban Mijin Siyama suke gaisawa da Sajida.
Kamar an Tambayi Sultana ta yi karaf tace musu"Anty Sajida ce bazawarar gidan mu ba."
Gabadaya sau aka bita da kallo bata damu ba ta cigaba da fad'in"Yanzu shikenan kiri kiri Abban su Amal ya ki maida ke dakin ki? Gaskiya bai kyauta miki ba yasa kin zama bazaawara Anty Sajida ni kuma kunsan na tsani zawarawa yawancin su Yan bariki ne masu kwacen mazajen wasu."
Umma kunya duk ya kamata Sajida kuma sai da taji ba ta taba muzanta irin na ranar ba.
Matar ko cikin Tausayawa tace"Allah sarki, ai ba yin kanta ba ne shi kuma sha'anin aure ai na Allah ne, sai kiga kuma an daidaita a gaba.
Kuma da kike mganar zawarawa yan bariki ne ni na kulubance ki ta wannan bangaran ba haka ba ne, duk wacce kika ga ta zama bazawara ba yin kanta ba ne kaddarace ta fad'a mana, kamar ni anan mutuwa ce sila wata kuma zaki ga sakin na kaddara ne ba macen da zata so ta zama bazaawara da son ranta karya ne wannan burin kowace mace ta zauna a gidan mijinta lafiya lau, saboda haka zawarci ba aibu ba ne sannan ki sani kaddara ce ke maida mace hakan."
Umma da Mama har suna had'a bakin fad'in"Hakane wlh."
Matar ta cigaba da fad'in"Kuma mganar zawarawa duk yan bariki ne wannan karya ne, ke yarinya ce karama daga ganin ki baki san rayuwa ba har yanzu, ni nan shekaran mijina Goma sha hudu da Rasuwa ban yi aure ba, to ina zani gani da ya'ya mata a gaba na? Sannan ba wai bam samu maneman ba ne na samu kawai ban yi ra'ayin auren ba ne kuma Alhamdulillah na tsare kaina sannan na tsare mutumcin ya'yana ba Kasawa bace domin an saki mace ba, Kaddara ne ta Ubangiji da in yace kun yafakum ba wanda ya isa ya dakatar da hakan, sannan domin bazawara ta sake wani auren ba kwacen miji ba ne cika sunar ma'aiki da kuma kare kanta daga zargin mutane ko fad'awa halaka, sannan ki sani itama bazawara mutum ce kamar kowa kuma Cikakkiyar mace maj yanci kamar yadda Budurwa ke da yanci.
Ba Inda Allah ya ware budurwa da bazawara duka sunansu mata, kuma suma sun canchanta su samu farinciki wasu zaki ga sanadin hatsarin mota suka rasa mazajensu! Wasu kuma sanadin mutuwar Fuju'a wasu kuma sanadin Boko haram, wasu kuma sanadin Sakin aure da In Allah ya kaddaro ma mace ba ta da yarda zata yi, ya kamata ki daina Dariyan kaddaran zawarcin wata macen saboda ke ma macece kuma hakan ba abun mamaki ba ne in ke ma ya faru da ke watarana."
Sultana duk sai ta raina kanta Sajida ko hawaye wani na bin wani a kan Fuskata cikin kuka tace"Wlh kina mgana kamar da ni ki ke, nima a baya ina daukan duk macen da ta zama bazawara wata mara gata ko wacce da gangan ta bari hakan ya faru, sai na ke ganinsu kamar ba su kaimu zama mata ba, sai da abun ya faru da ni na kara gane rayuwa na kuma san cewa Mace ba ta siyan ma kanta zawarci sai idan Allah ya kaddaro mata."
Irin kukam da Sadija take yi sai da ta bama Umma da Mama tausayi.
Umma a ranta itama sai taji kamar da ita ake yi, itama ai ta kyamaci bazawar sanda Sadiq ya kawo Hasiya.
Gani ta ke yi kamar gazawa ce ke saka auran mace mutuwa.
Ashe ba haka ba ne, Komai na Duniya nan Allah ne ya ke tsarashi kuma ya faru a yadda ya ke so.
Matar nan har suka fita Sajida na kuka Umma da mama suka bi bayansu zuwa bangaren Innani.
Suna fita Sajida ta mike sai ji ka ke tas! Tas !
Sajida ta wanke Sultana da maruka har Biyu cikin bacin rai ta nuna ta da yatsa ta na fad'in"In kika kara kokarin tozartani acikin mutane sai na yi miki Bugun tsiya sultana, tunda sakara kike mara kunya."
Sultana Dafe da kunci ta na kallon Sajida kafin tace"Kika mareni Anty Sajida? Me na yi miki?
Sajida tace"Uban ki kika yi min? Nace ubanki kika yi min"
Sultana ta mike jikinta na rawa ta nuna kanta ta na fad'in"Ubana kike zagi?
Sajida tace"Shi na zaga wannan tsoho mai gemu da ke zaune a kauye shi na zaga maras mutumci."
Sultana ta saki shewa kafin tace"Wlh ba ubana ba, sai naki Uban, tunda uba bai fi Uba ba, kuma kada ki kara marina akan gaskiyata ba karya na fad'a ba da gaske ne ke din bazawara ce second Hand....!
Ai bata gama Rufe baki ba Sajida ta Buge mata baki ta na fad'in"Ke ce zaki sama second hand da ikon Allah Sultana ba ni ba, ban da an cusa ma Sadiq ke mai zai yi da ke? Banza kucaka kazama wacce bata san ciwon kanta ba.!"
Sultana na duba bakinta ta ga jini sai ta fashe da kuka tana fad'in"Kika fitar min jini? Wlh sai na rama kuma eh din ance bazawara second hand ce ni ai kuma ko da cusani aka yi da aurena mijina bai sakeni saboda bani  da hali mai kyau ba kuma kowa yasan halina ba na had'a husuma kuma ba na yad'a sharri."
Sajida ta nuna kanta ta na fadi'ib"Ni ki ke fad'a ma wannan mganganun ina yayar mijinki?
Sultana tace"An fad'a miki, ai ke ba uwata bace da zan ji kunyar gaya miki mgana."
Sajida tace in ba zane Sultana ba ita ba yar halas ba ce..kawai ta Rufe Sultana da duka itama ta na kokarin ramawa.
Chapter 71 · 0% Book details