← Book details Tmw Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 83

Sashe 22

Tmw Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sadiq ya kalli Abba kafin yace"Abba Umma ta Dauki zafi da lamarin, tace sultana ta kwaso kayanta ta dawo gida. Nima kuma da na zo yau ina gaisheta taki amsani daga karshe ma ta Boye ma ganina."
Abba ya gyara zama kafin yace"Kada ka damu da wannan, bazan baka Shawaran ka rabu da daya saboda d'aya ba, duka matanka ne kuma zaka Cigaba da zama da su, na riga na yi mgana da Surayya nace ina bukatar son ganin ita iyalin naka ta Zariya Domin samun masalaha da Daidaito."
Da Sauri Sadiq yace"Ai tazo Abba, na ganta tare da Anty Surayya dazu kafin ka dawo."
Abba sai ya jinjina kai kafin yace"Shikenan ma hakan ya yi, komai zai warware in sha Allahu kada ka damu."
Ya fad'a ya na Dafa kafad'an Sadiq din alamin lallashi, Sadiq sai ya yi Tunanin gwara ya fad'a ma Abba komai daya danganci auransa da Siya Tun yanzu kafin kuma daga baya yaji wata mgana  yar Sauran yardan da ke Tsakaninsu ta kara lalacewa.
Nan ya zauna ya fara ba ma Abba Labarin Tun ranar farko da ya fara had'uwa da Hasiya har zuwa yau tare da Labarin duka auranta da kuma Kaddaran da ke cikin Rayuwarta.
Abba ya ji matukar Tausayinta sosai shi kanshi a baya saboda Innani da irin manganunta ya na da dabi'ar rashin Tauhidi ammh godiya ga Allah da ya bashi yaro mai kaifin Basira irin Sadiq shine ya yi sanadiyar da yasa yasan Allah shine mai yin komai a lokacin da ya so, a kuma sadda ya so.

Cikin Tausayin da ya bayyana har a saman Fuskarsa yace"Allahu Akbar kayi babban Jihadi Magajin gida, Allah Ubangiji yasa wannan abunda da ka aikata ya yi sanadiyar shigar ka Aljannah"
Cikin Farinciki Sadiq ke amsawa da Ameen Ameen, Abba ya cigaba da fadin"Uwa ka share ma kukanta, kai ma watarana Allah ya baka ya'yan da zasu same maka sanyin idanuwana su kuma zamo masu jin kukan ka, sannan su kasance mssu share maka hawayen ka."
Sadiq na ta amsawa da Ameen Sai Abba ya yi shuru ya na wani Tunani kafin yace"Mu bar wannan mganar a nan, kasan mata ba lalle su iya Fahimtar irin wad'anan abubuwan da Wuri ba. Kuma kaga innani yanzu ta na ji sai kuma ta Rikita al'amarin"
Kamar Abba ya sani daman shi Sadiq ya fad'a ne saboda Tunaninsa ko har da wannan Labarin suka sani? Mganar Abba sai ta warware masa cewa ba su kai ga sanin haka ba.
Abunda bai sani ba Shine komai da ya Danganci Hasiya bazai zama Sirri ba a yau.

Suna nan falon Abba suna Hira Surayya ta kira Abba kan mganar gashi ta zo da Hasiya, sai Abba yace Sadiq ya fad'a masa ga su ma tarre. Yanzu an kusa kiran sallar azahar bayan sun je masallaci sun dawo su had'u a shashen Innani ta gaya ma su Umma.
Daganan suka yanke Kiran, duk da Sadiq na jin tsoro sai dai yaji gwarin gwiwar samun Abba a kusa da shi, Daya tambayi Abba ko wani ne yazo musu da Labarin auran nasa?
Abba yace Surayya ce da Saddiqa suka zo masa da mganar daganan ya yi shuru yasan Halin Big sis da bin Diddigi ya na da tabbacin har Zariya kila sai da taje.
Daganan masallaci suka tafi suka yi sallar azahar, sun jima a masallacin Abba na ta gaisawa da Mutane makota abokan arzuka, Shi ya bata musu Lokaci suna hanya ma Surayya ta kira Abba sannan ta kira Sadiq.
Sadiq ne ya amsa kiran nata sai tace masa suna shashen innani su kawai su ke jira, shiyasa suna shigowa gidan bangaren na Innani suka nufa kai Tsaye Abba na gaba Sadiq na bin bayansa kamar ya na kirga takun Abban.

Da sallama Abba ya shiga Falon, Sadiq ya yi sallamansa iya a saman bakinsa ammh, Falon nan na Innani a cike ya ke da yan'uwansa mata shi ba su ne a gabansa ba Siya Idanuwansa ke son gani acikin falon.
Bai lura da yadda gabadayansu suka Zuba masa ido ba, domin ya wani had'e rai  ya yi, yaso ma yazo da bakin glass din ya Rufe kwayar idanuwansa Sannan wacce ta masa shisshigi ko ta wuce gona da iri ya taka mata Burki, Ahto ai in sun girmesa ai ba su haifesa ba.
Allah ya nuna masa Siya chan gefen Surayya ta Rakube baiwar Allah kanta na kasa, Tausayi ta bashi yasan a takure ta ke ko da ganin yadda ta ke ta mutsu mutsun zaman bai yi mata dadi ba, ko baka da juna Biyu kayi zaman tankwashe kafa na wani Lokaci ya ka ke ji, ballatana ga Ciki kuma ya Tsufa.
Sanda ya biyo bayan Abba zuwa Cikin Falon, kamar zai wuce ta bangaran Siya da Surayya sai kuma yaga Umma gefenta Kuma Mama ce ta inda zai wuce irin kallon da Umma ta yi mssa ne yasa da Sauri yaje ya zauna a gefen kafafun Abba.
Innani na zaune itama akan kujera kusa da Abba, ga sandarta a gefenta da gilashinta sai faman cin magani ta ke yi, Daga gefensa ne yaji ana ta jan majinan kuka da shessheka ya juya sai yaga sultana wajen kafafun Innani ta dunkule kanta ta na kuka.
Mamaki ya kamasa miye abun kuka Fisabillahi in ba gata ne ya yi ma Mutum yawa ba?

Karamin Tsaki yaja a ransa ya Kauda kansa, Innani kuma sai kallonsa ta ke yi ta cikin gilashinta ta na Hararansa, sai kuma ta waiga barayin da Hasiya ke zaune itama ta harareta.
Gani tayi magajin gida ya kalleta ya watsar kamar yaga kashi yasa ta ture Sultana da rabin jikinta ke kusa da kafafunta ta na fadin"Ke ni ja chan sakara mara wayau? Miye kike wani kuka ni da nace miki ki kwantar da Hankalin ki, in dai ina Raye Magajin gida bai isa ya Tozarta ki ba, ke ba ma shi ba Kaf a falon nan ba wanda ya isa, ko da sulaimanun ne da kansa kuwa, Saboda haka ki bar kuka zan karb'an miki yancin ki, ba mai had'a ki zama da yar Bariki Tsohuwar kilaki."
Ta karishe fad'a cikin Kufuluwa  Da Sauri Sadiq ya kalleta bai san bakinsa ya Kubce ba sai da yaji yace"Innani wacece Tsohuwar Kilakin?
Innani ko ba tsoro da karfi ta nuna Hasiya da Sandar Hannunta Lokaci daya ta na fadin"Ga ta chan a wannan a bar mai kama da mayun da ka kawo  min cikin Zuru'ata mai Tsafta."
Sadiq ya kara girman Idanuwansa ya na kallon Innani ransa na baci da karfi yace"Innani.."
Bai sauke ma numfashi ba yaji Umma ta kira sunansa a fusace"Abubakar."
Dole ya yi shuru ya koma ya na kallon Umma Lokaci d'aya ya na fadin"Na'am Umma."
Cikin gargadi tace"Ka yi ma mutane shuru anan wajen Tunda baka da kunya."
Innani na jin haka sai tayi kayci tace"Da kin barsa ya zageni, da yau kunga illar auran bariki ganin idon ku salamatu."
Abba ne ya yi gyaran murya kafin yace Surayya ta Bude taro da addu'a a gefe daya kuma ya na mamakin ganin duka ya'yansa shi dai bai ce su zo ba, Sadiq kawai ya Bukaci gani da matarsa.
Girgiza kai kawai ya yi, acikin ransa yace mata mata, duk abunda aka had'a da mata sai an yi Hakuri.
Surayya ta yi sallama sannan ta Bude taro da addu'a.
Kafin ta ce"Abba ga Hasiya matar da Sadiq ya aura kafin ya auri Sultana gata nan kusa dani."
Ta fad'a ta na dafani, ni ko jikina ba inda baya rawa, daga fuskata kuma hawaye ne ke diga a saman Hijabin jikina na kasa dagowa duk da naji Idanuwam Assadiq a kaina ba maganganun Innani ne suka sakani kuka ba, Sai tun zuwana cikin gidan nan na Fahimci kaf cikin yan'uwan Assadiq ba wacce ke maraba dani sai Surayya.

Tunda muka je falon Umma ita kad'ai ke kulani, na sha manganun cin zarafi a wajensu In Surayya ta taremun su taso mata, Umma kuma da ta fito Surayya tace na gaisheta bata amsa ba, Daga karshe ma tace duk su koma daki sai aka barni a falo kamar wata almajira.
Daganan wasu suka shigo su Sakeena kenan yan dakin Mama suna kallona suna Tabe baki, na gaishe su suka amsa a wulakance kamar ba sa so, tun a lokacin jikina ya saki na ke kuma da Tabbacin ba lalle su bar dan'uwansu ya cigaba da aurena ba
Ko yanzu da Innani ke ta aibatani bai Dameni ba, ni damuwata d'aya shine Assadiq ina cikin Tsaka mai wuya matukar suka ce zasu rabani da shi.
Ina cikin wannan Tunanin naji Muryan Abba na fadin"Ma sha Allah, ta taso ta zo kusa da ni ta zauna itama."
Sai gabadaya kowa a falon ya bi Abba da kallon Mamaki musamman ma Umma da Innani.
Surayya kuma sai da ta Murmusa Sadiq kuma kamar ya goya Abba, Daman yasan Siya ta gaji da wannan zaman.
Surayya ta taimakamin na mike Tsaye kafafuna sun haye sumtum, jikina na dan rawa ta kalleni kafin tace"Asiya ke ji Abba na kiran ki."
Ba musu na gyad'a mata kai sanman na fara tafiya a hankali zuwa gaban Abba ammh na saka Hannu ina kare Cikin jikina duk da ban isa na Rufeshi ba Allah ya Riga ya bayyanar da shi.
Chapter 22 · 0% Book details