← Book details Tmw Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 83

Sashe 69

Tmw Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sultana kuma ko ta na dashi bazata bata ba, tunda ta taba rokonta 5k tace itama ai d'aya suke tunda Mijinta baya tare da ita yana can tare da kishiya.
Kuma tasan ta na da kudi Sadiq ba mutum ne mai mugunta ba.
Umma kuma bata ko bi ta kanta ta na ta yi ma Sultana Shirye shiryen komawa gidanta cikin satin nan.
Ta kuma siya mata kayan gyara na abunda uwa zata yi ma yarta, daga Shinkafi ma Matan Babanta sun aiko mata da mganin sanyi da Tsumin Amare.
Itama ana ta bangaren da Taimakon  Surayya ta gyara Sultanan sosai, kuma ta yi mata kyakyawan Jego mai kyau ta maida jikinta ta yi sharr  ita da Ummi.
Sadiq ya yi waya da Umma zai dawo ranar jumma'a.
Suna zaune a falo a daran Laraba ita da Sajida ita Sajida wayarta ke hannunta ba ko data game ta ke yi ta na rage zafi.
Ummi na bayan Ummi ta goyata bayan ta gama yi mata wankan yamma sai ta samu barci.
Sultana kuma tunda ta shiga ciki sallah bata fito ba.
Umma ta yi zaune ta na kallon Sajida ta na kara nazarinta kamar ta na bata Tausayi ammh bata so ta nuna mata tana jin Tausayinta.
Kuma har Allah ta ga abunda Mallam da Sadiq suka rika gayamata.
Ba ita ke da littafin kaddara a hannunta ba  Allah ne itama ko ita kanta bata wuce zama bazawaran ba.
To ga shi bai faru da ita ba ya Faru a kan yarta itama Sajida ta na daga cikin masu kyaamatar bazawara da aibata kaddaran da ba mutum ya zana ma kansa ba.
Sajida duk ta rame ta yi baki kamar ba ita ba, Umma ta sauke ajiyar zuciya kafin tace"Sajida wai nace baki kira shi Yusuf din ba ne?
Sajida ta kalli Umma cikin wani yanayi kafin tace"Umma ya ma daina daukan wayata yanzu, yana so na fa duk sharrin kannensa ne da uwarsa."
Umma ta kalleta kai Tsaye kafin tace"Uhm ashe har yanzu da Sauran ki ban sani ba Sajida?
Sajida ta tura baki kafin tace"Umma to ni me na yi? Har da ya'yana sai ya rabani da su?
Sai idanuwanta suka ciko da kwallah tana kaunar ya'yanta Damuwarta akansu ma tafi yawa, tunda ta yi aure ba ta taba kawo ma kanta zata iya dawowa gida ta zauna da sunan wai mijinta ya saketa ba, hasashen da bata tab'a yin kamarsa ba.
Ganin abun ta ke yi kamar a mafarki, kuma tabbacin ba mafarki ba ne.
Suna nan zaune sai ga Sultana ta fito tana fad'in"Umma yaushe zan tafi Shinkafi na kai ma Baba Ummi ya ganta ne?
Umma tace"Sai ki jira mijin ki ya dawo in ya barki duk sanda kika Shirya sai ki tafi."
Kai Tsaye Sultana ta zauna kusa da Sajida ta na fad'in"To Umma shikenan ma sai Anty Sajida ta rakani saboda Daukan Ummi."
Daga Umma har Sajida sai da suka kalli Sultana ita ko har acikin ranta ta yi mganar.
Umma ta kauda kai ta na fad'in"Sai kuje tare itama ta kwana Biyu ba ta je ba"
Sajida na gefe ta bi Sultana da wani kallon Lalle ma yarinyar nan..
Cikin gatsali tace"Ke ba inda zani."
Sultana ta kalleta cikin mamaki tace"Saboda mene?
Kawai sai Sajida ta mike a fusace ta na fad'in"Bansani ba mara kunya kawai."
Ta fad'a lokaci daya ta na wucewa cikin Daki a fusace.
Suka bi ta da kallo Sultana ta kalli Umma Lokaci d'aya ta na fadin"Umma me ya samu Anty Sajida kuma?
Umma ta ce"Ina zan sani, me yasa baki bita kin tambayeta ba?
Sultana ta tabe baki kafin tace"To ni me na yi mata da zata ce min bani da kunya?
Umma na jinta ta na kunkuni bata tsnka mata ba, ta yi kamar ba ta ji ta ba.
Ganin Umma ba ta bata fuska kan mganar Sajida ba yasa ta sauya Hira da fad'in"Umma zan sha yawo har Abuja zani fa."
Umma ta kalleta a karkace kafin tace"Gidan wa zaki je a abuja?
Kai Tsaye tace"Gidan mijina mana, kema Umma da wata mgana ina da inda zan je da ya wuce gidan Yaya Sadiq na Abuja."
Umma ta gyad'a kai kafin tace"Na sha'afa ne, Allah ya kai ku lafiya."
Ta amsa da Ameen sai ta fara yi ma Umma korafin Sadiq wajen wata daya da sati bai zo ya gansu ita da Ummi ba tun bayan suna da ya tafi.
Cikin Kishi tace"Umma don ina adalci anan, sai kuma yazo ya yi kwana Biyu yace zai koma sai mutum ya yi mgana aga laifinsa."
Umma na zaune kala bata ce mata ba har tagama mganganumta.
Ummi ce ta tashi ta kuma fara kananun Rigima yasa Umma ta sauko mata yarta ta bata.
Ita kuma tace bari ta shiga bangaren Innani ta dubata.
Kai Tsaye Sultana tace"Allah Sarki Innani, ki gaisheta jiya ma ban shiga na gaisheta ba."
Umma ta harareta kafin tace"ni ce yar aiken ki? In ko da Amana bai kamata Ruwa ya Dafa kifi ba, ace kina gida nan ki yini baki iya leka innani acikin gidan nan ba."
Sultana ta tura bakinta gaba kafin tace"Umma ban samu lokaci ga makaranta ga kula da Ummi."
Umma ta kalleta ta watsar ta yi ficewarta ta bar sultana ta kunkuni ita ya zata yi? Ko dame ake so taji.
Ba sosai yanzu ta ke zuwa bangaren Innani ba tunda ta fara rashin lafiya sai taga dama.
Kuma in ta shiga a tsaye ko zama bata yi, Ita kanta Innanin ta san cewa Sultana ta sauya ita saboda ta kanta ta ke yi bata cika ma damuwa da ita ba.
Washegari da Safe Umma tace Sajida ta dauki Farida su je gidan sultana su gyara mata gobe jumma'a zata koma gidanta.
Sajida ta kalli Umma cikin mamaki kafin tace"Umma ni kuma?
Umma tace"To da wa zan saka? Ku tafi da wuri saboda ku samu ku gama gyaran akan lokaci."
Sajida tace"Umma idda fa na ke yi? Kuma a musulunci ni matar Yusuf ne har yanzu"
Umma tace"Kaniyarki da Iddan, ina saka ki aiki kina cemin kina Idda ne, in matarsa kike me ya zaunar da ke a gabana! Da sai ki zauna gidan Yusuf din ki gama Iddar taki."
Ranar Sajida da kuka ta fita, Sultana na daki ta na jinsu ta na dariya.
Lokacin ma tana waya da kanwarta ne mai bi mata.
Tana fad'a musu zata zo in Yaya Sadiq ya zo ya koma zata zo ta yi sati a shinkafi.
Sajida ba ta da mafita dole ta yi abunda Umma ta sakata.

A gidan Sultana ita da Farida sun ci aiki Tunda gidan ya ji ma kulle duk ya yi kura.
Suna cikin aikin Sadiya ta kirata tace gata nan tazo gida Umma tace ta na gidan Sultana suna gyara.
Sajida tace"Sadiya kinga yadda Rayuwa ta yi dani ko? Na zama yar aikin Sultana ina yayar mijinta na koma kamar kanwar mijinta."
Sadiya tace"Tabdijam, Allah ya kyauta."
Da Sajidan tace Sadiyan ta zo nan gidan su had'u sai ma ta tayasu sai tace megidanta ya yi tafiya daga kasuwa ta biyo gidan Umma gida zata koma zata yi masa girkin Tarba.
Kiri kiri Sadiya ta wucewarta gida kuma Umma ma da ta yi mata mgana haka tace mata.
Sultana kuma Saloon taje bayan ta dawo ta biya gidan kawarta ita ta rakata gidan kumshi aka yi mata.
Sai Yamma Sajida ta dawo sun gaji ita da Farida.
Suna dawowa ba dad'ewa Sultana ta Dawo Umma na ta fad'an ta yi dare ga jaririya a bayanta.
Kai Tsaye tace"Umma kunshi fa naje, haka zan koma jiki fari."
Umma ba ta yi mgana ba Sajida ma da idar da sallah bata tanka mata ba.
Umma taso ta tusa ma Ummi sai taga ta tashi tace zata shiga wajen Innani daganan ta wuce shashen Abba.
Mama bata nan suna kano bikin diyar kanwarta bangarenta kulle ya ke ba kowa.
Kawai sai ta isa gaban Sajida ta mika mata ta na fad'in"Anty Sajida ga yarki, ban yi sallar azahar ba ballatana mangariba."
Ko kallonta Sajida bata yi ta mike lokaci daya ta na fad'in"Salla zan yi, kin ji an fara kiran sallar isha'i."
Daga haka ta kabbarta salla tabar Sultana tsaye rike da yarta.
Chapter 69 · 0% Book details