← Book details Tmw Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 83

Sashe 62

Tmw Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Assadiq na kallah Fuskarsa ba Fara'a mun had'a ido da shi, har sau biyu banga ya sakarmin fuska ba.
Sai dai da na yi masa mirmishi kad'an ya kuma maidamin da na Fatar baki.
Abba ne ya katse shurun da kallon Sadiq yana fadin"Magajin gida ne ya kirani da Asuba yace zai zo tare da Sultana yana son zai yi mgana da mu tare da matansa gabadaya Saboda warware wata matsala."
Ya fad'a kafin ya dagata yana kara kallon Sadiq da ya yi shuru bai yi mgana ba.
Umma tace"To Allah yasa lafiya?
Sadiq ya sauke Numfashin bacin rai kafin ya nuna Sultana yana fad'in"Itace zata jawo in ma matsalar ce zata faru Umma"
Cikin mamaki Umma tace"Topha me ya faru ne?
Ya gyara zama yana fadin"Kan zencen Tafiya da Siya Abuja ne, tunda na gayamata ta hana kanta sukuni wai ko na tafi da ita ko kuma duka bazan tafi da ko d'aya acikin su ba.
Umma ban taba fad'a muku wani abu game da abubuwan da Sultana ke yi min ba, zaki tuna wani zuwa da Hasiya tayi nace ta sauka a gidana?
Umma ta gyad'a kai alamun ta tuna shi kuma ya Cigaba da fadin"To Umma wulalanci ta yi min dagani har Siya, shiyasa washegari bayan na koma nace ta koma wajen ki ta zauna Sultana ta ce gida gidanta ne Tunda da sunanta Abba ya bani gida, tundaga Lokacin na saka ma raina Hasiya ba zata kara zuwa gidanta da sunan ta zauna ba, sannan Lokacin da ma'aikantan mu suka yi mana mganar gida, na so na yi ma Sultana mganar zan tafi da ita Abuja Saboda ina da mata Biyu, bai kamata na rika zama ni kadai acan ba, kuma Dalilina alokacin Saboda Hasiya na karatu itama kuma ba ta yi, har ga Allah da Farko ita na yi niyar kaiwa Abuja ta zauna Saboda nasan halinta na Zargin tsiya da nuna ana mata ba daidai ba.
Itakuma Siya zata dawo gusau ta zauna kusa da ku sai na rika zuwa ina ganinta Abba nasan ko a daji na ce Siya taje ta zauna na rantse Abba bazata taba yi min gaddama ba, ballatana yau ace ta Turkeni ta na son  jin Ba'asi.
Nasan halinta Shiyasa na zabi tafiya da Sultana da Farko, ammh Saboda ta na Daukam zugan su Sajida sun kitsa mata Siya na karatu itama ta matsamin sai ta koma makaranta ni kuma tana gayamin nace shikenan Tunda haka ta ke so a lokacin na so ne sai ta koma can na nema mata Jami'r Abuja, sai kuma ba ta Fahimta ba tafi Daukan mgangansu munafukan su Sajida sama da tawa mganar, Shiyasa bayan an gama gina gidajen an bamu key na yanke shaawaran tafiya da Siya Tunda tagama karatunta, ita kuma ta zauna a gidanta na nan tare daku ta Cigaba da karatunta ina zuwa ina ganinta a wata sau daya in sha Allahu."
Abba da su Umma suka yi shuru suna jinjina mganganun Sadiq.
Sultana kuma sai kuka tana fadin"Ni ai baka gayamin Abuja zan koma tare da kai ba, in da ka gayamin da ban shiga makarantar ba kuma yanzu ma bata baci ba ana Transfer."
Kai Tsaye Sadiq yace"Haka su Munafukan suka kitsa miki?
Cikin kuka tace"ni wlh ba wanda ya ke zugani na ran.."
Umma ta katseta da fadin"Karya kike yi kuma anan Sultana, ai Sajida da Sadiya manyan banza ne marasa Tunani, nasan komai duk zuwa gidanki da suke yi suna Dora ki kan mgamganun banza.
Ta koma ta na kallon Sadiq kafin tace"Hukuncin da ka yanke ya yi daidai magajin gida, Hasiya ta koma wajenka da zama ita kuma ta zauna a gidan da tace da sunanta aka Si ya."
Mama tace"To ban da sakarcin Sultana, Hasiyar mai sanyin hali ma ba ta da girman ki in da kin kwantar da hankali lafiya kalau za su zauna."
Umma ta yi Tsaki kafin tace"Ai ko ta kwantar su Sajida ba za su kyaleta ba, Abban Siyama ka kirasu ka ci mutumcin su in ba haka ba sai sun raba auran Magajin gida da Sultana da Shiga da Fitan su."
Sadiq yace"Umma gwara su kashe mata auran kila ta yi hankali, ni ban mata iyakata da su ba yan'uwanta ne tunda sun fini Daraja a wajenta Fine, ni ne dai na yi musu iyaka da Matata da Rayuwa kuma na basu Lokaci ne suka kara Cikani duk sai sun kara Rena kansu."
Abba ya yi shuru kafin yace"basu bar Abunda suke yi ba kenan? Ku kyaleni da su, ke kuma Sultana ki yi hakuri ki bi umarnin mijin ki kin ji ko?
Sultana ta rushe da kuka tana Fadin"Abba ni tare da shi na ke son na zauna, ina fama da laulayi mai zafi ba na iya barci ni kad'ai"
Umma ta saki baki tana kallon Sultana ita da Mama.
Sadiq kuma ko kallo bata ishesa ba yasan halinta ni kaina na kasa ina mamakin makirci irin na Sultana.
Kai Tsaye Abba yace"Ki dawo wajen Umanki, daman ai wajenta ki ke in baya gari ko?
Umma tace"Sosai kuma muna nan ai zamu kula da ita, renon cikin ma duk a dakina ta yi jinyar kuma ai tare da Hasiyar da ta tsana muka yi mata Wahala"
Sai kuma ta kara saka kuka har da wiwi kamar karamar yarinya Abba ya koma ya lallashinta.
Ta na kuka tana fadin"Abba to kace masa ya tafi tare dani, in na kwana Biyu sai na dawo."
Kafin Abba ya yi mgana Sadiq ya yi saurin taran Numfaahinta da cewa"Kinsan Allah ko da bakunta bazan tafi da ke ba. Abuja gidan Siya ne ke kuma ga gidan nan a gusau kamar yadda kikace da sunan ki Abba ya bani gidan, itama da sunanta na karb'i gidan saboda haka ki zauna a gidanki itama ta zauna ana ta gidan.
Iya adalci da san zan yi miki kenan , kuma kinga ban rabaki da masu baki Shawara ba sai ki ba da Himma."
Abba ya jim kafin yace"Sultana ki yi hakuri ki zauna saboda karatun ki."
Umma tace"Kada ma Allah yasa ta Hakuran, kana wani bata Hakuri "
Abba yace"Salamatu komai a sannu ake bi."
Ina zaune na gyara zama ina Fad'in"Abba ni na hakura sai na zauna anan din ya tafi da ita."
Sultana na jin haka ta daina kuka, Abba kuma sai ya yi shuru bai yi mgana ba.
Kaina na kasa ammh nasan ina shan Harara wajem Assadiq
Umma ce tayi karaf tace"Hasiya tare zaku tafi, kai Tashi kaje ka shirya ku zo ku tafi ba ko ba Zariya kace zaku tafi ba yau?
A sannu yace'Eh zan kaita can saboda akwai Sreening din da zatayi a makaranta sai kuma sallama da yan'uwa sati biyu dai nace zan koma na Dauketa zuwa can."
Umma tace"Hakan ya yi, Allah ya tsare maza ka tashi kaje ka Shirya kada ku yi yamma, ita kuma wannan kabar mana ita anan."
Sultana ta kara saka kuka tana Fadin"Don Allah Umma ki ce ya tafi dani."
Umma tace"Bazan ce ba, da kike zaune anan wani abu ya cinyeki? Ko duk baki san da haka ba ne sai yanzu."
Sultana ta yi shuru ta kasa mgana, Saboda ita kishinta da bakincikinta Zai tafi da ne zai je ya bani duniya ban da ita, ita kuma zai barta anan sai yaga dama yazo ya ganta.
Haka su Sajida suka kitsa mata, tare da bata Shawaran ta yi ta rigima tace bata yarda ba in yace karatu tace ai za'a iya Transfer indai ya nace zai tafi da Hasiya to itama tace sai ta je, Daga karshe sai da ya fasa tafiya da kowacce Shiyasa ta hanashi zaman Lafiya tun jiya da ya sauka a garin ta ke masa rigimar ita ta fasa karatu tare za su koma Abuja, shi kuma yace bata isa ba nan ne gidanta anan zata cigaba da zama.

Sadiq kuma Tuni ya bi umarnin Umma ya fice abunsa bayan ya gama Hararata kamar Idanuwansa za su fad'o, ni kuma na kauda kai ni na yi hakane Saboda a samu masalaha ni bani da damuwa su je can ni sai na zauna anan tare da su Umma.
Allah na Tuba wani Dare ne jemage bai gani ba? Ai sai dai daran mutuwarsa.
Abba kuma ya Cigaba da fad'a akan su Sajida Mama ce ta kara da cewa"ai ni ko su Salima nace su fita sha'anin shiga abunda ba ruwansu, kada su je  su ja da ikon Ubangiji."
Umma tace"Suma ki kyalesu lokaci suke jira, duniya zata koya musu hankali, ko ni da na haifi Sadiq din na saki nace Allah yasa albarka to su kuma Munafunci me suke ta kai kawo a kansa?
Ni dai duk ina zaune ina jinsu, Sultana kuma na ta jan majina ta na Shesshekan kuka, Umma ta kalleni tace na tashi naje na shirya tunda zamu kama hanya ne.
Abba ma yace haka ya kamata Kada magajin gida yazo yana jirana.
Nima Umarninsu na bi na koma Bangaren Umma na cigaba da shiryawa.
Can sai ga Sultanan ta Shigo bangaren Umma, ta kuma bi ni har cikin Dakin da na sauka ta iskeni na gama had'a kaya na da na su Asim gabadaya.
Assadiq kawai na ke jira ko sallama bata yi ba haka ta shigo kanta Tsaye.
Na dago ina kallonta cikin mamaki ammh dai ban yi mgana ba.
Sai na maida kaina kan wayata na Bude data muna Chart da Safiya rokonta na ke yi, ta taimaka in na dawo ta rakani cikin makaranta na yi Screening.
Chapter 62 · 0% Book details