← Book details Tmw Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 83

Sashe 67

Tmw Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ni abunda ke bani mamaki gasa take yi dani, taga zoben zinare a hannuna ni kuma Kud'aden da na samu da haihuwan yan Biyu ne da kuma kudin da na ke tarawa a hannuna.
Karami ne ma na dubu 230k na siya Adda Rukayya ta bani shawaran na siya saboda kaddara kuma da na bar kudin duk sai na kashe su, sannan kuma ban siya ba sai da na Nemi izinin Assadiq yace yana da kyau hakan.
Nasan kuma ita tunaninta Wlh Assadiq ya siyamin shine zata saka Rigiman itama sai an siya mata.
Kai jama'a ni ban taba ganin kishi irin na Sultana ba.
Ka yi da kishiya kuma ka yi da miji Saboda sakarci.

Ni sai na rika Allah Allah ma na tafi katsina Biki duk sai gidan ya isheni, yarinyar nan tsirfarta ta yi yawa.
Sajida kuma ko suna bata zo ba taji Haushin mganar da Abba ya yi mata.
Sadiya dai tazo ta na ta harare harare da jefa manganganu.
Yara kuma sai dare na ke ganinsu suna wajen Umma ko mama, in Abba ya dawo gida suna tare da shi.
In kuma suka ga Babansu su manne masa tunda yanzu su san kowa.
An yi suna Talata, Jumma'a muka tafi katsina tare da Assadiq tun da bai koma ba.
A gidan Amarya Hauwa'u na sauka Tahir ma na garin shi yaje ya tarbemu, ni kaina naga tarba Hauwa'u kamar ta taba ganina.
Ko'ina sai ta nuna ni tace matar Abokin Tahir ne Sadiq.
Su Mama sun ce sai dai mu had'u a Daura har da su Anty Surayya duk za su je ma Hajja Biki Sanadin Tahir.
Abba ma yace zai zo daurin aure sannan 100k ya tura ma Tahir Gudummuwa.
Ranar asabar aka Daura Tahir da Amaryansa Hauwa kuma a ranar suka kwashemu zuwa Daura.
Ankon less ne ya yi das a jikina kamar an auna ni, gwamin ban sha'awa tunda ban wasa da kunin sabaya.
Saboda ni dai ina so na ganni da jiki ba na son ramar nan nawa.
Sai kananun halittun jikina su rika bayyana.
Mutane ma kallon mai ciki suke yi min, Har Anty Surayya sai da tace ko Ciki gareni nace tukunnah dai
Kuma ban saka tsarin iyali ba Tazara ne Allah ya bani, ina fatan sai su Asim sun shekara uku ko da zan samu wani cikin.
Tare muke da Matar Abokinsu Mb, Jb dai bai yi aure ba, bai gama iskancin na shi ba.
Motar Mijina na shiga zuwa Daura tunda suma su Mb kowannen da Motarsa sauran motocin kuma suka kwashi Amarya da Ahalinta.
Acan daura muka hade da Mama da Anty Surayya sai shahida da A gusau taje barkan Sultana daganan ta Biyo su Mama daga kuna nan zata koma katsina.
Hajja da yan'uwan Tahir sun yi ta godiya wannan karan sosai Umma ta ba da kudi da kayan abinci an kawo ma Hajja.
Kwana daya muka yi a Daura muka wuce Abuja ni da Assadiq da yara, wasu kayanmu ma na gusau yace na bari karshen wata in ya koma sai ya Taho mana da shi.
Sallama sai dai ta waya su Anty Surayya daman mun riga su tafiya, yace in ya tafi ya barni wahala ne kuma sai an saka wani ya maidani gida.
A daura muka bar Amarya Hauwa'u da Angon Tahir, sai fatan Allah ya ba au zaman lafiya.
Mun koma Abuja bamu san abunda ya faru a gusau ba.
Ashe a satin  da aka yi Bikin Tahir Mijin Sajida ya dankara mata saki har Biyu.
Rigima ta yi da Danginsa kaca kaca shi kuma ya saketa.
Sakin aure bai da dadi, kuma ba wanda ya kirani ya fad'amin Anty Surayya ce kuma kwana Biyu bamu yi mgana ba.
Siyama kuma bamu yi waya da ita ba.
Kuma Assadiq baya gayamin irin wad'anan abubuwan.
Nima sai da naji suna mgana da Anty Surayya.
Yana cewa"Allah ya kara mata, ba tun yau ba nasan abunda Sajida ta shuka watarana shi zata girba."
Sai da suka gama wayar ne na tambayesa abunsa ya faru.
Shine ya kalleni kai Tsaye yace"Sajida ce mijinta ya saketa saki biyu, Abba ya kirshi sun zauna mganganu ba dad'i ashe acan dangin nasa ma munafunci da Rigime rigime ta ke ta had'awa dara taci gida mahaifiyarsa tace ya saketa."
Cikin jimami nace"Innalillahi Abu bai yi dadi ba"
Mikewa ya yi lokaci d'aya yana fad'in"Ya yi dad'i mana, ai kad'an ta gani wanda yace daman tukunyar wani bazata tafasa ba ai tashi ko Dumi bazata yi ba."
Ni dai ban ce komai ba, har ga Allah jikina ya yi sanyi.
Saki ai ba shi da dad'i, ina ga shiyasa ba wanda ya kirani ya gayamin Labarin ba dadi.
Anty Surayya kuma ke kiranshi inaga kan mganar har cewa ta yi yaje Gusau yace ba inda za shi shi yana da abun yi.
Umma ina ji ta na kiranshi, kan mganar sai ya zille mata da mganar aiki daga karshe dai ba'a samu masalaha ba, mijin Sajida ya zuciya ya kuma ce har Abada duk da ya'yan da ke tsakaninsu.
Dole kanwar naki ta dawo gida ta fara Idda, ga ta  ga Sultanan sai su cigaba da munafuncin na su.
Su dasa daga inda suka Tsaya in ji Surayya.
Take gayamin da muka yi waya da ita, a bakinta naji ba'a daidaita ba, Sajida na gida.

*Janafty*
*TMWB3K018*

*TMW is a paid Novel, Pay 500 for regular or VIP N1K, Via 0552179550 Jamila Umar Gt bank, 09069067488*

https://chat.whatsapp.com/I7uxPXgtPKBHnVQjaEbRlE

*LAME NIG!*

*KASAITATTUN MATA MUN GAISHE KU*.
*AISHA LAME TA KAWO MUKU DUKKAN NAU'IN KAYAN KWALLIYA*.
*KUNSAN GWANAACE WAJEN BAWA FATA HAKKIN TA*
*KUN TUNA KYUAN FATAR GUDUYO KO?*
*KUN TUNA DAI YADDA BULKACHUWA KE SIYAWA YABI KAYAN KWALLIYA NA ORIFLAME KO?*
*TO KEMA GARZAYO KI ZABI NA KI, KO TA ZABA MIKI WANDA ZAI FI DACEWA DA FATARKI*.
*BA IYA KAYAN ORIFLAME BA KAD'AI.*
*TANA DA PRODUCTS DABAN DABAN MASU KYAU, MASU MASTAKAITAN FARASHI*.
*KU TUNTUBE JIKAR DADAR MARINA A WANNAN LAMBAR 07036662633*.
*ADO DA KAMSHI NE SIRRIN GAYU*

Daga Sajida har su Umma ba su tab'a Tunanin Sajida zata iya tsintar kanta a cikin zawarcin da ta samu kanta a ciki Dumu dumu ba.
Sajida ta gama sakankancewa da ta kama gida ta kuma fi karfin wani ya tugeta, ta na ganin Yusuf mai Hakuri ne sannan mai kawaici wanda baya maida kai kan wasu abubuwa kuma ta na ganin cewa ta Haihu ga ya'ya uku a tsakaninsu tana ganin babu wanda ya isa ya iya ja da ita.
Ta saki jiki ta na ta rashin mutumcin da ta saba daman tun tana gidan Sajida akwai munafunci sannan in dai ta zauna a wuri ba ta yad'a alheri, kuma bata sulhu sai dai ta kara Hura wuta.
Bayan ta yi aure ma bata daina ba, a makota ne a dangin mijinta ne duk inda ta shiga ta zauna bata yad'a alheri ba sai dai ta fad'i sharri ta Hura wutar wata fitanar.
Bata kuma shiri da wasu kannen mijin nata tun tuni shima mijin nata ya sha ja mata a kunni karya ne su had'u a taro Sajida ba ta watse taron nan da fad'a ba, ita kanta mahaifiyarsa bata son Sajida sabida tace ba mutuniyar kwarai ba ce.
Bata son zaman lafiya, Ta dad'e ta na yin abubuwa Yusuf din da kauda kai sai wannan na karshenta da wa'adin auran na su ya kare.

A gidan sunan matar kanin Yusuf din, Ta yi fad'a da kannensa har suna zaginta ita kuma tace sun san wacce suka zaga wannan Tsohuwar mai Dattin dankwali na gida.
Ai ko ba sanya suna zuwa gida suka gayama Mahaifiyarsu ga abunda ya faru har suna kari, nan ta ke ta kira Yusuf tace ya sauwake Sajida kila in ta d'andani zawarci zata yi hankali.
Shine dalilin da yasa ya saketa sannan Saboda a kara kuntata mata uwar tace duk ya kwaso mata yaran ya kawo mata hadda wanda ta yaye.
Zaman da Abba ya yi da shi sai ya Fahimci Sajida ta canchanci ta zauna a gida ta ga rayuwa kila ko zata yi Hankali shiyasa shima bai kara neman Yusuf ba.
Ballatana Assadiq da yace Allah ya kara gwara da ya saketa kila nan gaba zata Fahimci rayuwa ko Allah zai saka ta zauna lafiya da kowa.
Ita ko Sajida da farko ta dauka wasa ne, Ta na ganin Yusuf bazai iya Rabuwa da ita ba wasa ya ke yi, zai zo da kafarsa ya neme ta ya kuma bata Hakuri ya maidata gidansa.
Shiyasa ko da ta dawo gida da Abba ma ya kirashi Haushi ta rika ji a tunaninta za'a zubar mata da Ajinta, sai da taga har ta shafe wata d'aya a gida har jini daya ta yi ba Yusuf ba sakonsa sannan ba wayarsa.
Daman tun faruwan abun bata kirasa ba ta zauna ne sai ya nemeta da kansa sai ta fara ganin karshenta.
Umma ta damu da wannan Lamarin sannan nadama ya shigeta, In ta zaunar da Sajida ta na mata fad'a sai ta rika Tura baki tana fadin Yusuf zai zo da kafarsa har dakin Umma ya Duka ya bata hakuri.
Sai da ta ga lokaci ya fara tafiya bai zo ba, sannan bai kirata ko a waya ba.
Sannan ga shi ta fara gajiya da zaman gida kewar ya'yanta take ji sosai da gidanta inda ta ke yi duk abunda taga dama ba nan da ba ta da ikon yin wani abu ba.
Chapter 67 · 0% Book details