← Book details Tmw Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 83

Sashe 11

Tmw Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau Alhamis muna da karatu a makaranta, ammh saboda yadda na tashi cikin nauyin jiki yasa na yanke shawaran bazan fita ko'ina ba.
Kafafuna ne na lura yau sun kara tasawa, sannan kamar cikin jikina ya sauka a saman kafafuna haka na rika ji, Dakyar na iya tashi na yi shara da goge goge saboda wajen kwana hud'u ban iya taba komai acikin dakin ba.
Assadiq ya kirani Tun asuba shi ya ma tasheni sallar asuba, kuma bayan na idar ya sake kirana mun yi mgana, sai da ya tabbatar da lafiyata kalau sannan yace na koma na kwanta na Huta.

Ban yarda na fad'a masa yanayin da na ke ji ba, yanzu sai ya d'aga Hankalinsa ya kasa natsuwa, kuma naga lalurorin ma su cikine, shiyasa ban gaya masa ba dama ya tambayeni zan shiga makaranta ne sai na amsa masa da Eh! Har kuma yace zai Turomin kud'i ya na tunani na hannuna sun yi kasa.
Ko da na gama gyaran dakin nan, sai da koma na zauna ina ta faman Numfarfashi na tsawon wani Lokaci sannan na tashi na shiga kitchen na Dumama ragowan Tuwon da Maman Suhailat ta zubomin jiya.
Tuwon masara miyer karkashi, rabi na ci jiya na rage na safe, ga uban wanke wanke jibge  na fara tunanin ko na kira Adda Fati ne Habiba tazo? Domin har ga Allah zan sha wahala in nace zan tsaya na yi wannan wanke wanke.
Sai da na gama cin Tuwon sannan na fara Tunanin wanke kwanukan, abun dai sai a hankali ina yi ina faman Hutawa, kafin na gama baya na ya kage, kafafuwa sun kara nauyi, ko gyara kitchen din ban yi ba, na koma cikin Daki na kwanta da na huta sosai har sai da naji ina jin barci barci.

Sai dai ban kwanta ba, ta shi na yi na sake ruwan zafin da na saka a kittle, na shiga wanka na gasa jikina, da na Fito sai na Shafa mai, saboda kaya na duk sun matseni na dai na saka su, iyakata Dogayen Riguna da T.Shirt da riga da zani.
Kuma duka sun yi datti, na had'a zan kira Habiba ta zo ta je gidan Adda Fati da shi ta wankemin, Tunda ni dai yanzu ina gabda daina Daukan Laluran kaina.
Sai na Bude bangaren da Kayan Assadiq suke cikin Wadrope d'ina na Dauko wata farar T.Shirt dinsa na saka na dauka ma zata yi min yawa Tunda ta na da fad'i ammh sai naga ta shigeni gabadaya, sai na had'a ta da wani zanin Atamfata na saka Hula.
Wayata na dauka na yi masa Hoton kaina da Rigar ina Dariya a raina nace in yazo zan nuna masa rigarsa har ta faramin kad'an.
Game na fara yi a waya ta, daganan bansan Lokacin da barci ya kwasheni ba, sai da naji kamar daga sama ana ta Bugamin kofa, na mike da sauri wajen saukowa daga kan gado har sai da naji kafafuwana sun sage, kuguna ya amsa sai da na tsaya na yi salati na d'an sarara sannan na fita zuwa falo ina kokarin gyara hulan kaina.
Har na isa kofar dakin knooking a ke yi cikin Sanyin murya nace"A na zuwa."
In da ace nasan abunda zan gani in na Bude kofar nan, na tabbata ko da kud'i aka had'ani bazan taba Budewa ba.
Gwara rashin Budewan akan Bud'ewan, ina jin d'an cikina na Motsi lokaci bayan Lokaci ammh yau da na ga Yan'uwan Assadiq Tsaye a gaban kofar dakina sai da naji kamar abunda ke cikina yafi d'aya, Saboda yadda cikina ya murd'a naji ta ko'ina ana juyi tare da irin naushi kamar dai akwai abunda yafi d'aya acikin cikina.
Tsabar kad'uwa yasa sai naji kamar an kafeni a wajen, bakina na rawa tare da kiftawam idanuwana, zuciyata kuma ta na barazanan fitowa waje saboda Tsabar tsoro da Firgici.

Yadda na ke kallonsu ido waje haka suma suke kallona, na gane su bayan ganinsu a hoto dukkansu na gansu a bikin Sultana da Assadiq har mun gaisa.
Ina rike da Kofar Rud'ewa yasa na ma kasa saki, Sajida ce ta kalleni kamar Idanuwanta zasu fado kasa saboda takaici Cikin gatsali tace"Ke ce Hasiya?
Sai kawai na samu kaina da gyad'a mata kai ina jin marata ta Daurewa kamar ace haihuwa zan yi, Sajida zata kara mgana Surayya ta kalleta kafin ta girgiza mata kai alamun tayi shuru, kaina ta dawo da kallo kafin tace"Zamu iya shiga ciki?
Ta fad'a kai Tsaye ta na kallona, sai a lokacin na lura da yadda na tare kofar, cikin daga kafa na matsa baya ina fad'in"Eh eh! Ku shishigo sannun ku da zuwa"
Bakina tare da bugun zuciyata su ke tafiya, Surayya ce kan gaba Sajida na bayanta Dauke da yarinyarta a saman kafad'anta.
Tsabar Rudewa na kasa bin bayansu, Sai da na tsaya dafe da kuguna acikin raina ina maimaita"Innalillahi wa"inna ilaihirraju'un shikenan abunda na ke ta gudu ya zo ya faru, ai shikenan"
In da ina da yadda zan yi bazan bi su ciki ba, fita zan yi na nemi mafaka ammh kuma bani da wata mafita, sai dai a chan kasan raina ina Tunanin ko dai Saliha ce ta aiko su? Sai naji kamar mganar ba ta zauna a raina da hakan zai faru ba.

Da jan kafa na kariso falon na iske su har sun yi ma kansu matsugguni a daya daga cikin kujerun falon.
Surayya wayarta ta ke dannawa ta yi shigar alfarma sannan Fuskarta bata bayyana abunda zuciyarta ke ciki ba  Sajida ko sai faman kalle kalle ta ke yi cikin Raini da wulakanci.
Kamar wacce wani abu ke cizo a kafa haka na kasa tsayuwa a gabansa sai na juya da sauri na shiga kitchen jikina na rawa, na dauko musu Ruwan Gora guda biyu kofi na saka cikin wani Farantin silba.
Na Kwaso ina rawan kafa da na zuciya na kawo gabansu na sauke sannan na Durkushe ina jin kamar ina cikin wani abu mai zafi saboda yadda Tsoro da firgici suka saka naji kamar ina cikin zazzabi mai zafi.
Surayya ta kalleni yadda na zauna duk a takure sai tace"Ayya kinga ta shi ki koma saman kujera"
Kaina na kasa ammh na kasa mgana a raina ina fadin ko dai ko dai?
Saboda ban ga alamun sun san wani abu ba.
Kamar daga sama naji Tace"Hasiya ko?
Sai na dago da sauri ina kallonta kafin nace"Eh eh ni ce."
Kai Tsaye tace"Nasan kila kin gane mu, in ma baki gane mu ba mu yan'uwan Saliha ce, mun had'u da ke da kika zo mana Biki a gusau."
Cikin yaken karfin Hali nace"Eh an yi haka sannun ku da zuwa."
Surayya ce kad'ai ta amsa kafin ta kalleni na wani lokaci.
Sajida ta kalleta ta na fadin"Big sis mu yi abunda ya kawomu, na kosa mu bar nan.".

Surayya bata ce komai ba, sai dai ta mike ta zo ta zauna kusa dani, jikina na rawa naji na sake zaman Dirshan a kasan Tayels, Kallona ta ke yi ni kuma na kasa kallonta kallo d'aya zaka yi min kasan bani da gaskiya.
Cikin Kakkausan murya Surayya tace"Hasiya tambayarki na zo yi takanas daga Gusau zuwa garin da ban taba zuwa ba, kuma ina so komai na Tambayeki ki fad'amin gaskiya, in kuma kika yi min karya nan gaba zai zame miki matsala, ita kuma gaskiyarki in kika tsaidata Allah shi ne zai nuna miki aikin gaskiya, ina fatan zaki fad'amin gaskiyan Abunda kika sani"
Ina salati a cikin raina, a fili kuma sai na gyad'a mata kai zuciyata na rawa nace"In sha Allahu zan fad'a miki iya gaskiya abunda na sani."
Sai ta gyad'a kai kafin naga ta Dauko wayarta ta Danna ta saukemin wayar a saman Fuskata, lokacin da na yi arba da Hotona ni da Assadiq sai da naji na fara fitsarin da na matse, cikin gwalalo ido na kalli Hoton sannan na koma ina kallonta tare da mamakin ina suka samu wannan Hoton?.
Ko Assadiq ne ya nuna musu?
In kuma ba shi ba ne, na tabbata yau karya ta kare, sannan kuma muna cikin Tsaka mai wuya.

Surayya sai da ta gama ganin yanayin Firgicina sannan tace"Waye wannan a tare da ke? Wace alaqa ne a tsakanin ku? Mun ga Hoton a Duniya, mu kuma bamu san ke wacece ba, gudun yanke Tunanin da ba shi ne ba, sai na yi Tunanin na Bincika komai kafin mgana ta kai wajen manya."
Ta dakata ta na Sauke Numfashi ganin har na fara sharan hawaye.
Cikin kasa da Murya tace"Ni sunana Surayya kuma ni ce babba a gidanmu, ina daukan girman da Allah ya bani da Muhimmanci, Hasiya ki gayamin iya gaskiyan ki meke tsakanin ki da kaninmu Sadiq? Domin hankalina ya tashi da naga wannan Hoton ina Fatan kada tunanin da na ke yi ya zama gaskiya."
Bani da mafita sai na Fad'in gaskiyata, kuma na tabbata in ma na yi karya sai sun gane, tunda ga shi sun samu kyakyawan Hujja a garemu.
Kaina na kasa ina sharan kwallah zuciyata Tuni naji ta tsinke, na amince zan fad'i gaskiyata ammh kuma zan rokesu Kada su rabani da Assadiq a Lokacin da zuciyata bazata iya Daukan Rabuwa da shi ba.
Sajida cikin dakamim Tsawa tace"da ke fa ake mgana, malama kina bata mana Lokaci."
Kawai sai na fashe musu da kuka, Surayya ta daga ma Sajida Hannu cikin bacin rai tace"Sajida kada ki kara mgana na gaya miki."
Sai ta maida kallonta kaina cikin sigar lallashi tace"yi hakuri Hasiya,ki gayamin a ina kika san Sadiq?
Kaina na kasa nace"Na san shi, Mi. MIJINA ne shi."
Sajida ta Dafe kirji kafin tace"Mun shiga Uku miji kuma?.
Chapter 11 · 0% Book details