Sashe 27
Tmw Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Bayan na gama ci ne na yi sallar Isha'i daman kuma sai da na yi mangariba na ci abinci bayan na idar da salla ina zaune naji tashin murya kamar ta Assadiq a falo kuma chan sai naji kamar harda muryan mijin Anty Surayya.
Ban ko kai da tashi daga inda na ke ba sai gashi ya shigo.
Ina ganinsa na sakar masa mirmishin jin dadin ganinsa.
Shima sai ya maidamin martanin mirmishi kusa dani ya zauna Lokaci Daya ya na kallon kwanukan gabana kafin yace"Lalle kin zama yar gata a wajen Big sis."
Mirmishi na yi kafin nace"Ai ta na da Kirki ne."
Kai Tsaye yace"Shiyasa na fi sonta duk cikin su, ita da mijinta suna da kirki yanzu ma afalo da ita nake yi, Matar nan fa wai batamin magana yanzu Saboda taga agaban mijinta ne har da kukanta wai naja mata zargi a wajen Umma da Sauran yan'uwana."
Ido na zaro kafin nace"Zargin me kuma?
Yana Mirmishi yace"Zargin suna Tunanin Ta san nayi aure ammh ta Boye musu."
Jinjina kai na yi kafin nayi magana ya Rigani da fad'in"Sun ce hakane Saboda susan ba abunda na ke Boye mata abunda ba su sani ba itama yadda suka ji haka itama taji sa.'
Kai na lamgwabar kafin nace"Ai kai ne baka kyauta ba"
Mirmishi ya yi kafin yace"Nasan ban kyauta ai na karb'i Laifina ko?
To ba sai a Tsaya a saurareni ba."
Ni dai ban ce komai ba, sai naji ya Rungumoni ta gefen kafad'ansa Lokaci d'aya ya na fadin"Matar Sadiq ya nauyin jiki kuma?
Dariya na yi ina dukan kirjinsa nace"Nauyin jiki ko Nauyin ka?
Gira ya dagamin kafin yace"Duka na ke mgana."
Dariya muka saka gabadaya ni da shi, ina gefen kafad'ansa ya dafani kamar wata kawarsa ya na min Hira shiyasa na ke son Assadiq saboda Halinsa na kwarai da sanin yakamata.
Acikin Hirar ne ya ke gayamin Abba yace da wuri zamu dauki hanya.
Ina kallonsa nace"abokin naka fa, ka kirasa ne ?.
Kai tsaye yace"Tahir ai ba shi da kirki gaba ya ke yi dani, na yi ta kiransa bai Dauki wayata ba sai na Tura masa sako in yagani shikenan in bai gani ba Shiya sani."
A marairaice nace"Duk Saboda ni ne ko? Ni dai don Allah kada ka bata da abokinka saboda ni."
Da Sauri yace"No kada ma ki saka wannan Tunanin a ranki, ni da Tahir mun saba kada ma ki yi wannan Tunanin."
Ya fad'a daidai Lokacin da wayarsa dake gaban Aljihunsa ta fara Daukan Tsuwwa.
Ni na saka Hannu na Dauko masa wayar na mika masa, ya na Dubawa sai yaga Tahir ne.
Ni ya kallah cikin mirmishi kafin yace"Kinga Mutumin ki ko?
Tahir ne"
Yana fad'a ya na daga wayar kamar Tahir na jira yace a kufuluce"Mallam wani irin sako naga ka Turomin?
Sadiq na jin haka sai ya saka wayar a Speaker ya na Danne Dariyansa.
Shima cikin kai Tsaye yace"Ka karanta mana, ai da Hausa na yi maka Sakon."
Shuru Tahir ya yi kafin yace"Naga wai kace Abba na nemana zamu je Zariya, Mallam baka ji abunda na fada maka Tun Farko ba ne? Ni ba ni cikin wannan Rigimar taka, tunda tun Farko kasan bazan barka ka aikata haka ba shiyasa ka Boyemin Saboda haka Count me out acikin Rigimar ka na gayamaka."
Da Sauri Sadiq yace"Haka zan gayama Abban?
Tahir yace"Bangane ba"
Sadiq na danne dariyansa yace"Abba ne yace na kira ka na fad'a maka zamu je Zariya gidan Baffan Siya."
Tahir yace"Saboda mene? Meyasa sai da ni kuma?
Kai Tsaye Sadiq yace"Saboda kai ne waliyina."
Tahir ya yi shuru bai yi mgana ba, Sadiq yace"Me zan gayamasa? Bazaka je ba?
Tahir yace'"Ban ce ba, d'an sharri sai dai mu Had'u a zariya tunda baka gayamin da wuri ba."
Sadiq yace"Better.."
Daga haka suka yanke kiran ya kalleni ya na fadin"Kin jisa ko? Tahir ai dan renin sense ne."
Mirmishi na yi sai dai ban yi mgana ba, hira ya cigaba da min yana bani Labarin Diramansu da Tahir ina ta Dariya.
Bamu san lokaci ya ja haka ba sai da Mukaji muryan Surayya daga sama kanmu, cikin cogewa a bakin kofar dakin tace"Mallam kazo ka tafi zamu Rufe gidanmu ne".
Ta fad'a lokaci d'aya ta na hararansa, dukkanmu muka kallesa ni kuma kunya ce ta kamani,ina ta noke jikina ganin Assadiq yaki sakina.
Shi ko Surayya ya kallah kafin yace"To tunda zaku Rufe gida ko na kwana anan ne?
Ya fad'a ya na kallonta ita ko sai Faman balla masa harara ta ke yi, yar dariya ya yi kafin ya cigaba da fad'in"Tunda daman gobe zamu yi tafiya daganan sai mu wuce kawai."
Ko mgana batayi masa ba, sai shigowa dakin da ta yi, ni ko ina ta son kwace jikina ammh yaki sakina.
Surayya na zuwa ta duka ta Masa katon Dundu a gadon baya kafin tace"Tashi ka fita kafin na sab'a maka wlh"
Bayansa ya sosa Lokaci d'aya ya na fadin" Big sis."
Kara Dukansa ta yi, ganin haka sai ya bi ni ya kamkameni ya na dariya ni kuma sai na ke fad'in"Anty Surayya ki ce ya sakeni."
Surayya ta Rarumo Filo ta daga sama ta nuna Assadiq ta na fad'in"Sakarta ko yanzu na yi maka Rufdugu a saman kan ka."
Ganin yaki sakina yasa ta fara makamasa Filo ta na fadin ya sakeni sai da yaga dama ya Cikani ta kuma ja hannunsa ta fitar da shi daga dakin ina gani yana Dafa kafadarta ita kuma tana Turesa.
Sai naji sun Burgeni daga gani suna da kyakyawan Fahimta a tsakaninsu.
Ina ta jin hirarasu har na yi barci bansan Lokacin Tafiyar Assadiq ba.
Washegari tun Asuba Anty Surayya ta sakani na yi wanka na Shirya cikin Abaya na Maryam's Eyptian Abaya Tunda yanzu ne kayan sawa na.
Ko kafin takwas na safe na karya na sha Tea sannan na ci soyayyan Buredi.
Tunda tace Sadiq yace ta kaini chan gida da wuri tare muka fita da Mijinta ya kaimu ya sauke sannan ya wuce wajen aiki.
shima yana ta bani baki da nuna min na kwantar da Hankali ba wata matsala.
20k ya bani bayan Anty Surayya ta bani Ruguna bubu da yawa, ga kuma kayan kwalliya har da kayan jarirai Sabbi Overroll, ta kuma Tambayeni ko mun fara siyan kayan Haihuwa? Sai nace mata a'a, nan take tace zata yi ma Sadiq mganar ya kamata mu fara siya tunda Haihuwan ta kusa
Bangarem Umma muka fara sauka, Sabai ne da Saddiqa su Sadiya sun koma gidajensu tun jiya da Daddare.
Na duka har kasa na gaishe su Anty Saddiqa ce kad'ai ta amsa banda Anty Suba'atu.
Umma kuma har ciki Anty Surayya ta shigar dani na gaisheta, kallona ta yi kawai ta kauda kai bata amsa ba sai ma ta tashi ta shige Tiolet ta barmu nan zaune.
Anty Surayya bata damu ba ta Jani har bangaran Mama, in da su Salima duk suna nan suma dai kalilansu ne suka amsamin cikin sakewa kasa kasa suna karemin kallo.
Mama ce ta amsa cikin sakewar har tana ce min ya bakunta? Kaina na kasa nace lafiya.
Muna zaune Shahida ta kalli Surayya kafin tace"Ki ce gidanki ta ke da masauki kenan?
Surayya ta kalleta kafin tace"Ai ba ma ita ba, ni kinsan gidana masaukin baki ne, ballatana ita Asiya ai ba bakuwa bace yar gida ce Tunda matar Sadiq ne."
Sai gabadayansu suka wani tabe baki, mama da Sauri tace"Umma ta hakuran kenan?
Kai Tsaye surayya tace"Umma ai bata isa ta ja da abunda Allah ya tsara ba, ko bata Hakura ba, ba wanda ya isa ya tada wannan kaddaran na auran Sadiq da Asiya"
Duk sai ta kashe bakinsu, daga haka ta yi musu sallama muka fita bayan Salima ta tambayi Surayya tare dani za'a je zariyan? Tace musu Eh.
Daganan sai bangaren Innani chan mukaje muka tarar da Sultana da Siyama.