Sashe 23
Tmw Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ba gefen Sadiq na nufa ba sai nufa ta bangaran Damansa zan zauna sai naji Bayana ya kage, ina cije baki wajen na gyara kafata sai naji na Turgud'e kamar zan fadi.
Kamar kiftawan Ido sai gani a Hannun Assadiq ya Rikoni cikin Sauri bakinsa na rawa yace"Siya ki kula fa.'
Ya ke fad'a ya na kallona, Kaina na kasa ganin gabadaya falon ana kallonmu cikin Saurin na zame zan zauna da Sauri Assadiq ya kalli Abba ya na fad'in"Abba ka yi mata izini ta zauna saman kujera saboda lalurar da ke tare da ita."
Da Sauri Abba yace"Ta zauna mana, ai ta na da uzuri, zauna zauna Bismillah"
Abba ya ke fad'a da Sauri ko Sadiq ya zaunar da ni gefen Abba kunya ta kamani cikin sanyin muryata nace"Assadiq.."
Shii..!
Yace ya na kallona sannan ya Girgizamin kai, Dole na yi shuru sai da na zauna sannan ya duka ya mikar min da kafafuwana Lokaci daya ya na fadin"Ki bar su a mike su d'an sake kinga sun kara kumburi."
Ni dai kunya da wani irin nauyi sun hanani Dagowa, shi kuma ko ajikinsa sai ma tashi da ya yi ya koma bangaren Hagun Abba in da ya tashi ya zauna duk da yasan shi ake ta kallo ammh bai yarda ma ya Daga kai ba, ballatana ya kalli wani acikin su.
Sultana ce suka had'a ido ta yi masa wani rin kallon, shi kuma sai ya kafeta da ido domin sai yaga kamar kallon yafi kama da na reni ya na so ya fahimci abunda ta ke nufi ne, sai kuma ya ga ta kauda kanta ta na sharan kwallah.
Abba na zaune ya na d'an mirmishi Innani kuma sai ta hau kad'a kafa ta na Faman Tabe taben baki.
Abba ya juya ya na kallona da naji duk na kasa sakewa cikin muryansa yace"y'ata ya sunan ki?
Muryata na rawa nace"Ha. Hasiya."
Sai Abba ya jinjina kai kafin yace"Sannu Hasiya, ina iyayen ki suke ne?
Kai Tsaye nace"Babanmu ya rasu , sai mahaifiyata Amma ta na garinsu yanzu, sai yayyena guda Biyu da kanwata guda d'aya."
Abba sai jinjina kai ya ke yi alamun gamsuwa kafin yace"Har na tsawon wani Lokacin kika san Abubakar?
Assadiq na dago ina kallo sai naga ya Jinjinamin kai, shi ya bani karfin gwiwan yi masa bayanin Farkon had'uwata da Assadiq har zuwa auren mu."
Abba yaji tabbas yadda Magajin gida ya bashi Labari ne, cikin gansuwa yace"Dakyau, shima haka ya fad'amin"
Sai kuma ya yi shuru kowa ya zauna kawai ya na kallonsa mirmishi ya saki kafin yace"Na saka ma auran ku albarka, Allah ya sauke ki lafiya ina miki sannu da zuwa cikin Ahalina."
Kowa sai da ya Bude baki ya na kallon Abba.
Ni kuma shi na ke kallo idanuwana cike da kwallah nace"Ni?
Sai ya gyad'a min kai kafin yace"Daga yau kema kin zama d'aya daga cikin Ahalina, gobe in sha Allahu zamu je Zariya gidan Baffanki da ya Daura muku aure na samu tabbaci."
Sai kuma ya Juya ya na kallon Sadiq kafin yace"Ka kira abokin ka Tahir ya taho shima muje tare da shi."
Cikin girmamawa Sadiq yace"To Abba , Allah ya kara girma."
Kai Tsaye Abba ya kalli Sauran ya'yansa kafin yace"ga wata yar'uwa nan kun samu acikin ku, sai ku marabaceta cikin Ilimi kamar daman kun saba, ke kuma Sultana ki yi hakuri Bamu isa mu sauya wannan kaddaran ba, Magajin gida zai zauna da ku dukkan ku a matsayin matansa In sha Allahu."
Umma ta mike a fusace kafin tace"Abban Siyama wannan wani irin Hukunci ne?
Mama na gefe tace"Gaskiya fa, wannan ai ba mgana ba ce."
Suma sauran nata kuskus, Surayya dai batace komai ba Sajida ne ke ta yi ma Sadiya rad'a suna Gulma.
Sultana kuma kamar da kasa sai kwai ta fashe da kuka.
Jin haka yasa kafin ma Abba ya samu Zarafin mgana Innani ta mike kad'an ma ya rage bata fad'i ba Saboda masifa tace"Ishunki Salamatu ai Sulaimanu bai isa ba, samman wannan Hukunci da ka yanke bai yi ba."
Abba ya sauke Numfashi kafin yace"Innani wani Hukunci ki ke so na yanke bayan wannan?
Innani na Huci tace"Ka yi masa fata fata na cin amanarmu da ya yi mana, bayan haka a gabamu ka saka ya saki kilakin nan a yi mata Korar kare shine hukuncin adalci Sulaimanu."
Abba yace"Subhanallah Innani, Magajin gida aure ya yi ba zaman Haramci ba, kuma shi da Niyyar taimako ya yi wannan abun, mun zauna da shi ya yi min bayanin komai kuma ni na aminta da shi."
Umma da ke tsaye tace"Kai ya yi ma bayani ai bai yi mana ba ko?
Abba ya kalleta kafin yace"Hakane to ku koma ku zauna, kai Sadiq juya ka yi musu irin bayanin da ka yi min dazu"
Sadiq da gabadaya yaji gwiwarsa ta sare, ni ya ke kallo ganin na dukar da kaina ina ta kuka komai fa zai Faru bazai bari a Tozartamai mata ba.
Cikin gyara zama ya fara bayaninsa haduwarsa da Hasiya da auransu sai dai kamar yadda Abba ya Bukata ya Boye wasu abubuwan.
Ya karishe da fadin"Kuma ni har Allah acikin zuciyata Tausayi ne, sai daga baya na Fahimci ba'a Tausayi in ba so, ina son Siya sannan Kuma ina son zama da ita har karshen Rayuwata Umma don Allah Ki Fahimceni."
Umma cikin harzuka tace"In naki na Fahimceka fa? Nace in naki na Fahimceka fa? Sai aka yi ya ya?
Kansa na kasa yace"Ki yi hakuri Umma, na yi kuskure kuma na yi miki alkwarin in sha Allahu hakan bazai kara Faruwa ba."
Kai Tsaye Umma tace"Abubakar bazan karbi wannan auran naka ba, sannan kuma Wallahi Tallahi sai dai ka zab'a ko Auran da muka sani ko wanda ka yi ma kanka."
Da sauri ya dago ya na kallon Umma kafin yace"Umma."
Hannu ta daga masa kafin tace"Abunda nace shi na ke nufi, kuma anan wajen zaka zab'a, gwara Tun wuri nasan matsayin da ka ijiyeni."
Sai kuma kawai ta Fashe da kuka, Innani ta yi zaraf tace"Kwarai mganar Salamatu haka take, gwara dai mu san matsayin mu."
Abba zai yi mgana Innani ta daga sandarta ta na fadin"Ka na cewa Tak Sulaimanu kagani in ban kwad'a maka sandar nan ba."
Duk da ana cikin Rudani ne, ammh bai hana wasu darawa ba.
Abba sai ya koma kawai ya yi shuru ya na kallon ikon Allah.
Sadiq ya rasa yadda zai yi ya tashi yaje gaban Umma ya duka ya na fadin"Umma don Allah ki janye kalamanki, duka ina son mata na kuma ina son zama da su bazan iya zabar d'aya na bar d'aya ba."
Umma na sharan kwallah tace"Sai dai ka zab'a, tunda har ka iya nuna ko ni mahaifiyarka ba ni da ta cewa acikin Rayuwarka Abubakar"
Yadda ta Juya masa Fuska ne yasa yasan ta riga ta yi fushi.
Mama ya kallah tun kafin ya yi mgana tace"Sadiq gaskiya ne fa gwara dai ka sahale ma kanka, kafin ma ta san irin bakin fentin da ke tare da matar da ka aura."
Ido ya kura mata ya na kallonta Umma ko da Sauri ta Juyo ta na fadin"Wani irin bakin fenti ne Suwaiba? Don Allah ki fad'amin."
Mama ta Juya ta na kallon ya'yanta su Sa'ima su kuma suka gyad'a mata kai alamun ta fad'a.
Surayya kuma Tsoro ya kamata sai ta kalli Sajida ita kuma sai ta ware mata ido alamun ni bansan komai ba.
Mama ta gyara zama ta na fadin"kunsan dai salima na auran danginta, Alhaji jibril da ke kanin babanta da kansa ya ke fad'a ma Salima Matar da Sadiq ya aura Farar kafa gareta, duk wanda ta rab'u dashi ko asaran lafiya ko na dukiya ko na rai, Sannan da bakinsa ya fad'a yace tunda aka haifeta iyayenta ke ganin bala'i har sai da ta yi sanadiyar karayar arzikin Ubanta daga karshe tayi ajalinsa, sannan Mahaifiaryarta ta fara ciwom da aka kasa gane kansa, komai na su ya kare sannan kowa ma ya gujesu har su dangin Uban nasu, Sannan yace auranta Biyu na Farkon shima sai da komai nashi da na iyayen suka kare daga karshe ma zaman garin ne ya gagaresa, na Biyun kuma ranar Daurin aure ya samu had'ari ance har yanzu bai warke ba ya nakasa ga asaran dukiya, Wlh ance duk zuru'ar da ta shiga sai ta tarwatsasu sun rasa komai na su in ba'ayi asaran rai da lafiya ba fa an godema Allah."
Gabadaya Falon sai ya Dauki salatin su Umma, Innani kam kamewa ta yi a zaune Tsabar tashin Hankali.
Surayya kanta ta yi kasa da shi tasan komai ya lalace.
Sajida kuma ta mata alama da Hannun cewa ba ita ta fad'a ba, sai yanzu ta tuna da Hoton da ta Turama Salima shi ya lalata komai.
Kafin kace me salima ta karbi mganar ta na kara maida yarda akayi sai nanata take yi wai ance auranta ma Biyu duka ana sakinta Saboda bakin Jinin da ke tare da ita.
Shahida ta saka salati Kafin tace"Sadiq yanzu wannan Annoban da kowa ke gudu kai ka kwaso mana?
Sadiya kuma tabdijan kawai ta ke fad'i kafin tace"Wlh Umma Canfi gaskiya ne, mun shiga uku."
Abba kuma na zaune yana jinsu, yana maimaita sunan Alhaji Jibril shi sai yanzu yasan Komai da mafarin lamarin.