← Book details Tmw Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 83

Sashe 52

Tmw Part 3 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Daran yau dai su Asim ba su yi ma Babansu kara ba kwana suka yi kuka, bamu yi barci ba daga karshe ni yace naje na kwanta ganin akwai barci a idona.
Yace naje na kwanta tunda ina jin barci shi zai kula da su, Allah Sarki bawan Allah duk farkawan da zan yi yana Rike da su duka yana Faman jijjiga in ya gaji ya koma ya zauna a gefen gado ya kwantar da su, ya Fara Daukansu d'aya bayan d'aya yana basu Madaran su.
Ni uwace kukansu yasa na kasa natsuwa na yi barci dole na mike na isa garesa na mika Hannu ina Fadim"Assadiq kawo su, kaje ka kwanta ka yi tafiya akwai gajiya a jikin ka"
Kallona ya yi cikin so da kauna kafin yace"ni nace kije ki kwanta Siya zan kula da su kinga ai sun fara rage kukan na su ko?
Cikin wani yanayi nace"Haka muke fama da su, ammh na yau yafi na kullum wlh, kawo su kaje ka kwanta Tunda gobe muna da tafiya a gabanmu."
Kin bani su yayi, yace sai dai na basu Nono na koma na kwanta.
Haka na zauna yana rike da Asim na fara ba ma Asif Nono sannan na karbi Asim na bashi shima.
Gaahi sun koshi sun kuma daina kuka ammh yaran nan sun ki yin barci idanuwansu kyar suna kallon kowa.
Cikin Tausayinsa na kallesa Wlh akwai gajiya tare da shi, tare da barci ammh yaki zuwa ya kwanta.
Cikin taushin murya nace"Kaga fa kana jin barci kawo su don Allah."
Cikin Kaushinsa yace"Nace ki barsu ko? Ni da ba na zama ke fa kadai kike wahala da su yanzu na dawo ki bari nima na tayaki mana Siya."
Yadda ya yi maganar ne yasa wani kaunarsa ya kara kamani naji wani Shauki na Dibana.
Kawai sai na saka kaina saman kafad'arsa ina fad'in"Ina sonka Assadiq, na tabbata cikin maza Dubu sai an tona an kara Tonawa kafin a samu kamarka, Allah na gode maka Sannan yau na kara godema Amma da ta yi min kyakyawan zabi a Rayuwata.".
Yana yar dariya yace"Ba kin ce baki so ba? Alokacin har rashin kunya kika so ki yi ma Amma wai baki sona?
Dariya na saka ina fadin"Ba rashin so ba ne, kawai ina Duba manganun da ke kaina ne. Ina sonka Tun a Lokacin ka Fahimci mganata ba na son wani mummunan abu ya sameka ne ta Sanadina."
Mirmishi ya yi mai Tsada kafin yace"ba abunda ya isa ya sameni face abunda Ubangiji ya kaddaromin acikin kaddarata."
Kwanciyar da yaso na yi ban yi ba, hira na zauna muka yi ta yi, yaran nan kuma sai gabda asuba suka yi barci.

Shiyasa sai bayan ya Dawo masallaci ne muka kad'aice da juna ta inda na kara sara ma magungunar gyara na marubuciya Surayya dee shine yadda Assadiq ya ke min rawan kafa da na Jiki in muka had'u da juna.
Daganan na Bata Makin dari bisa dari kan duka mgangunanta na Sanyi da na gyara ga Gimbiyar kaza, tare da Tabntabaru Shiyasa ni yanzu ba na siyan kowani kayan gyara sai ta hannunta, kayanta masu inganci ne sosai +234 803 277 3332.
Chapter 52 · 0% Book details