Sashe 8
Tmw Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gatan duniya da Miji ke yi ma matarsa Assadiq na yi mini shi, Har fiye da zato na da Tsammanina, Ko da yaushe cikin kira na ya ke yi yaji Lafiyata, in kuma ya samu sarari ko ba ranar zuwansa Zariya ba ne zai samu lokaci ya zo ya ganni ko da bazai kwana ba.
Bai taba bari na yi kukan wani abu ba, Duk abunda na ke so kafin nayi mgana ya riga ya yi min shi.
Kayan abinci wani baya karewa ya ke tarar da wani, komai na Bukatar macen kwarai a gidan mijinta Allah ya bani shi ta bangaran Assadiq ta ko'ina Rayuwata ta inganta.
Kudi bani da matsalansu har ma ina taimaka ma yan'uwana, Amma ma dagachan bangaran ina taimakon su da iya abunda na ke da shi.
Sun zo kwanaki ita da Adda suka Dubani ba su dai kwana ba ne, Amma daman bazata iya kwana a wajena ba, da ma dai gidan Adda Fati ne, gidan Adda Rukayya daman Saboda Mijinta ba ta cika ganin baki ba.
Bangaren Maman Suhailat itama Tsakaninmu sai godiya sosai ta ke kula dani, in dai ta na gida sau ukun nan zata lekoni taga lafiyata shiyasa da Assadiq ya yi mganar kayan Haihuwa da nawa nace ita zan bamawa ta Siyomin ta na da kirki.
Nasan yadda zaman gidan haya ya ke, ana samun mutanen kirki da na banza ita dai maman Suhailat ko da ta na da wani halin to kirkinta duk ya shafe wannan.
Ramatu da tazo ta ga irin gatan da na ke ciki sai da ta kara dawomin da mganar da ta tab'amin shekarun baya.
Ta kalleni da tsinin Cikina a gaba kafin ta yi mirmishi tace"Kawata daman ai na fad'a miki watarana Zaki ji dadin Rayuwa kamar kowa koma fiye da kowa."
Na kalleta cikin mirmishi kafin nace"Hakane wlh gashi komai ya wuce sai dai Tunawa."
Ramatu tace"Kin tuna na sha gayamiki Daga salisu har Abubakar ba su ne gwanayen ba gwanin in yazo Shine yardaddaje har a wajen Ubangiji ki ka yi ta min musu kina ganin kamar haka bazata faru ba, yau gashi kin samu fiye da zaton da na yi miki Fata Hasiya."
Sai na kasa yi mata mgana ina ta shafa Cikina ina jin wani farincikin zamowa uwa a cikin raina.
Yau ga shi ni Hasiya da na cire rai ga aure ma, ni ce dauke da cikin Haihuwa lalle Allah ne abun godiya
Rayuwata daidai ta ke tafiya sai dai abu d'aya ne na ke tunawa ya sakani Fargaba shine na rashin sanin gobena a cikin Ahalin Assadiq tunda har yau ba su san da zamana ba.
Ramatu ce te katsemin Tunani da cewa"Ke na manta ban fad'a miki ba, ranar na shiga anguwan su Salisu na had'u da shi"
Cikin mamaki na dago ina kallonta kafin nace"Haba? Me ki ka je yi?
Ramatu tace"Makociyata din nan, Maman Basma mahaifiyarta ta rasu naje mata gaisuwa sai naga ashe kusa ne da gidan iyayen Salisu, aiko ina fitowa sai ga shi mun had'e da shi, shi da Musabahu."
Cikin wani yanayi nace"Allah Sarki? Ya kika gansa? Ya warke?
Ramatu tace"Ya warke, sai dai har yanzu ya na dan d'ingishi, sannan ya na Dogara karamar sanda."
Sai na yi shuru na kasa mgana acikin raina ina jin wani iri, kenan har gobe in aka kalli Salisu Bakin Fentin da na yi ma Rayuwarsa bazai taba goge masa ba.
Kila Ramatu ta Lura da sauyin yanayina ne, kuma tasan saboda mganar ne, yasa da sauri ta dafani ta na fad'in"Kinga ba na gayamiki ba ne saboda ki shiga damuwa ba, na fada miki ne saboda sai da ya tambayeni ke, yace yaji an ce kin yi aure nace masa Eh! Sai yace in mun had'u nace ya na gaisheki"
Kai kawai na kad'a kafin nace"Ayya Ramatu ina amsawa! Ammh dai ko da ya warke, akwai wannan tabon a jikinsa in shi bai kirani bakar Daka ba, yan'uwansa baza su taba mantawa dani ba."
Ramatu cikin wani yanayi tace"To ai ba ke bace Allah, ke dai kawai kin zama Sanadi ne Hasiya, ki kara godema Allah domin kin cinye jarabawarki."
Sai kawai na gyad'a kai kafin nace"Hakane ina Labarin Abubakar? Ya dawo garin ko ya na chan kanon?
Ramatu tace"Anya? Kinsan bansan kowa daga bangaransa ba, ko ya dawo kila dai ya na chan, ko kilama ya yi auransa."
Da Sauri nace"Allah yasa."
Daga haka muka saki maganarsu muka kama wata, sai dai har ta tafi abun na cikin raina.
Yanzu Fargabata d'aya yan'uwan Assadiq ta yadda zasu karbi' mganar auranmu daga sama, ni abun da ke damuna in suka ji Bakin fentin da ya bata Rayuwata dakyar su amince Assadiq ya cigaba da zama da ni.
Ga cikinsa a jikina in har ya barni bansan kuma wani Hali zan shiga ba.
Da farko farko na dauka in ma yace baya son cikin ni kad'ai zan iya renen Cikin har na haifesshi na bashi Soyayya da kulawa, sai daga baya na Fahimci wani abu ni kad'ai bazan iya ba. Assadiq shi ne ginshikina ni kuma ni ce mahad'in Rayuwarsa da Rayuwar abunda ke cikina gabadaya.
Ko da yaushe cikin Tuna ma Assadiq na ke yi akan ya yi ma yan'uwansa maganata su san da ni, ammh sai yace na kara masa Lokaci in sha Allahu zai sanar da su, abunda na lura shine tsoro ya ke ji, kuma ya rasa ta hanyar da zai iya fad'a musu kuma Lokaci na ta tafiya, Tsoro na d'aya in har na Haihu wlh abubuwan za su kwabe mana yadda bamu yi tsammani ba.
Kuma in har na Haihu nasan yan'uwana za su bukaci ganin Dangin Assadiq rashin ganinsu zai iya fassara karyan da na yi musu.
Ammh bayan wannan fargaban babu abunda ya tab'a Rayuwar auran mu, cikin Farinciki mu ke zaune tare da Soyayya da kauna da Tunanin Dorewa na har Abada.
In ya zo min weekend kashe wayoyinsa ya ke yi, sai zai kira Sultana ko gida sai ya kunna ya yi mgana da su, Lokacinsa da komai nawa ne, ba na girki sai dai ya Daukeni a mota mu fita mu ci a waje, mu ne wajen shan Ice cream mu ne wajen cin abincin da cin kayan kwalama, ba kowani zuwa ya ke zuwa da mota ba, wani Lokacin sai ya biyo ta haya.
Ya sauyamin waya ya siya Wata Samsumg Sabuwa, sannan ya siyamin wata karamar Tap mai kyau, har sai da na yi masa mgana baya gajiya da siyan computer, ko wani Lokaci sai na gansa da sabuwa ? Sai ya yi dariya kafin yace min sana'ar Abba kenan ya na shigo da su daga china, india zuwa Gida nan Nageria.
Daganan na yi shuru Tunda abun na masu uwa a gidin Murhu ne, Karamin Tap din sai na ke zuwa makaranta da ita babba kuma sai na rika barinta a gida na kallo na ko yin game da Sauran abubuwa.
Saboda gudun a samu matsala ko Hotona ba na Dorawa a waya Tunda Saliha na da lambata, sai dai in muka yi Hotuna na adana su a wayata, shima baya Turawa saboda gudun a samu matsala sai dai ya kan dauki wayata mu yi ta Hotuna da shi.
Akwai wani zuwan da ya yi lokacin cikina ya shiga watansa bakwai kenan ya kara girma da tsini.
Zamu fita ne zuwa gidan Ramatu daganan mu je gidan Adda Fati, na saka bakar Abaya na yi Rolling din mayafin shi ya ma nad'amin shi, shi kuma ya sanya Farar shadda har da Hula sai ya zama wani babban mutum kwarjinsa ya kara bayyana.
Rikeni ya yi ta gefen Damarsa ni kuma sai na kwantar da kaina saman kirjinsa, shi ya Dauki wayata ya yi mana Hoton ni na dago ina kallon wayar shi kuma ya na kallona dukkanmu muna Dariya aka yi Hoton
Farar Fuskata da ta kara wani haske ta bayyana acikin hoton shima Saboda Hutu ya kara fari da kiba sai muka yi wani irin kyau kamar Wasu Taurari acikin Wata.
A mota ma ni na kara yi mana wasu Hotunan ya na Tuki ina faman Sauke kaina saman kafad'ansa ina yi mana Hotuna har da Vedio.
Mun yi kyau sosai shima da muka Dawo gida na nuna masa yace Hotunan sun yi kyau na ijiye mana watarana zai saka a wanke mana Babban Frem dinsa.
Abunda bansani ba Shine ni dai nasan ba wanda ke Daukan wayana shiyasa ban taba Tunanin Samar ma Hotunanmu muhallin sirri ba, na manta Safiya na Daukan wayata, a satin da muka yi Hoton muka koma makaranta a chan ne Safiya ta karb'i wayata ta na gani sai ta ga Hotunan nan Sai ta fara santin mun yi kyau, Daman kuma tasan Assadiq tunda sun taba had'uwa yafi sau biyu.
Bayan Hotunan mu ina da littafan Hausa a wayata, wanda na kan samu a groups din novels, su ne su ke debemin kewa in Assadiq baya nan, duk da karatun ba sosai na ke yi ba su Safiya tace min zata Tura bansani ba ashe ta had'a da wad'anan Hotunan ta Tura cikin wayarta.
Wad'anan Hotunan su ne za su sillar fallasa Sirrin da Assadiq ya jima ya na Boyewa.
********
Saddiqa da ke aure a Jahar Kebbi yar kasuwa ce sosai, ta na kasuwanci saida atamfofi lesuka da Sauransu, sannan a cikin Family ko biki za'a yi ita kan fito da anko kuma ta Dauko.
Shiyasa ta na harka da yan kasuwa yan'uwanta daga mabambanta garuruwa.
Kuma harkan ta yafi yawa ne ta Kafafen sada zumunta, ta na da mutane sosai ma su kallon Status dinta, da kuma wad'anda ta ke huld'a da su.
Da safiyar ranar wata Laraba bayan ta gama abunda ta ke yi ta sallami yara da megidan ta dauki wayarta, akwai kayan data siya daga kano ta siya kayan za'a tura jigawa, ta na so ta yi mgana da mai shagon taji in har an gama had'a kayan gabadaya.