← Book details Tmw Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 83

Sashe 57

Tmw Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Taji dawowarsa kila ko Siyama ta fad'amata ta yi masa abinci an ci gayu ammh ko kallo bata ishesa ba ta Riga ta ba'ta garinta a wajensa.
Shi ya kona ma sultana rai ganin ta yi wahala ta masa tarba duk wulakantata da ya dinga yi ammh shine zai dawo tana yi masa sannu da suwa ya kalleta kamar yaga kashi ya shige ciki.
Da wannan Haushin ta bisa ciki Fuu lokacin data shiga ta gansa yana Cire rigane a kansa ta tsaya Hannu rike da kugu ta na fadin"baka lura dani ba ne Yaya Sadiq?
Ko kallonta bai yi ba sai ma kwanciya da ta ga ya yi  ya Dauko wayarsa ya na Dannawa.
Kuka ya taso mata ammh sai ta Danne ta taka ta isa gabansa ta saka Hannu ta warce wayar.
Kallonta ma bai yi ba sai kawai ya Juya zai kwanta nan take ta saka hannu ta Juyoshi ta na fadin"Kana ji ina mgana fa?
Cikin kaushin murya yace"Me kika ce?
Ya fad'a ya na kallonta Ido Cikin ido, Sai ta kasa mgana cikin wani irin zafin kishi tace"Na yi maka abinnci ka taso kaci."
Kai Tsaye yace"Na koshi aci lafiya."
Daga haka ya juya mata baya lokaci d'aya yana fadin"Ki tabbatar da kin ijiyemin waya kafin ki fita."
Kawai sai yaji Sultana ta fashe da kuka da karfi harda jiniya.
Ammh bai sa ya waigeta ba Cikin kukan ne yaji ta na fadin"Shikenan tunda ni baka sona ka sakeni na tafi Gidanmu mana."
Yana jinta sai ya yi kamar bai ji ba sai  da ta kara maimaitawa sannan ya Juyo yana fad'in"Wani gidan kenan?
Cikin gunjin kuka tace"In da ka auro ni, in kai baka sona Umma na sona."
Wata bazawar dariya ya yi lokaci d'aya yana mikewa zaume kafin yace"Umma? Ke yanzu domin baki da kunya sai ki koma wajen Umma da matsalarki? Kin manta kin gama yawo da ita da cewa ta miki gorin haihuwa?
Sai a lokacin Sultana ta dawo Hayyacinta sai ta dakata da kukanta ta na shan Shessheka.
Cikin takaicimta ya kalleta kafin yace"Yau Umma na gayamin Abunda kika yi mata  ta na sharan hawaye, tace bata taba tunanin haka daga gareki ba Sultana, kuma don ma ban zaunar da ita na Fad'a mata irin abubuwan da kike yi min ba, Ai in dai kikace na sake ki ba gidanmu zaki koma ba tunda kince Umma bata son ki yanzu ko ki koma inda ake zugaki ana nuna miki abunda kike yi mai kyau ne, ko kuma ki koma Shinkafi tunda daman kince duk wanda ya bar gida gida ya barsa."
Daga haka ya koma ya yi kwanciyarsa ya kara juya mata baya yana jan karamin tsaki.
Shi kanshi ya sha mamakin Abunda Umma ta fad'a masa, bai dauka Jakancin Sultana ya yi tsanani haka ba.
Sultana kuma sai a yau taji kunyar Nadaman mganganunta ga Umma, su suka taru suka Rufeta ta kara fashewa da kuka tana yi ta na yi har tana dire kafafu yana jinta bai kara bi ta kanta ba.
Sai da yaji tana fad'ar manganuganunta cikin kuka ta ke fad'in"Ka yi wajen wata baka zo wajena ba, ammh nasan kaje wajen matarka kuma ka yi mata abunda ta ke so, ammh shine ni ka zo ka faramin wulakanci da nuna bani da Muhimmamci a wajen ka."
Ta karishe fad'a cikin gunjin kuka yana kwancen yace"Eh baki yi karya ba naje wajenta, kuma ina yi mata abunda ta ke so kuma zan Cigaba da yi mata abunda ta ke so, tunda nima Abunda tasan ina so ko da ban Furta ba shi ta ke kokarin yi min, ki yi koyi da ita domin Siya ta na da Dukkan Sufofin Mace tagari."
Ai Sultana najin haka kamar an Tsunguli bakinta ta bude baki tace"Shiyasa ita ka yi mata ciki ta Haihu, ni kuma da baka kaunata ka kasa yi min cikin da nima zan haihu."
Sai kuka wiwi wiwi kamar wata karamar yarinya.

Kamar wani gaula haka ya mike zaune yana kallon sultana.
Cikin mamaki yace"Shima cikin kina Zargin da gangan na ki yi miki shi?
Kai tsaye tace"Eh mana, ai ita da ka ke so yan Biyu ka bata, ni da baka kauna ko dayan baka bani ba wama ya sani ko yanzu wani cikin gareta."
Cikin Mirmishin takaici yace"Ina fatan Allah ya amsa bakin ki sultana."
Daga haka ya juya zai kwanta kawai yaji ta fado masa a jiki tana fad'in"Nima wlh sai ka yi min ciki, kuma nima yan Biyu na ke so."
Kallonta ya ke yi kamar yaga Mahaukaciya sabon kamu.
Cikin kaushin Murya yace"Ke dagani ba na son sakarci."
Sai kawai ta kara sakamasa kuka tana fadin"Nima ai ina da hakki a kanka in bazaka bani ba shima sai ka fad'amin."
Shifa ya fara Tunanin ko Sultana kwakwalwarta ba lafiya, bai isa ya ce bazai yi mata abunda ta ke so ba Tunda itama ta na da Hakki a kansa.
Duk da ransa baya so hakanan ya Danne zuciyarsa ya biye mata ya bata Hakkinta kamar yadda ta ce.
Yana samun natsuwa ya tashi ya barta nan kwance yaje ya Tsarkake jikinta ita Tsabar ma sakarci da kishinta na Jahilci bai sa ta Fahimci mace na son gyara wajen dawo da Hankali miji a kanta ba.
Tana kwance cikin bargo ta na kallonsa yana Tsane ruwan da ke kansa daga murya ta yi tana fad'in"Allah yasa ka yi min ciki yau."
Tsaki yaja mai girma kafin ya Juyo ya na kallonta sai da ya kariso gabanta.
Sannan ya kausasa murya yana fadin"Ni ban isa na baki ciki ba Sultana, ina so ki sani Ubangiji shine mai komai, shi ke samar da Ciki a jikin mace sannan ya Rayar da shi daga Gudan jini zuwa ya Busa masa rai, ni din banza da na isa na ba da abunda ba ni da Hurumi a kansa? Ki saka aranki Allah ke ba da wa, kema shi zaki Roka ya baki mafi Alheri."
Daga haka ya yi gaggawar Ficewa daga Dakin bayan ya Dauki wayarsa da ta watsar nan saman gado, bai jira jin wata mganarta ba.
Falo ya fita ya zauna ya yi Shuru yana Tunanin Rayuwa, Sultana ta na neman ta hanaahi kwanciyar Hankali.
Ya yi iya Tunaninsa ammh ya kasa gano inda ya tauye mata hakkinta.
Saboda ya mamta da Tunaninta yasa ya Kira Siya har ta fara barci ya tasheta yace su yi hira.
Ya tambayi su Asim tace ta baro su aciki tare da Habiba sun yi barci da Wuri, da alamun akwai su da zarin cikin Dare.
Sadiq har wani gyara kwanciya ya yi a saman kujera na zaman mutum uku, Hira ya ke yi cikin Annushuwa da Farinciki da ya saba kasancewa aciki in dai yana tare da Siya.
Har ga Allah bansan Assadiq na Gusau ba tunda bai gayamin ba.
Hira na saki jiki ina yi masa duk da akwai gajiya tare dani tunda da Safe akwai makaranta Tp din mu sun kara mana wata daya mun samu an zo Dubamu sau biyu saura daya.
Ina basa Labarin yadda su Asim ke da Farinjini a makarantar ne.
Har mai makaranta daukansu ya ke yi su tafi office ko kuma in zai yi zagaye malamai har fad'a suke yi wajen daukansu ni kan nace masa bani da matsalan Renon su Asim yanzu.
Sadiq na dariya yace"Ko? To shikenan nan gaba Allah ya kawo wasu yan ukun lafiya."
Da Sauri nace"Astagafrullah.."
Cikin yar dariya yace"Ki ma shirya, ina harin yan uku ne wannan karon"
Cikin Shagwaba nace"Haba dai ni dai ka bar wannan mganar Assadiq kada ka fad'i gaban yan Amin su amsa hakan ta faru."
Cikin danne Dariyansa yace"To nasan Siyata jarumace zaki iya"
Ya shagala da wayar da ya ke yi baisan Fitowar Sultana ba.
Sai da yaji an fizge wayar hannunsa cikin Tsananin kishi idanuwan Sultana Jajir ta saukemai daya dago ya na kallonta.
Cikin mamaki yace"Miye haka? Ko baki ga ina waya ba ne?
Sultana ta Duba wayar ta kunnata Haske ya bayyana.

"Siya ta.."
Chapter 57 · 0% Book details