Sashe 53
Tmw Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Da safe kuma sai shirin Tafiya Daman na gama shirya akwatina da na yara.
Tare da Tsaraban da zan tafi da shi da ko Assadiq bai sani ba.
ya dai ganni da Ledoji har sai da ya yi mganar na Dauki a ledoji kamar wata bafullatana.
Ina Dariya nace"Ita ce baka yi b'atan kai ba."
Karfe goma saura muka bar gida na yi sallama da Maman suhailat da Ummi da ke gida daganan muka Biya gidan Adda Fati na karbi sako, ba ma mu shiga ba ita ce ta leko muka gaisa da ita har ta leko mota ta na yi ma su Asim wasa da suke kan jikina sai Faman ware ido suke yo suna gane gane.
Watansu fa Biyu ne da wani abu ammh har sun yi wayau, ga shi sun yi Kiba gwanin ban sha'awa.
Haka muka Dauki hanya muna tafe muna Hirarmu ta masoya gwanin ban sha'awa kuma kamar yara nan su san tafiya tsit sukayi daga karshe ma sai barci suka yi ta yi, sai gabda zamu isa sannan suka Farka.
Muna hanya Ramatu ta kirani nace mata mun kusa isa ma, sai ta yi mana Fatan sauka lafiya.
Kafin isarmu Umma ta kirani shima ta kirashi yafi sau uku tana tambayan muna ina? Muka ce muna hanya.
Tace to mu fara sauka ta gida tukunnah.
Alokacin har ya kalleni yana Fadin"Siya kinga abunda na ke fad'a miki ko? Watarana Umma zata kaunace fiye da tsamnanin ki."
Sai na yi mirmishi kafin nace"Hakane, daman ka sha fad'amin watarana komai zai zama Labari."
Mun isa Gusau Biyu da wani abu na rana Tunda Assadiq bai yi gudu ba Sosai.
Tarba da na samu a gidansu Assadiq ban taba Tunanin zan sameta ba, Umma da kanta ta fito ta tarbanmu, ta fara kwasan jikokinta bakinta har kunne, ni kuma Siyama da Farida na yi min barka da zuwa.
Shashen Umma na fara sauka ni da kaya, ta kaini dakin da Sultana ta zauna tace na yi sallah kafin a kawo abinci.
Su Asim kuma Tunda muka zo suka bar hannuna, suna hannun kakarsu sanda Su Siyama suka kawo min abinci naga asif a bayanta ta Goya tace min Asim na bayan Umma shima sai barci ya ke yi.
A raina nace Lalle yan Biyu kyautar Allah, Assadiq kuma ashe gida ya tafi sai da muka yi waya ya ke gayamin.
Har yana Tsokana da cewa"Gwara na bar ki da surukarki ku gaisa da kyau."
Ina gama cin abinci na fito falo na kara gaida Umma ta amsa cikij yar sakewa, har tana ce min me na ke bama su Asim sun yi wayau da girma haka?
Kaina na kasa nace mata madara ce kawai.
Ita kuma kai Tsaye tace"Kina da nono mai kyau ne."
Na dad'e zaune ita ta na Dauke da Asim sai faman jijjigaahi take yi da ya Fara kuka ni kuma ina zaune a kasa cikin Ladabi.
Ganin ya ki daina kuka yasa ta Saukoshi ta bani shi tace na bashi Nono, kunya ta saka na kasa bata a gabanta da ta Fahimci haka sai ta Shige ciki ta barni sai da na gama bashi ta fito.
Da kanta tace naje na gaida Mama da innani na kai musu yaran su gansu.
Kila ma naga su siyama shaahen mama ko na Innani Asif na Hannunsu.
Ban yi musu ba na mike, gani ta yi ina Kokarin ijiyesa saman kujera da Sauri tace"Ya zaki ijiyesa?
Cikin Ladabi nace"Zan dauko wani abu ne Umma."
Da sauri ta kariso ta karbesa ta na fad"in"Sai ki bani shi na rike miye amfani na?
Ni dai ina jin kunya na mika mata shi, ta karbeshi ni kuma na shiga ciki na dauko Tsarabata na ciro na Umma da na Mama sai na Innani, sauran kuma na Abba ne da su Siyama har da Sultana ma na yi mata tsaraba.
Ina fita falo da leda a hannuna na duka a gabam Umma na ijiye mata ina fadin"Umma tsaraba ce ba yawa."
Sai naga ta washe baki kafin tace"Ah harda wahala?
Masha Allah Allah yasa albaarka.*
Bata Bude ba sai da ta bani Asim na rike a hannuna sannan ta zauna ta Bude ledan.
Yaji ne da ya ji dakada Nama da Tarfanuwa gashi yaji maggi.
Sai Turaren Wuta na daki da Humra.
Umma ta washe baki ta dago ta na kallona kafin tace"Wa ya gaya miki duk abunda na ke so haka?ko magajin gida ne?
Mirmishi na yi mata batare da na yi mgana ba, Anty Surayya na kira na Tambayeta ta fadamim Umma na son Yaji sannan a bata Turaren kamshin Daki da Humra ta na Daraja wannan kyautar.
Kuma naga haka, Domin ta nuna min jin Dadinta Sosai ta na min godiya karon Farko da ta kalleni tace"Nagode Hasiya Allah ya yi albarka."
Na amsa da Ameen cikin jin dadi, Sai ta Bude yajin ta lasa ta fara Santi ta na kara min godiya.
Shigowar Farida yasa Umma tace ta rike ledojin mu tafi bangaren mama.
Farida na gaba ina baya rike da Asim zuwa bangaren Mama.
Na iske Anty Sakeena a bangaren Siyama ma ta na ciki Asif na Hannun Mama itama ta reno.
Tana ganina ta washe baki ta na fadin"Kaga fara mai Farar Aniya, ana zencen ki sai kuma a ganki."
Mirmishi kawai na yi, Sakeena ta tashi ta karbi Asim a hannuna..
Ni kuma sai na Duka kasa ina gaisheta ta amsa cikin kulawa.
Na juya na gaida Anty Sakeena itama ta amsa cikin Fara'a kafin tace"Yara nan fa girmansu ya bani mamaki kamar sun yi wata Hudu' wai sannu da kokari."
Mirmishi na yi ban yi mgana ba, na karbi leda guda daya hannun Farida na tura gaban Mama ta dauka ta na fad'in"Me kuma muka samu?
Sai taga Turaren rushi sai na Tsinke masu kamshi Tafiyayye d'an maiduguri wajen makociyar Adda Rukkaya na siye shi."
Mama ma nata godiya har Anty Sakeena sai da ta yabi Turaren nan tace Umma zata san mata.
Siyama na kallah ita da Farida kafin nace"Kuma tsaraban ku na nan sai kun zo amsa."
Sai suka fara Murna, na jima a bangaren Mama sannan Sakeena ta Rakani har Bangaren Innani.
Mun isketa kwance baiwar Allah ashe bata jin dadi zazzabi ta kwana dashi ta kuma hana Farida ta fad'a ma kowa .
Shuru shurun da ta yi mana ne yasa muka san bata da lafiya.
Sakeena ta aika Farida ta kira Umma tazo ta gani.
Sadiq ta kira ba jimawa sai gashi yazo Tunda Abba baya gida.
Innani bata son asibiti dakyar ta yarda Sadiq ya bata abinci a baki ya kuma bata maganin ciwon kai.
Yana ta ma Faridan fad'an ta daina Biye Innani da ta ga wani matsala tazo ta yi mgana.
Yarinyar ta bani Tausayi sai sharan kwallah ta ke yi, a bagaranta muka zauna da Sakeena ashe ta na da mgana muna ta Hira da ita.
Mune har mangariba,Allah Sarki Innani sai gashi taji Sauki har ta na Daukan su Asim.
Ita Nama na kawo mata soyayye Saboda Anty Surayya tace ta na so, aiko na sha addu'a da Godiya.
Anty Sakeena ta tafi gidanta ni kuma ina Tare da Innani a bangarenta tare da su Siyama.
Bayan isha'i sai ga Assadiq da Abba sun shigo Dubata anan muka had'u da Abba na duka ina gaishesa.
Assadiq kuma ya kwashi su Asim ya kai masa ya rikesu yana Dariya.
Mun gaisa dashi Cikin sakewa kamar yadda muka Saba.
Ya saki jiki muna ta Hita daga karshe har Umma da Mama nan shashen suka dawo suma.
Anan kuma suka ci abincin dare ni dai Saboda kunya ina cikin Dakin Innani ni da Farida.
A falo kuma Abba na ta yi ma su Umma Tsiyan sun ga fararen maza sun yi masa kishiya.
Mama taja Asif tace shine mijin Robanta Umma kuma ta rike Asim.
Innani na zaune tana dariya a ranta tana jin wani Farimciki ganin Sulaimanu cikin Annushuwa.
Sadiq ma ransa Fes sai mirmishi ya ke yi.