← Book details Tmw Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 83

Sashe 44

Tmw Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bayan bayan sun dawo daga sallar Mangariba Shi da Abba, sai Abba ya wuce bangarensa shi kuma sai ya Shiga bangaren Innani ya kara gaisawa da baki suka taba Hira sama sama daganan ya baro su zuwa Shashen Abba ya ci karo da Sultana Tunda aka yi haihuwar wannan ne gani na Biyu da ya yi mata.
Ganin Farko zasu tafi makaramta ta gaisheshi ya amsa fuskarsa a had'e.
Sai kuma yau abunda ya bashi mamaki bata yi masa barka ba daman kuma baya Tsammanin haka Daga gareta Shifa tunda ta nuna masa bata da kunya ya fita sha'aninta..bazai zauna yarinya karama na wasa da Tunaninsa ba.
Kallo daya ya yi mata ya dauke kansa ya so ya wuceta ne sai yaji ta na gaishe shi sai ya Tsaya kad'an yana amsawa.
Kuma ya tsaya ne yaga ko zatayi mgana yaga kuma ta wuce bangaren Umma ya bita da kallo.
shifa yanzu an gama kuresa bazai kara matsa mata ta koma ba, ta yi ta zama tana Biye ma Umma har sai Lokacin da tagaji da ganinta a gabanta tace ta koma shidai kam ya Riga ya gama Tsara matakin da zai Dauka.
Bangaren Abba ya shiga cikin sa'a kuma sai ga Umma da Abba sai Sadiya da Sajida daman dazu yaji muryoyinsu a shashen Umma da Rana shiyasa yaki shiga.
Shifa Tun da yaji Labarin abunda suka aikatama Siya yaji baya son ko ganinsu bai kara yarda sun had'u ba kuma ya gama sanin duk masu kaunarsa acikin yan'uwansa da wad'anda suka kirasa suka yi masa barka da wad'anda suka ja da Hukuncin Ubangiji duk ya san su, kuma ya yi ma kowaccen su wajen zama.
Umma ce kadai bai riketa a rai ba Tunda ita c din sha Kudun ce uwa ce bashi da yadda zai yi da ita ammh su yana da yadda zai yi da su, tunda ba wacce ta haifesa acikin su. Sannan ba wacce ta taba daukan Laluransa ballatana iyalansa.
Ko a hidimar suna nan da kudinsa ne na banki tunda duk wattanin da ya yi yana jinya ma'aikatarsu duk wata suna saka masa albashinsa.
Sannan Abba shi ya ba shi kudin Raguna duk da yace ya barshi ammh yace kada ma yace komai.
Da su ya samu ya yi hidimarsa sannan ya Tura ma Tahir kudinsa da ya ara lokacin haihuwar siya.
Sanda ya shigo ba su san da shigowarsa falon ba tunda yanzu in dai acikin gida ne baya tafiya da sanda ya fara lallaba tafiya hakanan.
Sai in har zai yi tafiya mai nisa ne ya ke dogara sanda.
Ba su san ya shigo ba ya yi tsaye a kofar bangaren Abba da farko ma kamar ya koma sai dai mganar da yaji Sajida na gayama Abba ne yasa ya Dakata.
Karan Surayya suka kawo domin ba su da kunya.
Domin sunga Abba ya yi musu Shuru haka ma shi ma, da ita kanta Surayya shiyasa suke Tunanin ba wanda yasan abunda suka aikata.
Mgana suke akan taki saka su cikin Lissafin wad'anda za su tafi suna Zariya gobe Sajida ta kirata a waya taki Dauka kuma taje gidanta ta yi mata wulakanci shine suka zo suna gayamai ta ya ya zata ware su, ai suma yan'uwan Sadiq ne.
Tsabar yadda mamakinsu ya kamashi sai da ya murmusa yana tsaye.
Abba ne ya hangosa sai ya kira sunansa.
Dalilin da yasa suka san yana falon kenan duka suka waiga suna kallonsa.
Umma kuma na gefen Abba,  ita su Sadiya suka fara samu da mganar tace su gayama Abbansu itama Surayya ta rainata yanzu sai tazo gidan nan bata nemeta ba.
Itama tana so Abban ya tambayeta hala ita ce uwar sadiq din? Domin taga ta zake da yawa akan Lamarin shi da bakar Annobar yarinyar nan. ita fa ba yan Biyu ba ko yan goma ta haifa ma Sadiq bazata kaunaci bala'i da Annoba a kusa da magajin gida ba.
Kuma ganin daga Sadiq din har Abba sun yi banza da ita basa ma mata maganar sai ta fara rena kanta itama ta kwaso kananun maganganunta bata ta san zata bare da su ba.

Karisowa falon ya yi yana gaida Umma, rabon shi da ita tun safe ta amsa lokaci d'aya takallesa kafin tace"Ya karfin jikin naka?
Ya amsa mata da Alhamdulillah.
Umma ta mele baki kafin tace"Ka dai rika Hutawa ina lura da kai cikin kwanaki nan baka san zama waje d'aya kada dai ka manta har yanzu jinya ka ke yi baka gama warkewa ba."
Abba na gefe ya yi yar dariya kafin yace"ina shi ina Hutawa baban yan Biyu ne fa, abun alheri ne ya same shi fa sai ki ce ya koma ya zauna kuma salamatu"
Jin Abunda Abba yace ne yasa Umma ta kasa mgana.
Sajida ce ta kalli Sadiq kafin tace"Sadiq ba mgana"
Kallonsu ya yi dukkansu a dage kafin yace"Sannun ku."
Sadiya ce tace"Wai ya sunan yaran ne?
Domin sun ji kishi kishin sunan yaran, har Umma suka fesama ammh bata ce musu komai ba.
Shi kuma da gayya yace"Sulaiman da Muhammad"
A tare suka had'a baki wajen fad'in"Allah ya raya."
Dagaji ba har zuciyarsu ba ne.
Shuru suka yi gabadayansu ransa sai ya fara baci ganin suna ta kuskus har ya mike kome ya Tuna sai ya koma ya zauna ya na kallon Abba kafin yace"Abba daman ina so mu yi mgana."
Abba ya gyara zama yana kallonsa kafin"Ina sauraranka Abubakar"
Sadiq ya gyara zama yana fadin"Lokacin da Hatsarin nan ya Faru dani ka samu Labarin Sadiya da Sajida sun bi matata har zariya sun ci mata Mutumci da Tsohon ciki suka koreta suka kuma kwace makulin dakin da wayarta har da Atm din bankinta? Ko ka samu Labari?
Abba ya jinjina kai kafin yace"Tabbas na samu labari. Surayya ta sanar dani komai tun a lokacin."
Ya fad'a ya na kallon Umma da ta Tsargu ta sunkuyar da kanta
Su Sajida kuma sai suka fara Zare ido.
Cikin gyada kai Sadiq yace"Yauwa daman dalilina na yin shuru ban Dauki wani mataki ba shine ina fama da jinya sannan aka zo aka yi ma Siya aiki na samu karuwa, kuma ni daman na Riga na gama Tarasu ne Abba zan yi musu iyaka da iyalina kada kace ban kyauta ba."
Kai Tsaye Abba yace"Ka yi musu duk abunda ka yi ra'ayi, domin wannan karin nima sai naci mutumcinsu Tunda sun Tsallake Hurumin da ba na su ba."
Jin haka yasa Sadiq ya mike Zumbur ya nuna su Sajida da yatsa kafin ya fara fad'in"Wallahi Tallahi kun ji rantsuwar d'an musulmi in dan ku ka kara shiga Hurumin matata sai na saka Shari'a ta yi min iyaka da ku gabadayan ku."

A razane suka kallesa Sadiya tace"Eh Saboda mace za ka saka shari'a ta yi mana iyaka fa kace Sadiq?
Kai Tsaye yace"Kwarai ma da gaake, ai ko a yanzu sa'a kuka ci wani abu mara dad'i bai samu matata ba da na rantse da wanda raina ke hannunsa sai na yi kararku, kuma kunsan Tsab za'a hukuntaku saboda kun Shiga Hurumin da na  ku ba, uwa uba kuma kun ci zarafinta a matsayinta ta yar Adam kuma yar kasa."
Mamaki ya hanasu kara mgana sai kallonsa suke yi baki bud'e.
Umma kuma sai Harara ta ke jifanshi dashi baisan tana yi ba.
Cikin Fushi ya Cigaba da fadin"Ina ruwan ku da ita? Ko ku kuka auramin ita ? Ba wanda ya taba taimkamin da sisin kwabo wajen Rike ta, shine kuma zaku rika shiga cikin Rayuwata kuna min katsaladan? A kan wani Dallili na saka ku ne? In ku baku yarda da Allah ba ni na yarda da shi na kuma san duk abunda ya Faru dani mai kyau ko akasinsa daga Ubangijina ne Siya bata isa ta zama Silar faruwar wani abu gareni ba face abunda Ubangiji ya kaddaramin, Kashedi na gare ku shine ni ne dolen ku, dani ku ke da alaqa ba da ita ba, so ban  yi ma kowa Dole ya karfafa alaqa da Siya ko ya'yana ba, ku kyale ni da su ni ne Dolensu ita din matatace ni ya kamata na kula da Hakkokinta tare da Amanarta, ban kuma ce kowacce taje ta yi mata barka ba, ban kuma ce nima ku yi min ba, duk ku je na yafe wanda yaga dama ya yi abu mai kyau kansa ya yi mawa ba ni ba, ni dai karfafan Kashedi na shine ba Ruwan ku da matata in kuma baku ji ba ku sake Shiga harkaarta ku ga yadda Shari'a zata Shiga tsskanina da ku."
Sajida sai ta saka kukan munafunci ta na fadin"Abba Umma kuma gani dai ko? Kuna ji yana fadin zai yi shari'a damu Saboda matarsa ko? Ai dai mu ci Darajan mu yayyensa ne muna gaba da shi."
A fusace Sadiq yace"In kun girmeni ai baku halliceni ba? Ko kuma domin kun girmeni sai na zauna kuna min cin kashin da kuka dama?
Ai girma ba Haihuwa ba ne, bazai hana naci zarafin duk wanda yace ni zai ci nawa zarafin ba, ko da akace bin na gaba na tare da Bin Allah, in babba bai kama girmansa ba karami na daidai da ya taka girman babban ya wuce abinsa."
Chapter 44 · 0% Book details