← Book details Tmw Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 83

Sashe 78

Tmw Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kiran sunansa na yi ya amsa hankalinsa na kan abunda ya ke yi, ina fad'a masa ya kalleni kafin yace"Bansani ba gaskiya, ammh Tahir yace min za su zo shi da Amaryansa abunda za'ayu zan kirasa na tabbatar shin yaushe zai taho?
In cikin sati nan ne sai nace don Allah ya Biya ta Zariya ya Daukota tunda yace min a ranar da za su taho sai ya shiga kaduna."
Da shawaransa muka Tsaya a daran ma yaso ya kirasa na hanashi.
Cikin daure fuska yace"To uban me ya ke yi yanzu? In amarci ne ai ya gama cinye romon tuntuni."
Ina Mirmishin karfin Hali nace"Kada dai ka kirasa, in har kai da ka ke da ni baka gama shanye Romon ba, shima mai auren jiya jiya ai bai gama Cinye Romon ba"
Yana yar Dariya yace"Ina ta ko shan Romo na mai d'an karen dad'i. Ga shi nan sakamakon Romon ne ya nuna a jikin ki.".
Ya karishe fad'a ya na shafa jikina ni kuma na Ture hannunsa na sauke kaina a saman cinyarsa na maida saman Filo cikin Bushewar baki nace"Assadiq sai da Safe."
Saboda bakina yanzu sai ya rika Bushewa har yana fashewa ni dai wannan cikin naga Jalala kala kala.

Sai washegari da Safe ya kira Tahir ya na tambayansa yaushe zai shigo.?
Shi kuma yace abunda zai kaisa kaduna an daga sai wani sati.
Da Assadiq ya gayamin sai nace zan kira Adda Rukayya na gayamata Amna ta shirya sai ta jira Tahir din Sati mai zuwa ya biya ya Daukota.
Haka muka yi dole tunda ba wanda zai Taho da ita, Assadiq ya gayama tahir yace ba matsala ta zo gidan Adda Fati tunda yasan gidan sai ya Biya ya Daukota.
Yanzu tsakanina da Tahir sai gaisuwan mutumci da girmamawa Sannan zumunci na ke yi da Hauwa'u sosai kamar mun zama yan'uwa.
Allah ya taimake ni a satin Safiya ta kirani tace ta raka Mamansu Abuja bikin diyar kanwarta sun kawo Amarya nan cikin garin Abuja.
Tace ta na so tazo sai naji dad'i daman tasan bani da lafiya nan ta ke na Tura mata Address ba dad'ewa sai gata.
Ta yi jimamin halin da ta ganni, duk na tsumaye na rame kamar ba ni ba sai Farin Fata da ido.
Gabadaya kananun jikina sun kara bayyana daman can a baya gyaran jikin na kama sannan kuma cikin ma ba d'aya ba ne da na su Asim
Wanna daga gani in ban yi wasa ba kafin ya girma sai na zama abun Tsoro.
Ita da ta zo min bakunta itace ta Tube ta zage ta gyaramin gidana tas ciki da waje, Assadiq baya samun Lokaci sai Weekend wannan karshen watan ma saboda ni bai tafi Gusau ba.
Ina ji suna waya da Sultana ta na kananun mganganunta da ta saba.
Ya fad'a mata ina da Ciki kuma ya na wahalar dani zai tsaya ya kula da ni.
Nasan dai Sultana na can bakin ciki kamar ya kasheta.
Ta so ta tafi a ranar tunda tace gobe da Safe zasu koma Zariya ni na Hanata tafiya tunda ta kai Dare, har girki sai da ta yi min ta kuma matsamin na yi wanka.
Ni daman ban iya cin komai sai Farar shinkafa ba mai ba manja ba maggi
Hakanan na ke iya turawa in naji kamshin mai ko magi wlh ranar bazan kwana Lafiya ba.
Shiyasa da ta yi mai miya ni sai naci fara hakanan da Assadiq ya dawo shi kanshi yaji dadin ganin gidan da ni kaina.
Allah Sarki har ya Biya ya siyo abinci ni kuma ban yi hausan na kirasa nace kada ya siyo wani abu ba.
Sai fad'i ya ke yi"Safiya kin zo mana Bakunta muna ta saka ki wahala."
Kai Tsaye tace"Ni ai ba bakuwa bace ni yar gida ce, kuma lalura ce fa."
Ina gefen mijina nace"Tun da ta zo bata zauna ba, sai aikace aikace ta ke yi da na yi mgana sai tace ita ba bakuwa ba ce."
Assadiq yace"Gaskiya ne mun gode sosai Allah ya bar zumumci."
Ranar dai bata tafi ba sai da safe suka fita tare da Assadiq zai kaita kafin ya shiga Office.

Sai naji kamar kada ta tafi ammh ba Dama tunda mamansu na ta kiranta za su tafi da wuri, jin ma ba ni da lafiya ne yasa ta barta ta kwana kuma Safiyan ta bani ita mun gaisa ta yi min sannu.
Na gayama Amma bani da lafiya ammh ban gayamata ciki gareni ba, ita da kanta ta gane sannan sun yi mgana da Adda Fati ita ta gayamata zencen zuwan Amna wajena.
Amma ta kirani ta na cewa"Ko dai Habiba tazo wajen ki ne, ni nan ba wani abunda ta ke yi min naga zata fi Amna amfani tunda ta fita shekaru."
Ni kuma ganin Habiba bata taba zuwa ta jima wajen Amma ba yasa nace ta kyaleta kawai ai ba wani abun wahala ba ne Tunda Adda Rukayya ta bani Tabbacin Amna zata yi min komai in dai ba mai wahala ba ne.
Sai Amma tace shikenan Allah ya kara lafiya.
Kafin mu yi sallama sai da tace"Ina Mazajen nawa? Ba sa cefane kuma ba sa zuwa zence?
Ina dariya nace"Amma suna gusau ba su dawo ba."
Amma tace"Kin huta da yanzu ai aikin ya yi miki yawa"
Kai tsaye nace"Ai nace su yi zamansu can sai na warke Amma bazan iya ba ji na ke yi kamar zan mutu."
Amma tace"Ki bar cewa Haka Haseta. Haka kowani ciki ya ke da na shi Tarnakin Allah dai ya sauwake ya kuma Raba lafiya."
Sai naji kunya amsar ma a sannu na amsa ta.

Mun gama waya da Amma kenan sai ga kiran Umma itama muka gaisa ta gaisheni tunda ko jiya ta kirani ta gaisheni da jiki.
Ni da kaina na ke gayamata diyar yayata zata zo ta taimakamin
Umma tace"Eh gwara haka ko ya ya mutum ya ke ai Rahama ne. tunda ga su Asim a wajena."
Cikin karfin hali nace"Umma su sha zamansu wlh, in suka dawo bazan iya da su ba."
Umma na dariya tace"Jiya ai sun yini Hiran Mami, Jiya Asif da rigima ya tshi ashe zazzabi ke jikinsa sai da na bashi mgani"
Sai na ke gayama Umma su Asim ba su cika yawan ciwo ba sai dai ko zawon Hakora da suka yi ta fama da shi Shima din bai ba su wahala sosai ba.
Kaf yayayen Assadiq ba wacce bata kirani ta yi min sannu ba, Hatta Sadiya itama ta kirani ta min sannu Sajida kuma daman tunda muka daidaita lokaci bayan Lokaci muna mgana.
Allah sarki har ce min ta yi in ina so sai ta yi ma Umma mgana ta zo ta taikamin, ni kuma kunya da nauyi suka saka nace ta yi zamanta bakomai.
Bazan iya kwanciya yayar mijina na Hidima dani ba abun akwai wani iri aciki.
Da na gayama Assadiq ma a lokacin Dariya kawai ya yi kafin yace"Ikon Allah Su Sajida an zama gama garin zawarawa."
A lokacin da ya fad'i haka sai da nace"To wai bazaku iya gyara Lamarin ba Assadiq?
Assadiq yace"Abba ya zauna da shi, laifin fa duk na Sajida ne ko za'a gyara sai in shi mijin ne ya dawo yace zai maidata kuma abu ne da ya had'a da Uwa dole kuma ya yi ma mahaifiyarsa Biyayya, ni tausayinta na ke ji ya'yanta Uban duk ya rabata da su Yar kibar nan ta Sajida duk ta ta fi, bakin nan nata da baya shuru da Had'e had'e rayuwa ta gama nuna mata gaskiyan da ake gayamata bata Dauka ba, duk ta zama wata a firgice."
Ya na wannan mganar ina Hasaso abunda ya faru dani Lokacin da Abubakar ya sakeni.
Kusan zauncewa na kusa yi, na fita Hayyacina kai Allah ka raba kowata mace da kaddaran sakin aure da zawarci.
Kamar yadda muka Tsara Tahir ya Biya ta Zariya ranar Wata alhamis ya Taho min da Amna.
Da ya ke wani Taron siyasa ya karfafa ma Tahir shigowa Abuja kuma daman Hauwa'u ta matsa zata Biyosa ta zo wurina yasa ya zo da ita.
Sanda suka iso Assadiq na wajen aiki shima yana sauke su ya wuce inda zaa shi.
Dakin da Sultana ta sauka na sauke Amna da Hauwa'u.
Hakuri na ba ma Hauwa'u na Roketa ta shiga kitchen ta da fa musu wani abu su ci ni dai ba na iya moran kaina Ballatana na Morama wani.
Hauwa'u tace"Haba bakomai bari na shiga na girka"
Da ta tambayeni me zata girka nace abunda zai fi sauki tunda tafiya suka sha. Ni kuma na shige daki na kulle kaina saboda kamshin girki in na shaka ba zaman lafiya.
Ina da sauran miya tun wanda Safiya ta yi ne kafin ta tafi, Sai ta dafa musu Taliya fara suka ci da miya.
Ni kuma na Tura gaya hakanan na sha Ruwa.
Amna kuma ta shiga kitchen ta na wanke wanke, Adda Rukayya ba ta wasa sosai ta ke koyama ya'yanta ayuukan gida saboda Rayuwa.
Muna falo ni da Hauwa'u muna ta Hira, ta na gayamin taji dadin kayan gyaran da ta siya hannun Surayya Dee.
Ni na had'a su tunda na gayamata ingancin kayan tace taji dad'in mganin sanyin nan tare da tsumin nan, ita yanzu kazar Amare ta ke so ta kara siya taci.
Ina daga zaune nace"Ki siya wlh kazarta na da kyau, kuma ta na jimawa a jikin mace ta na aiki, nima fa na so na kara siya sai kuma ga Laulayi da gudu na watsar da su na yi ta kaina."
Hauwa'u na min dariya tace"Result din gyara ne kika gani fa Madam"
Ina jin miyau ya Taru a bakina nace"Uhm ai naga gyara sosai."
Ni na gayamata Surayya ta fara Dahuwar Tatattabaru sosai kuma suke da inganci nan take Hauwa'u tace zata yi mata mgana ta na so.
+234 803 277 3332.
Chapter 78 · 0% Book details