Sashe 13
Tmw Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Kamar ta sani sai ta fara min bayanin ta inda suga hoton da komai.
Surayya ta ce"bamu sha wani wahalan gane gidan ba, tunda baya cikin lungu, sai dai mun shiga wani gida achan baya matar gidan ne tace mu zo nan ta na Tunanin ke ce'"
Sai na kasa mgana ina kara jin Tsoron Rayuwa zaton abunda ba ka yi zato ba.
Ko ni bansan Safiya ta Tura wannan Hoton ba, sannan bani da masaniyar yayarta khairiya na mu'amala da Daya daga cikin yan'uwan Assadiq.
Surayya ce kad'ai ta sha ruwa har na samu karfin halin cewa zan musu girki tace za su tafi ne ba wanda yasan sun yi wannan tafiyar.
Har ga Allah sai naji Surayya ta Burgeni baki ta ke ta bani ta na lallashina akan na daina kuka ko Damuwa ta na da tabbacin Komai zai zo da sauki na kwantar da Hankalina Sajida ko da mun had'a ido sai ta harareni da kallon Tsana, daman nasan ba kowa ne zai karbi mganata ba, zan Fuskanci tarin kalubale.
Tun ballatana da za su tafi, surayya ta rike hannayena ta na kallon cikin Idanuwana tace"Ki kwantar da Hankalinki Asiya, ba bu abunda zai Faru Sadiq kanina ne kuma Favorite d'ina, ya na ji dani, nima kuma ina ji da shi, kaf gidanmu ba shi da abokiyar shawara kamata, na yi mamakin da bai iya sanar da ni labarin ki ba, na yi masa uzurin Halinsa ne na Taimakon wanda ke neman taimako sai dai bazan taba masa uzurin boye mana wannan gagrumin abun ba, Tunda abu ne da ya shafi aure da Rayuwa gabadaya,so ki kwantar da Hankali komai zai wuce in sha Allahu."
Sai naji hawaye sun cikamin kwarmin Idanuwana, na fara yi mata godiya tace min bakomai.
Sannan ta yi ta jadaddamin na cire damuwa har ta na zolayata akan ina Dauke da Bbyn su, kada na yi musu asara sai ga shi ina Dariya.
Sajida ko ta fita mota, saboda ta kasa zama gani ta ke yi kamar kunnuwan Surayya Hala sun toshene da ta tsaya tana Saurarena kuma har ta na Neman Goyen bayana.
Suna tafiya na koma falo na zauna kan kujera, na saki kuka ta wani bangaren in na duba Surayya sai naji kamar na samu salama, ta wani Fannin kuma in na Tuna ire iren su Sajida sai naji na Raunana, na Shiga uku ina zan saka kaina in har Assadiq ya rabu da ni? Na tabbata Rayuwata sai ta fi baya kuntata matukar haka ya faru.
Surayya da Sajida a kan hanyarsu ta komawa Gusai, Direba na gidan gaba ya na Tuki su kuma suna gidan Baya, Surayya ko mijinta bata gayama gaskiya ba, Sai cewa ta yi Umma ce ta aiketa Sajida kuma zata rakata.
Kowannensu ya yi Shuru zuciyarsu na saka musu tunani iri iri.
Surayya tunaninta ya zurfafa sannan ba irin na kowa ba ne, Damuwarta daya ne yadda su Umma za su Karb'i mganar uwa uba kuma Innani tasan akwai babban kalubale, ballatana su san Labarin Hasiya, sannan ta ga alamun za su kyamaceta jin ita bazawara ce, sannan ga Sultana bata san ta ina zasu Karb'i mganar ba.
Ba ta jin Abba shi ya na da Saukin kai, Umma ce abun ji saboda ba lalle ta yarda da abunda zataji ko zata gani ba.
Sadiq ya yi kuskure kuma ya zama Dole a nuna masa rashin kyautawarsa, sai a yanzu abubuwa ke dawowa kanta daki daki ta tuna yadda aka sha fama da shi kan auran Sultana tun a wanchan lokaci ashe ashe ya na dalilinsa, daman ita fa ta yi wannan Hasashen na cewa akwai wani abu a zariyan nan da ya ke Dauke ma Assadiq Hankali, ta kira Tahir ta tambayeshi ya yi mata karya shima, ta na mamakin Wayau Sadiq har ya iya yin aure a boye ya kama ma matar haya suna zaune tare, har tsawon wannan Lokacin ba wanda ya sani abun a jinjina masa ne.
A gefe daya kuma na zuciyarta tausayin Hasiya ya darsun mata, Ba laifinta ba ne ammh sai ga shi ta na Shiga gagarin rayuwa saboda hakan, sannan har itama Sadiq ya yaudareta Don ma zuciyar macece da Rauni Sannan Tsskanin mata da miji sai Allah, ammh ai ko ta barayin hanata Haihuwa yaci Amanarta, ammh ko ma menene Allah ya nuna isharansa shi ya Kulla auran su, kuma shi ya nuna cewa akwai zuru'a a tsakaninsu.
Tunanin ta ya na tafiya ne kan yadda zata iya gayama Umma da Abba wannan Labarin.
Ba Sadiq zata taimaka ba, Hasiya ce wacce taji matukar Tausayinta ta na cikin wani Halin da ta ke Bukatar taimako, Sadiq kuma chan ya karata Shi da ya kira ruwa shi ruwa zai Cinye, zata dai Tsaya tsayin daka ta ga an yi ma Hasiya adalci ko domin cikin Sadiq da ke jikinta.
Ammh tabbas sai ya karb'i Hukuncin abunda ya aikata, sai ya gane ba shi da wayau bazata yarda ta karesa ba, Gwara ya gane kuskurensa nan gaba bazai kara gigin aikata haka ba.
Sajida ko acikin ranta ta gama kissima, irin yadda zata zuga Umma da Innani, in sha Allahu wannan bakar Annobar bazata zauna acikin zuru'arau ba.
Sadiq kuma ta zageshi a ranta bata san iyakata ba, Shege bata san Uban me ya gani a jikin wannan yarinyar ba farinta kamar na ma su cuta, ta gama tsara har Sultana sai taji mganar nan kuma zata zugata tace bazata zauna da Sadiq ba sai ya saki wannan Annobar.
Surayya kamar tasan Tunanin Sajida ta kalleta ta na fadin"Sajida kada naji mganar zuwan mu zariya a bakin kowa, Saddiqa kawai zata ji itama Saboda tasan mganar ne, ammh ban da Labarin Rayuwar Hasiya na baya Sajida ko a gida bazan fad'a ma su Umma canfin karyan nan da mutane ke yi a kanta ba, domin ni kaina ban yarda ba, sai dai ba laifin in sun ji cewa a bazawara ya aureta."
Sajida ta kalleta Sheke sheke kafin tace"Meyasa ba za su san abunda Sadiq ya kawo mana cikin zuru'a ba?
Big sis ki yi hakuri duka sai na karanta ma yan'uwa da su Umma gwara su san abunda ke Faruwa, kina fa ji da bakinta tace duk wanda ta aura ko rasa dukiya ko rasa lafiya, Sadiq kadai ne garemu namiji in wani abu ya same shi ba? kuma mun sani muka Boye wlh Allah bazai barmu ba, ni dai ba Ruwana bazan iya Boye wannan mganar ba ki yi hakuri."
Sai Surayya ta kasa mgana ta na kallon Sajida jin ta kara cewa"Kuma banda Sadiq ya yi asara me zai ci da auran bazawara? Bazawaran ma wacce ta yi aure Har biyu, abun takaicin ma kuma yasan komai a kanta ammh kuma ya aureta a haka ba da sanin iyayensa ba Dan Burauba ai ya yi asara wlh, ina sultana zata had'u da wannnan matar? Fatar jikinta kamar na mayu, har ga Allah ban ga abun so a jikinta ba sai wauta irin ta Sadiq."
Ran Surayya ya baci da Sauri tace"Ya isa Sajida, kar ki Rufa asirin kin Dad'e baki Tona ba, ammh ki saani wanda ya Rufa ma wani asiri shima Allah zai Rufa masa asiri ranar gobe kiyama, kuma da ki ke mganar bazawara kina Zagin dan'uwan ki, kin san adadin ladan da ya samu akan haka? Ba zaman bariki ya ke yi da ita ba Matar aurensa ce da shaidu suka shaida auran su, kinga kuwa ko wannan kadai ya isa ki yi salama ki kuma jinjina hikimar Ubangiji"
Sajida ta kyabe baki kafin tace"Daman Tun a dazun na Fuskanci zaki goyama Sadiq da yarinyar nan baya kamar yadda kika saba tsaya masa, ammh ina so ki sani ko Umma bazata taba karb'an wannan yarinyar da abunda ke Cikinta ba."
Surayya tace"Ni ba su zan tsayama ba, Ina bayan gaskiya ne, domin ita ba namu ba ne hakan baya nufin bazamu yi mata adalci ba, itama in zamu kalli abunda ta Fuskar adalci ya yaudareta kamar yadda mu ma ya yaudaremu, maganar Annoba da kike fad'i ki bari Allah ne ya Halliceta tare da kaddaranta ki daina Dariyann rayuwarta ke kuma kina alfahari da naki Rayuwar, mganar bazawara kuma kada ki zama Jahila Sajida, da ilimin ki da komai, ki ke so ki kawo wani karatu na banza wani nafsin ne yace ita bazawara ba Mutum ba ne? Ko kuma akace Saurayi ba zai iya auran bazawara ba? Kin manta da Labarin Annabi ne da Nana khadija? Ashe ko in da shi mu ke ko yi, mu al'ummarsa bamu isa mu kyamaci bazawara ba."
Sai ta yi shuru ta dakata, ta na lura da Sajida da ta koma ba ma yaronta Nono, kanta na gefe kamar maganar na Surayya ta na shiga ne ta na fita.