Sashe 36
Tmw Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Tunda Lokacin da mutane suka kawo agaji a wajen da akayi hatsarin an samu dai an cirosa daga motar sai dai wayarsa ta fashe, ta cikin motar aka ga I.d card dinsa na wajen aiki sai wani jami'a cikin jami'ai masu kiyaye had'ura na titina Road Safey da suka zo wajen
ya dauki lambarsu ya Kira su ya gayamasu bayan ya yi musu bayanin sunan ma'aikacin nasu.
Su kuma daman suna da duka bayanan ma'aikatan su kuma bayan Lambarka kana saka wata lambar ko na mahaifi ko mahaifiya anan suka samu lambar Abba suka kirashi suka sanar da shi abunda da ke faruwa, sannan suka ce za su Turamai lambar jami'in da ya kira su.
Kawai gani suka yi Abba ya mike yana ta jera Uban salati.
Da Sauri Umma da mallam Zakari suka mike suna tambayan lafiya?
Innani kuma har ta fara gyangyd'i kamar daga Sama taji Abba na fad'in"Abubakar ne wai ya samu Had'arin mota yanzu daga ma'aikatarsu ta chan Abuja suka kirani suna fad'amin."
Sai ga innani ta fado daga kan kujera ta na fadin"Na shiga uku ni Dije, wani Abubakar din ba dai magajin gida ba?
Umma kuwa kasa ta koma ta zauna Dabas ta Dora hannu a saman kai ta na fadin"Shikenan abunda na ke gudu ya faru, na shiga uku na lalace wayyo d'ana."
Mallam Zakari kuwa salati ya saka yana tambayar Abba a ina abun ya faru? Abba yace ba su yi masa wani karin bayani ba ammh sun ce za su turo masa lambar jami'in da ya Kirasu sai ya kira yaji a ina ne? Kuma sannan a wani Halin Sadiq din ke ciki.
Abba jikinsa na rawa ana Turo lambar ya latsa kira bayan bayanin shi mahaifin Abubakar ne wanda ya yi hatsari yanzu aka kirasa daga ma'aikatarsu na Abuja kuma su suka Tura masa lambarsa.
Jami'in yace"Hatsarin ya faru a tsakanin barin kaduna ne zuwa Abuja, kuma mara lafiyan yana asibitin Sojoji na 44 da ke kaduna za su iya zuwa domin ganin Halin da ya ke ciki."
Abba da mallam Zakari ko Tsayawa jin ta ihun su Innani ba su yi ba suna fita Direba daman yazo ya na jiran Abba za su fita kawai suka fad'a mota Hankali tashe.
Sai bayan fitarsu ne Umma ta fito ta na kuka ta yi shashen Mama ta na fad'a mata abunda ke Faruwa.
Mama ta Rude' fad'i ta ke yi"Mun shiga uku, a ina abun ya faru?
Umma na kuka tace"Bansani ba, Abban siyama da Baba da yazo da Safe sun fita ba su yi mana wani bayani ba."
Mama itama sai hawaye hankula suka tashi ita Sultana ihun Innani ne ma ya fito da ita a haraban gida ta na kuka da jiniya ta na fad'in"Bala'i da Annoba sun sauka a rayuwar magajin gida."
Siyama ke gayamata ta na kuka cewa Yaya Sadiq ne ya yi hatsari.
Itama nan da nan ta rud'e daman kuma ta gama kukan fad'an babanta kenan sai kuma ga wani bakin Labari.
Kafin wani Lokaci gabadaya wannan Ahali na nesa da na kusa sun san abunda ke faruwa yan kusa kuwa irin su Surayya, Sadiya, Sajida Sa'ima, sakeena, Sa'adatu duk sun hallara na nesa kuwa irin su Saddiqa da su saliha sai faman kira suke suna tambayan yadda ake ciki.
Abba kuma yace suna hanya har Lokacin ba su isa kaduna ba.
Hankali sun tashi, Innani kuka ta dinga yi ta na fadin in Magajin gida babu shi ne gwara su fad'a mata ta san gaskiyan mgana.
Umma kuwa har sai da idanuwanta suka sauya muryanta ya dishe, Surayya ma ta yi kuka kamar mene, sai dai ita ke ta faman waya da su Abba tana ce musu suma ga su nan za su taso ammh kuma Abba ya hana yace su dakata su fara isa su ga Halin da ya ke ciki.
Sultana kamar mai aljanu sai shidewa ta ke yi, kawai ta na Tuna rashin kunyar da ta yi masa ne ranar kafin tafiyarsa.
Su sajida kuwa ko duba Halin da ke ciki ba su yi ba fad'i suke yi shikenan Sadiq ya Dauko abunda zai kashe shi ba karya komai ya Faru da shi silar wannan bakar Annoban da ya kwaso musu ne.
Umma dai sai kuka bata mgana su Baba sammani ma Tuni sun samu Labari dagachan suma suka ce za su wuce kadunan domin su ga Halin da ke aciki.
Abba sun isa kaduna wajen uku na rana ne, shima domin Direba ya yi gudu ne sosai suna zuwa asibitin 44 shashen Emergency suka nufa Tunda suna ta waya da wannan jami'in yace tare da shi aka kawo Sadiq asibitin shi yaje ya Dauko yan Sanda Tunda cases ne na hadari sai da jami'an Tsaro zasu karbesa.
Sun je sun iske har alokacin Sadiq na Emergency, sai dai yana nan a raye ammh kuma ya samu Raunika, akwai karaya a hannunsa na dama sai kuma karaya a kafar dama sai kuma Raunin da ya samu a kansa da gefen fuskarsa sai kananun Rauninka a sassan jikimsa.
An gode Allah ma tunda ya farfado sai dai baya cikin hayyacinsa sannan sunce Hoton kansa za su yi zuwa Gobe su gani ko Buguwar ta tab'a cikin kansa.
Abba da mallam Zakari sun shiga sun gansa sai ga Sadiq halitta duk ta sauya kansa duk ya kumbura.
Abba ma sharan hawaye Mallam Zakari na sharan hawaye.
Jami'in shi ya ba su kayan Sadiq da suka samu a motar wayarsa da I.D card ,key din mota sai Wallet d'insa mai Dauke da kudi da Atm din bankunansa sai wasu Takardu.
Allah yasa an yi saurin adanasu da tuni an nemesu an rasa.
Suka rabu da su Abba suna yi masa Godiya bayan Abba ya yi masa ihisani.
Shi ya gayamusu ba Motar ta da gogesa kawai motar ce ta kwace masa, kuma in da Abun ya takaita ba wata mota mai zuwa a gaba da abun yafi haka Muni.
Abba bai san yana iya kuka ba sai da yaga Sadiq cikin wannan Halin, shiyasa ko da Surayya ta kara kira ya kwantar musu da Hankalin cewa Sadiq na raye kuma jikinsa da Sauki shi yace kada su taho su bari sai gobe ko Jibi.
Su Baba Sammani ne Tunda sun taso bai hanasu zuwa ba, suma sai yamma suka iso Abba me ke ta shiga yana Fita zuwa Lokacin har Alhaji Jibril da Mubarak da salima suna asibitin, salima ta yi kuka kamar ranta zai fita , tunda su ke ba su taba ganin tashin hankali irin shi ba, duk wanda yaga Sadiq a wannan Halin sai ya Zubar masa da kwallah shi Abba ya sakaya abun, ammh Salima da suka yi mgana da Big sis ta na kuka tana gayamusu halin da dan'uwansu ke ciki, tace ma yanzu a daran nan Hoto kansa za'a yi masa tunda ya samu Buguwa a gani ko buguwar bai shafi kansa ba.
Sai gida ya kara rikicewa, da koke koke duka ba wacce ta yi shirin komawa gida nan suka kwana da kuma Shirin gobe da safe za su bi bayansu Abba suma su ga halin da Dan'uwansu ke ciki.
Tahir ma a daran Surayya ta kirasa ta na gayamasa abunda ke faruwa ya Rud'e daman kuma yana katsina ne yace gobe zai biyo motar asuba zuwa kaduna in sha Allahu.
Mallam Zakari da su Baba Saminu har Abba ma a gidan Alhaji Jibril suka kwana tunda su a tsarin asibitin ba'a kwana da majinyaci sai dai gobe da Safe mutum ya dawo, kuma yana cikin Emergency har Lokacin ba'a Fito da shi ba an samu dai an yi masa Hoton kan sakamakon ne sai a washegarin zai fito.
Alhaji Jibril fadi yake yi"Sai da daman nace, yarinyaar nan auranta ba alheri ba ne, gashi ta saka yaron nan cikin jarabawa."
Su Abba dai suna ta Sadiq ba su ko Biyema Alhaji Jibril da manganunsa ba.
Dagachan Gusai ba su yarda sun gayama su Abba suna tafe ba, Mijin Surayya ya dauketa ita da su Umma da Mama da Innani sauran kuma mijin Sa'ima ya Tuka su, sai kuma Direban mijin Sadiya shima ya ba su mota dai uku duka kuma gidan suka tafi, megadi kawai aka bari mallam Taju ya na binsu da Fatan isa lafiya da kuma Allah ya tashi kafad'un magajin gida.
Da azahar suka isa can suka iske Tahir ya iso shima Tun safe sai dai sun samu hankula sun kwanta Tunda sakamakon Hoton kai ya fito kuma komai Normal buguwar ba ta shafi kwakwalwar kansa ba.
Kuma an fito da shi daga Emergency zuwa daki na musamman Cuwukan ne kad'ai suka samu Dressing ammh karayan ba'a Daura shi ba Abba suna ta shawaran in da za'a bar shi ko anan din ko kuma a kaisa asibitin dala kano a yi masa Daurin asibiti.
Har alokacin Sadiq barci ya ke yi a wahale sai dai ance da safe ya farka yana ta kukan kansa.
Dukkansu matan nan da kuka suke Fitowa daga dakin nan Sultana kam ta kasa shiga ma saboda tashin Hankali a ranar ma sai ga su mallam Shitu da su Goggo Hassu sun zo suma cikin Tashin hankali.