← Book details Tmw Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 83

Sashe 5

Tmw Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Assadiq ya kalleni cikin sanyin murya ya na fad'in"Nasan zaki ce meyasa bayan haka ban biyo bayan ki ba? Siya bani da mafita illah zabin na zauna a gusai tare da Sultana da ta tare a gidan da Abba yaa bani tun a daran, in na yi wani motsi abubuwa za su kwabe ni kuma bazan so haka ba, Shiyasa na zauna har na Tsawon Hutun da na Dauka na Sati daya daga wajen aiki, ammh na rantse da Allah ki sani ko wata dakika ba ta wuceni sai na Tuna ki Siya, wayarki ta na kashe, sannan karamar wayata ta bace a sha'anin nan na rasa duka Lambobin su Adda Ballatana na kira su naji Lafiyan ki, sai dai ina da yakinin guda daya da cewa kina lafiya, na tabbata da wani abu mara dad'i ya sameki da zan samu labari, da wannan Tunanin na samu kwanciyar Hankalin komawa wajen aikina sai dai tare da Nadama mai Dimbin yawa da kuma alkwarin zuwa na same ki na baki hakuri, sannan na gayamiki komai game dani, kuma ki tambaayeni abunda baki sani ba na amsa miki."
Shuru ya biyo bayan maganarsa kowa da abunda ya ke tunani, ni ina Tunanin wannan Satin dayan da ya yi tare da Sultana amarci suka sha? Kamar sai naji idanuwana sun ciko da kwallah, kishi Halitta ne ina son Assadiq, kuma nasan Sultana itace zab'insa da zabin Danginsa Dole zan ji ciwon abun in dai na tuna ko da Sunanta ne.
Shi ko Sadiq a cikin ransa ya ke wani Tunani, Hasiya itace matarsa ta farko, kuma ya aureta ba'a a matsayin budurwa ba, Sultana kuma Budurwace, Zai iya ba da shedar shi ya fara saninta a y'a mace, akwai wani sirri da dukkansu suke da shi, sannan kuma sirrin na su ya yi tasiri mai girma a tsakaninsa da su, ya bar ma ransa Muhimmanci da kowaccensu ta ke da shi a Rayuwarsa, ya na son Siya, kuma ya na son Sultana ba ya kinta, Shiyasa komai zai faru bazai Rabu da d'aya Saboda D'aya ba.
Kamar daga sama ya ji na jefo masa tambayar yanzu shi daga ina ya ke? Naga kuma wannan karon bai zo da mota ba?
Assadiq ba shi da wani zabi illah na Boye wata gaskiyar domin ya kara gina wata gaskiyar.
Sai kawai yace daga Abuja ya ke, alhalin Daga Gusau ya ke, tun ranar jumma'a ya isa da yammah, ya gaji da tuki ne sai kawai ya hau ta haya, tunda ya tafi sultana ke damunsa a waya da Shagwabar ta yi kewarsa ita dai ya dawo ta gansa, daman dakyar ta barshi ya tafi, ta na ta kukan wai bata warke ba zai tafi ya barta.

Duk da yasan ba wani Rauni ya yi mata Sosai ai shi ba karamin mutum ba ne yasan mace, ya bi da ita a Hankali sai dai yasan yan'uwansa ne suka sakata ta yi ta shaye shayen magungunar da ya sa ya makalemata a satin da suka yi armaci ba karya ta Gurzu a hannunsa shiyasa ya ke Tausayinta, kuma ya kasa kwabe shagwabarta a garesa, duk da yaso a wannan satin ya zo yaga Hasiya.
Ba shi da mafita sai ta fara zuwa Gusai yaje yaga Sultana, itama ba domin Hasiya na ransa ba zata iya Rinjayansa ya koma Abuja batare da yazo Zariya ba.
Haka suka rabu ta na kukan shagwaba, duk da ta na kusa da gida, kuma in baya nan Siyama ke zuwa ta na tayata kwana.

Ga shi ta koma makaranta so ba ta da wani kadaici tare da ita, kawai Sakalci ne da Shagwaba na yaran zamani.
Ba na son mganar Sultana Shiyasa na kauda maganarta a tsakanim mu cikin Sanyin murya nace"Tambayata itace me yasa tun farko ka yi mana karya baka da kowa sai kakar ka?
Mirmishi ya yi kafin yace"Bansani ba, nima kawai naji ina fad'a ma Amma hakane, sai dai daman duk wanda ya had'u da ni ba lalle ba ne kafin mu rabu ya san wani abu game dani ba, ina bambamta Rayuwata ta gida da kuma Rayuwata ta waje."
Dagowa na yi ina kallonsa kafin nace"Kowa na sonka a gidan ku, sannan naji ana kiranka da wani suna ko magajin gari ko?
Dariya ya yi kafin yace"Magajin gida ne Sunan Siya? Kina so kinsan waye mijin ki?
Sai na gyad'a masa, kai tsaye ya maida kaina saman kirjinsa ya kara gyaramin zama sannan ya shiga bani Labarinsa haihuwarsa karatunsa Asalinsa da komai da komai yawan yan'uwansa mata, gatan da ya ke da shi Soyayyar da Mahaifinsa da kakarsa su ke yi masa da Dalilin da yasa a ke kiransa Magajin gida, da kuma labarin wacece sultana? Alkwarin auran da ke tsakaninsu tun tana yarinyarta da alakarsu.
Ya karishe da fad'in"Ni a gida mu ba bu da'n gata irina, ni kad'ai ne namiji sauran yayyena duka mata ne, kanwata guda d'ayace Autarmu Siyama, Sai Sultana da ita daman alkwarin aure ne Tsakanina da ita, Ina daraja mata guda Biyu a Rayuwata mahaifiyata da kakata bani da kamarsu, Abba ba shi da wata Damuwa ya ma fi fifita Ra'ayina akan na shi Ra'ayin, Siya ina jin wani nauyin acikin zuciyata nauyin cin Amanar yardansu da na yi, na aure ki batare da sanin su ba."
Ya dakata lokaci d'aya ya na sauke Numfashi, ni kuma ina jikinsa nace"To me yasa ka aureni in dai baka sona?
Kuma me yasa ka aureni ba tare da sanin iyayenka ba?
Cikin Wani irin yanayi yace"Bansani ba Siya, abu daya na sani naji Tausayin Amma sosai, kuma naji Rauni ya shigeni da naji Labarinki, maganar gaskiya ba so ba ne yasa na aureki Tausayi ne, ammh daga baya sai na Fahimci shi So dabam ya na iya Farawa da Tausayi sai ya Rikide ya koma Soyayya  Allah ne shaidata Hasiya, Ina sonki kuma ina kaunarki kuma ina son na Dauwama tare da ke har Abada, in da ba na sonki a yadda na ke cikin Tsaka mai wuyar nan da Tuni na Rabu da ke., Maganar kuma meyasa na aureki ban sanar da Ahalina ba? Ina da dalilaina na Farko bani da Lokaci, na Biyu kuma in har na je musu da maganar ina da yakinin ba za su amince ba, ko da ma Abba ya Amince Umma da Innani ba za su amimce ba, sannan a lokacin na yi niyar na sakeki bayan na baki jari mai Tsoka, shikenan in na bar zariya na koma gida komai ya kare, ashe ba haka ba ne, Allah bai aura ma na juna Domin mu rabu ba, saboda ke na rika Dojema auran Sultana har na Tsawon shekara uku, saboda ke na fara masters a zariya sannan kuma ke ce Dalilina na karb'an aikin kamfanin da na yi Bautar kasa a zariya  Siya kin Sauya Rayuwata, Saboda ke na zama mai karya kuma na iyata, Saboda ke ma ke wata Boyayyiyar Rayuwar da na san Cin Amana ce ga Ahalina."

Ya na mgana ina jin zuciyata na kara narkewa cikin soyayyarsa, ina jin na gama yarda da shi, ko da baya so na to ina da matsayi mai girma acikin Rayuwarsa.
Abu daya na ke so na kara sani, shine me yasa ya kaini aka sakamin Implanta?  Tunda yace ya na sona meyasa ba ya son had'a zuru'a dani?
Kai Tsaye ya Dago ni muna kallon juna, sumbata ya ke shirin yi na yi saurin kauda kaina ina nuna masa bakina da ya fara cika da miyau.
Sai ya yi dariya ya mikamin ledan da har miyau ya fara taruwa ya taramin na Zuba, ina kallonsa ya ijiye ledan a gefensa ko kyamkyami ba shi da shi.
Cikin mamaki nace"Baka kyamkyamin Miyau Assadiq?
Cikin sauri yace"Ina da kyamkyami mana, Sai dai ke ce ban isa na yi kyamkyamin ki ba, abunda ke sakaki miyan ai ni ne na Digasa ko?
Zai sake rikoni na yi saurin kwace kaina ina fad'in"Ka bari na wanke bakina."
Ya na dagamin gir yace'To miye?
Ban kulasa ba na shige ciki da gudu sai da na sake yin brush sannan na dawo, kuma bai yarda ba sai da ya kama Fuskata muka sumbaci bakin juna na wani lokaci sannan ya kalleni ido cikin yace"Siya soyayyarki ce taja min duk abunda na zama yanzu, Wallahi kin ji Rantsuwan musulmi ban taba kyamatar komai da zai Fito daga Tsatson ki ba Hasiya, a lokacin bani da mafita ne, sai ta hakan dalilina shine ba na so ki samu ciki har ki haihu iyayena ba su san da ke ba, ba na so abunda zamu haifa ya zo ya Fuskanci laifin da ba shi ya aikata ba, Daman ina da niyar in komai ya Daidaita na gaya miki da kaina sannan na kai ki a cire miki, ammh har ga Allah har acikin zuciyata Siya bani da wata manufa ta sharri ko kin had'a zuru'a da ke daga bangarena."
Ya karishe fad'a ya na kallona nima shi na ke kallo ammh na kasa mgana.
Zuciyata daga chan gefen ta na gasgasta shi, wata kuma na Kokarin nuna min ba haka ba ne.
Ganin haka yasa ya kara rike Hannayena ya na fad'in"Ki yarda dani Hasiya wlh ba karya na ke fad'a miki ba, ki Fahimceni."
Sai na lumshe ido kafin na bude ina kallon yadda ya marairaicemin kamar wani maraya, lokaci daya kuma ya na shafa Tafin hannuna cikin wani irin Salon da ya sa, sai da tsikar jikina ya tashi.
Chapter 5 · 0% Book details