Sashe 25
Tmw Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Kai Tsaye yace"Eh tabbas baku san menene Qur'ani ba, Domin duk wanda yasan abunda Qur'ani ya kunsa bazai yi irin manganganun da kuke yi ba, tunda munsan cewa kashi na Farko na alqur'ani Tauhidi tare da Bauta kashi na Biyu kuma al'amaru wannahi Umarni da Hani, kashi na uku kuma yana mgana ne kan Alkillas Labaran Annabawa da Al'ummar da suka gabata."
Sai falon ya kara Daukan wani irin Shuru har da masu komawa ma su zauna, Abba na gefe ya na ta mirmishi hatta Innani da ke kuka sai da ta Dakata ta baza kunne tana Saurara.
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya Cigaba da fadin"In da ace kunsan haka da duk baku fad'i mangaganun da kike fad'a a kanta ba, saboda haka ku sani Wani abu bai isa ya samu bawa ba face Abunda Ubangiji ya kaddara masa ko ina tare da Siya ko ba na tare da ita Wani abu bai isa yasa na Gujema kaddaran da ke cikin Littafina ba. Sannan karya ne babu Canfi acikin Addinin mu, kuma kauce ma abunda Addnimmu bai zo da shi ba Farillah ne,hakan kad'ai ya isa ku gane cewa aurena da ita na cikin Littafin kaddarana."
Ya sake yin shuru kafin ya kalli Sajida ya na fadin"Ke kuma da kike ta nanata ita bazawara ce? Miye illar bazawaran ko ita ba Mutum bace? Kada ki manta Annabi Rahma Sallallahu alaihi wasallam, ya auri Nana Khadija Ta na da shekara arba'in kuma a matsayin bazawara Annabin Rahma kuma na da shekara ashirin da Biyar, in da ace Haramcine da Annabi bai yi ba, ta nan ma ya kamata kusan zawara na cikin Tarihin musulunci, ke awa kice zaki aibata bazawara? Kina da tabbacin zaki Mutu a gidan mijin naki ne! Kina da tabbacin watarana bazai iya sakin ki ba ? Ko kina Tunanin watarana bazaki iya zama bazawara ba?
Sajida ta zaro ido ta na kallon Sadiq cikin Subutar baki tace"Allah ya kyauta na zama bazawara."
Kai Tsaye yace"Itama ai ba ita ta maida kanta ba Allah ne, kuma kema ina kara Tusanar da ke cewa Kema Allah ne ya Halliceki kuma baki fi karfin kema Allah ya Jarabceki ba."
Sai Sajida ta kasa mgana Tunda tasan gaskiya ya fad'a.
Ni kaina na zauna na sunkuyar da kaina ina sauraran Assadiq ina sharan Hawaye acikin zuciyata na cika da alfaharin kasancewarsa Mijinta.
Hannayensa duka ya zura a cikin Aljihun wandonsa kafin ya cigaba da fadin"
Allah da kansa yace Annabi(SAW) man ikira'a suratul ilkasi, Suratul Iklasi salatalmanrat, Duk wanda ya karanta Qulhuwallahu har sau uku kamar ya karanta Qur'ani gabadaya ne.
_Qulhuwallahu Ahad Allah Ahad guda d'aya ne, Allahu Samad Allah mai sama lam yalud walam yuulad bai haifa kuma ba'a haifesa ba walam yakun lahu kufuwan Ahad_ shine abun bukata kuma cikin Biyan Bukata._
_Walam yakun lahu kufuwan ahad kuma k bashi da kishiya acikin Bautarsa, Shi Ubangiji shi kada'i ne in kun yarda da shi da imani da duka Sahabbansa da littafansa zaku Fahimci abunda na ke nufi_
Gaban Umma yaje ya duka kafin yace"Umma ki yi hakuri ki yafemin, sannan ki karbi Ziya ki sakama auren mu albarka na yi miki alkwarin zan rike miki sultana da Amana kuma zam zama mai adalci a gare su."
Umma dai kanta na kasa ta kasa mgana.
Sai kawai ya mike Surayya ya kallah kafin yace"Big sis ki tafi da Siya gidan ki don Allah.'
Harara ta makamai kafin tace"Ai da ya ke kai kazo da ita."
Mirmishi ya yi bai yi mgana ba Abba ne ya mike sai da ya yi gyaran murya kafin yace"Ina nan akan matsayata, Ku karbeta da zuciyarku daya d'a na kowa ne sannan cikin mu ba wanda yafi karfin kaddara."
Innani ta kallesa kafin tayi mgana Abba ya Duka gabanta ya na fadin"Ki yi Hakuri Innani ki saka ma magajin gida albarka, da ace ba aure ya yi ba akazo akace miki yana chan ya na lalacewa fa? Ko akawo miki yaro ace d'an gaba da Fatiha ne? Zaki so haka?
Innani sai ta saka kuka ta na fadin"in sha Allahu haka bazai faru b Allah na Tuba ai gwara auren, ni fa daman Gayyar Tsiya ce ban so ammh tunda ya yi mana nasiha ni na saki sai dai Sulsana nake ji kada Ubanta yaji yace Saboda ba yarka bace shiyasa kayi shuru ammh tuni na saduda yar nan ki yafemin"
Ta fad'a ta na jan majina, Abba ya mike ya na fadin"Kada ki damu kowa yaji yasan an yi abunda ya kamata, Abubakar muje a kawo mana abinci bangarena."
Daga haka Abba da Sadiq suka Fice Surayya kuma ta zo ta kama hannuna muka mike ta na ce ma su Saddiqa su riko Umma zuwa bangarenta.
Ni dai ina ta kuka muka fita Surayya na ta bani baki da lafiya komai fa ya wuce Abba ya saka albarka shi da Innani.
Cikin kuka nace"Umma fa?
Sai kawai tace"Itama zata sauko har ta saka musu albarka in sha Allahu"
Saboda tasan halin yan'uwanta sai ta kira Sadiq yazo ya bata makulin Shashensa ta kaini chan tace na yi sallah za'a kawo abinci.
Kuma da kanta tace min na saki jikina ina bangarem mijina ne'
Na shiga Tiolet din bedroom na yo alwala na zo na daidaici gabas na yi sallah.
Bayan na sallame na zauna na mike kafafuwana ina Tunani.
Wayata ma achan gidan Surayya na barta, ajiyar zuciya na ke ta saukewa a kai akai, ta wani bangaren nasamu salama ta wani bangaren kuma ina cikin Tsaka mai wuya.
*Janafty*
*TMWB3K008*
*TMW is a paid Novel, Pay 500 for regular or VIP N1K, Via 0552179550 Jamila Umar Gt bank, 09069067488*
https://chat.whatsapp.com/I7uxPXgtPKBHnVQjaEbRlE
*LAME NIG!*
*KASAITATTUN MATA MUN GAISHE KU*.
*AISHA LAME TA KAWO MUKU DUKKAN NAU'IN KAYAN KWALLIYA*.
*KUNSAN GWANAACE WAJEN BAWA FATA HAKKIN TA*
*KUN TUNA KYUAN FATAR GUDUYO KO?*
*KUN TUNA DAI YADDA BULKACHUWA KE SIYAWA YABI KAYAN KWALLIYA NA ORIFLAME KO?*
*TO KEMA GARZAYO KI ZABI NA KI, KO TA ZABA MIKI WANDA ZAI FI DACEWA DA FATARKI*.
*BA IYA KAYAN ORIFLAME BA KAD'AI.*
*TANA DA PRODUCTS DABAN DABAN MASU KYAU, MASU MASTAKAITAN FARASHI*.
*KU TUNTUBE JIKAR DADAR MARINA A WANNAN LAMBAR 07036662633*.
*ADO DA KAMSHI NE SIRRIN GAYU*
Anty Surayya da kanta ta kawo min abinci tare da ruwa da lemu, farar shinkafa da miyar Naman rago.
Kuma ta zauna tare da ni ta na lallashina har sai da naci abincin na sha ruwa ammh ina yi ina zubar hawaye saboda in na tuna kalaman Umma sai naji gabadaya na sare.
Ta gama fahimtar abunda ke sani kuka shiyasa kafin ta fita ta dafa kafad'ata ta na fad'in"Asiya ki daina wannan kukan in ba so kike wannan Masifaffan mijin naki ya zo yaga kina kuka ya taso min ba."
Idanuwana sun tara kwallah na kalleta ina Fad'in"Don Allah ki ba ma Umma hakuri kada ta rabani da Assadiq"
Tausayina ya kama Surayya ta saka Hannunta ta na sharemin hawaye kafin tace"In sha Allahu zan iya bakin kokarina."
Ko da bazata yi ba yadda ta nuna kula da Tausayina yasa na daina kuka sannan na tabbatar mata zan kwanta na Huta kafin mu tashi tafiya kamar yadda ta Bukata.