← Book details Tmw Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 83

Sashe 68

Tmw Part 3 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Sannan abun da ya bata mamaki yan'uwanta kowa sai yace laifinta ne, ita taja ma kanta saki kowa sai ganin laifinta ya ke yi, har Abba haka ya kirata ya yi mata kaca kaca ita kuma a ganinta bata aikata komai ba sai ma gani take yi da mutane ba sa son gsskiya ne.
Yanzu haka a daki d'aya suke kwana da Sultana tunda a bangaren Umma ba wani daki sai nata, ga shi cikin Dare Mai sunam Umma da suke kira da Ummi akwai kukan dare, Sultana juyawa ta ke yi ta sha barcinta ta barta da renon yarta.
In ta tasheta sai ta tashi ta na alamun barci barci in an samu ta bata Nono sai ta sakar mata yar ta koma ta kwanta tana fad'in kanta ciwo ya ke yi, sannan Umma da farko ta na shigowa ta taimaka mata itama in bata bangaren Abba to daga baya ma sai ta rika barin Sajidar da wahala ta bakinta tace tunda ta na kusa ta taya sultana jegon, kuma ma dai ai ta girmemeta a harkan ta rika nuna mata wasu abubuwan
Sajida ta na shuru da farko sai da taga Sultana ta maidata kamar Nany mai renon yarta, komai na ta ba tsari ba gyara ga son jiki da kazanta komai a watse sai dai in Sajidar ne zata gyara, in kuma ta yi mata mgana sai tace"Ni fa Anty Sajida na gaji ne, da me zan ji da kula da yarinyar ko da gyaran daki da kaya? Ai Umma tace tunda kin dawo gida kina zawarci ki rika tayani kina taimakamin mana."
Ranar Sajida ta sha mamaki kuma ba ta tab'a sanin haka kalmar zawarci ke da zafi ba sai da kanwar bayanta Kamar Sultana ta gasa mata mgana.
Abun ya yi mata ciwo kwarai ta samu Umma ta gayamata.
Umma ta yi wata dariya kai Tsaye ta kalli Sajida ta na fad'in"Ai ba karya ta yi ba, gaskiya ta fad'a tunda kin fito zawarci baki da wani amfani sai na Tayata kula da yarta, daman kuma bata da wata abokiyar shawaran da ta wuce ki ke da Sadiya, to tunda ita Sadiya na gidanta ke ce zaki zauna da ita kinga ma shikenan sai ku yi ta bama juna shawarwari ko?
Sajida bata gane mgana Umma ta gasa mata ba, sai da tace"To Umma ya dace ta wani ce na dawo gida ina zawarci?
Ni ai ba sa'anta ba ne, duk kokarin da na ke yi mata bata gani? Ni fa ban tab'a ganin sangantattaciyar kazamiyar mai jego irin ta ba wlh."
Umma dai yar dariya ta yi a ranta kafin tace tun yanzu?
Ai ta dauka da saura kafin zama yasa kowa yasan halin kowa.
Kuma sannan Sultana sai ta fara yi ma Sajida wani abu sai ana zaune sai ta kalleta cikin kamar mamaki ta na fad'in"Yanzu wai da gaske shikenan Anty Sajida kin zama bazawara?
Tambayar irin cikin izgili da Dariya da Renin hankali.
Sannan kuma ko a gaban waye ta kan fad'i haka ko a jikinta ita a dole da sunan wasa.
Tun Sajida na nuna bata jin haushi har ta fara nuna mata, sai tace ita a wasa ta ke mganarta.
Sannan wani karin abun haushin ma Har makaranta in Sultana zata shiga sai Umma tace su je tare da Sajida ta rike mata Ummi in sun shiga karatu.
Abun kuma da ya faru ba'a shiga da yara a ji, ita kuma Sultana tace a daukan mata mai reno.
Ko kuma Anty Sajida ta rika rakata makaranta ta na rike mata Ummi, ita kuma Umma ta amince tace tunda Sajidan na gidan bata komai idda ta ke yi, kuma tunda fitan ta zama ta lalura ta rika raka Sultana cikin makaranta.
Sajida bata kara jin ta raina kanta ba sai ranar da ta raka Sultana makaranta Lokacin har ta yi arba'in sai dai bata koma gidanta ba sai Assadiq ya dawo.
Yafi wata bai zo ba tun tafiyarsu ta bayan suna yana ta kawo uzurin aiki ne ya rikesa.
Tun safe suka zo, ita ta na waje rike da Ummi ta na fama da ita, ga sanyi Lokacin an fara iskar sanyi Sultana kuma ba su fito ba sai Wajen sha daya na safe sai gata ita da zugan kawayenta.
Suna zuwa suka ga Sajida rike da Ummi, cikin kawayen nata wata ta kalli Sajida ta na fad'in"Nanny ko da kika samu mai hankali daga gani zata kula da Ummi sosai."
Sultana ta kalli Sajida ta wani kyalkyace da Dariya kafin tace"Wata Nanny? Ba fa nanny ba ce Yayar mijina nace Anty Sajida da ya ke baki samu suwa suna ba ne shiyasa baki ganta ba, ammh ai su Maryam su santa."
Sajida ta na ji a gabanta Yarinyar tace"Au yi hakuri, na ganta a nan ne lafiya?
Sultana kai Tsaye tace"Zawarci ta ke yi mijinta ne ya saketa."
Ta fad'a ko a jikinta har ta na wani Dariya wani abu ya daki zuciyar Sajida.

Sai a lokacin ta kara jin girman nauyin sakin aure ga Rayuwar y'a mace, Shiyasa tundaga ranar ta fara kiran Yusuf domin ta samu ta lallashesa ko zai maida ta dakinsa.
Ammh ya ce mata umarnin mahaifiyarsa sai sanda tace ko zai iya maidata kuma ma shi ya gaji da hallayanta gwara su rabu gabadaya zai fi.
Hankalinta ya yi bala'in tashi tana ganin tun yanzu ta fara ganin Rayuwa kudi ma sun fara yanke mata, ta fara fuskantar rayuwar da bata santa ba.
Umma ba ta bata kudi Abba kuma bata isa ta tunkare ta ba, komai nata ya kare kayan kwalliya kati ma a waya na fara gagaranta gashi ba wata sana'a ta ke yi ba, da aurenta ta ke takama ba da komai ba.
Data ma yanzu ba ta dashi in kuma ta roki su Anty Surayya ta na ganin tasaukar da Ajinta Sadiya ta kan roka ta wurga mata 1gb daga baya itama sai tace ba kud'i a hannunta.
Chapter 68 · 0% Book details