← Book details Tmw Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 83

Sashe 26

Tmw Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ficewa ta yi ta dauke da Farantin abincin da ta kawomin, ni kuma sai na Rarrafa na hau kujera na kwanta sai naji na kasa sakewa sai na tashi ina jan kafa na shiga cikin Bedroom
Na sha kallo komai daman na Assadiq mai kyau ne da Tsari sannan duk da ya jima baya kwana a dakin akwai kamshin Turarensa sannan ga takalmansa nan da wasu kayan.
Gefen gado na samu na d'an kwanta ta gefen cikina na Dama, da gasken kuma na gaji wlh sannnan ga kaina ya fara nauyi, bansan barci ma ya kwasheni ba ina chan ina Tunane Tunane makomar Rayuwar aurena da Assadiq.
Cikin barci naji ni ajikin mutum sannan naji an zare min hijabin jikina, Hancina na kara Budewa ina shakam kamshin Turarensa, ina jin kamshin na ganesa, da Sauri na Bude idanuwa na sai ko fes acikin nasa ya na rankwafo ta kaina ya na kallona cikin Tattausan mirmishinsa.
Cikin muryan barci na kira sunansa"Assadiq."
Shima cikin wani sauti ya amsamin da cewa"Na'am Siya ta."
Kawai sai na yi Ririmi na taso na fad'a jikinsa na Rumgumesa sai kuma na saka masa kuka ina fad'in"Assadiq bazan iya rayuwa babu kai ba, don Allah kada ka rabu dani zan zauna dakai na yi maka biyayya na yi ma yan'uwanka Biyayya sannan ka gayama Umma ni zan yi ma Sultana Biyayya wani abu bazai tab'a had'amu da ita ba, in dai har ni zan zauna dakai na amimce na yi komai Saboda kai Assadiq."
Na karishe fad'a ina gunjin kuka shi kuma sai ya rumgumeni ta baya na. lokaci d'aya kuma ya na bubbuga bayana alamun lallashi.
Bai hanani kukan ba sai da na yi ya isheni sannan ya dago ni ya saka Hannayensa tattausa ya sharemin hawaye Lokaci d'aya ya na fadin"Shii. Nace ki daina wannan kukan ko? Ko so kike wani abu ya samu Bbyn mu?
Sai nayi shuru na koma na lafe a kirjinsa ina jan numfashi.
Rumgumeni ya yi kam lokaci d'aya ya na sauke ajiyar kafin ya fara fad'in"Nace ki kwantar da hankalin ki matukar ina raye ni nan zan tsaya miki siya, ba wacce cikin yan'uwana da zan bari ta tozartamin ke zaki yi musu ladabi a matsayin su na yayyena ammh kuma ni ma bazan bari su wuce iyakarsu ba Mganar Umma kuma kada ki damu zata sauko in sha Allahu."
Sai ya dakata kafin kuma ya gyara zamansa ya na dauke dani akan jikinsa sannan ya cigaba da fad'in"Sultana kuma ba ke ce zaki yi mata Biyayya ba itace zata baki girman ki, ko taki ko ta so ke ce na Fara aura kuma kina gaba da ita so a wajenta ya zama Dole ta girmamaki kamar yadda zata girmamani."
Ina jinsa ammh na kasa mgana a raina ina fadin ai itace ke da kai ni ai yar karo ce.
Fad'i ya ke yi"Zan kare ki da dukkan iyawata wajen ganin kin samu daraja acikin Ahalina fatana kawai ki yi hakuri ki gani, ki ki gani, ki ji kuma ki ki ji, kinsan gida in akwai mata da yawa sai a hankali balle ni kinga kanin mata ne sai a hankali ammh duk da haka zan yi kokarin na zame miki Garkuwa."
Dago kaina na yi ina kallonsa kafin nace"Ka tabbata bazaka rabu da ni ba.?
Na fad'a cikin Rauni, Shi kuma sai ya gyad'amin kai alamun hakane sai kawai na kara Rumgumesa ina fad'in"I love u."
Shima cikin wani irin Shauki ya rikeni sosai lokaci d'aya ya na fadin"Love u too, and i miss u Siyan kuka i need u sosai."
Ina jinsa ya fara shinshinar wuyana Tunda kuma ya Furta nasan abunda ya ke Bukata sai na dago kaina na kama wuyansa na rike, da kaina na Fara Sumbutar bakinsa.
Kamar ya na jira shima ya Rike kaina ya na taikamamin wajen ba ma bakunan mu hakkinsu
Mun shagala shagalar da ta saka muka manta da inda muke, Duk da nauyin cikina ban yarda na Juyama Assadiq baya ba, sai da komai ya wakana ina kwance a gefensa a tare muke maida numfashi.
Tudun cikina ya shafa jin kamar Motsi yana mirmisshi yace"Shi kanshi ya na murna da zuwan Daddynsa."
Mirmishi na yi ban yi mgana ba mun jima tare muna shakan numfashi juna kafin ya tashi shi ya fara shiga wanka ya Tsarkake jikinsa.
Sai da ya fito nima ya taikamanin na yi nawa na fito na maida kayana, ammh shi sai da sauya wasu Tunda wad'ancan sun gama yamutsewa.
Muna tare muna hira har wajen La'asar shine ma ya ke fad'amin zai fad'ama Abba gobe tare dani zasu wuce Zariya gwara na koma zan fi sakewa achan Tunda ga makaranta kada na yi wasa.
Ban yi masa musu ba ni kaina gwara na tafin ko na ba ma wasu zuciyoyin daman samun Salama saboda zuwana.

Kiran sallar la'asar yasa ya barni ya fita shima sai da ya taimakamin na yi alwala ya shimfid'amin Darduma ya zaunar dani yace tunda ya gajiyar dani na yi sallar a zaune sai nace masa kada ya damu zan iya.
Allah ya taimaka ina idar da salla sai ga Anty Surayya ta shigo Cikin Shirin Fita ta na ganina na zaune tace"Au kin ma yi sallar kenan? To taso mu tafi gida sai gobe, tunda Abba yace tare da ke za su wuce."
Ban mata musu ba na mike dakyar ina gyara Hijabina, da muka Fito Haraban gidan sai naga ta Nufi motar ta Cikin sanyi na nace"Bazamu shiga na yi ma Umma sallama ba ne?.
Kai Tsaye tace"Muje gobe in zaku tafi kya shiga ki yi mata."
Ban yi musu ba ta bude min gidan gaba na zauna sai dai ina ta waigen ganin Assadiq.
Itace ta Lura da haka kai Tsaye tace min"Sadiq ya na bangaren Abba suna mgana, kina son ganinsa ne?
Da sauri na girgiza mata kai ina kokarin kauda kaina Saboda kunya.
Mirmishi ta yi kafin tace"Zai zo anjuma ina da tabbacin haka Tunda Siya na tare dani ta bakinsa"
Tare muka yi dariya ni da ita , sai dai kuma Tundaganan har muka isa gida bata kara mgana ba.
Abunda na Lura kamar ranta ya na bace ne shiyasa yara ma na mata Oyoyo mommy bata tsaya ta kansu ba, Tunda ta rakani daki tace na kwanta na kara Hutawa ta fice ta koma Dakinta.

Ran surayya ya gama baci da sauran yan'uwanta marasa fahimta musamman Sadiya da Sajida da Subai, Saddiqa ce bata zafafa ba har Sa'adatu ta bata mamaki yadda taga ta Dauki zafin kan al'amarin..
Kuma illar shine daukan zafin su To kara Harzukan Umma suke ta so ne su taru su ba ma Umma baki ta karbi wannan kaddaran ammh su sun ki gane haka sai kara Zuga Umma su ke yi suna fad'in kada ta yarda Sadiq sai ya zab'a ko Sultana ko Mayyar matarsa.
Kuma abun haushin harda karamar yarinya suka zauna suna ta zugata, ita sai ta koma kawai ta yi shuru Saboda sun ce ta na Goyon bayan Sadiq ne.
Shiyasa da ta bi Umma har Daki zata ba ta shawara da mgana.
Ta koreta tace ta fita ta bata waje har ta na cewa Daman tasan bakinsu d'aya da Sadiq abunda ya sa har ta yi kwallah shine sauran yan'uwan nata har suna zargin daman tasan Sadiq ya yi auren Tuntuni taki fad'a.
Shine ya sakata kuka ta na Rantsuwa ta na bata san komai ba Saddiqa na tayata gayamusu in da taga Hoton Sadiq da matarsa.
Kuma har Umma ta aminta da mganarsu Shiyasa ta zo ta ja Hasiya suka yi tafiyarsu.
Kuma ita abunda yasa tace abi komai a sannu shine ta riga ta gama Fahimtar Matukar aka matsa to Sadiq zai zabi Hasiya ne ya bar Sultana domin alamominsa sun nuna haka, kuma wlh zai yi iya fad'a da kowa akan Hasiya to in suka zo suna zuga Sultana taje ta yi masa rashin kunya fa? Yadda Sadiq ya tsani Reni ai sai a samu matsala Shiyasa ta so abi komai a sannu a Hankali kowa sai ya samu abunda ya ke so.

Ni bata gayamin ba ammh rashin walwalwarta ya bayyana har saman Fuskarta, tunda muka dawo ba ta da walwala ta ma shige ciki ba ta fito ba.
Nima kuma ina inda na sauka na iske kiran waya Rututu har da na Amma ga na Ramatu sai na Adda Fati.
Adda Fati kawai na kira, nasan itama ta na cikin Fargaban kawai sai nace mata ta bari na dawo gobe in sha Allahu.
Amma na kira gabana na fad'i na Dauka ko sun yi wata mganar ne da Adda sai naji kawsi mun gaisa ta na tambayan lafiya da kuma lafiyar Assadiq nace mata dukkan mu muna cikin koshin lafiya.
Shine ma ta ke fad'amin Adda bata ji dadi ba hawan jini ya taso mata kwanaki biyu kenan, sai nace ta bani ita na gaisheta.
Adda da karfin hali ta tambayeni Cikina watansa nawa? Nace bakwai da wani abu sai tace In Hamma Isuhu zai Shigo Zariya zata bashi wasu saiwowin itattace na Dafa na rika sha mganin zaki ne, ni dai sai na bita da Toh kawai.
Bayan Amma Ramatu na kira muka gaisa itama mun kwana Bamu yi waya ba tambayata tayi ina gida gobe sai nace mata a'a sai dai jibi, nan take gayamin Jibi zata shigo da haka muka yi sallama.
Da daddare Khalil ya kawo min abinci Tuwon Semo miyar Kubewa d'anya, kuma naji dadi Sosai naci da yawa Sannan ga Zobo mai sanyi ga dad'i.
Chapter 26 · 0% Book details