← Book details Tmw Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 83

Sashe 54

Tmw Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A daran Surayya ta zo min Sannu da zuwa, Abba ne ya yi ta fad'an me yasa ta fito bata bari sai da Safe ba.
Shiyasa bata dade ba ta tafi gida, ni kuma Assadiq yace na shirya mu karisa can gidan, Kafin mu tafi na bama su Siyama Tsarabansu na mayafai sai kayan kwalliya.
Abba kuma Turare mai kamshi na kawo masa ya yi ta saka min albarka.
Su Umma sukaji kamar kada su barni na tafi da su Asim suna ta cewa Gobe da Safe suna jiran magidanta nasu.
Sai goma na Dare muka isa gidan Assadiq.
Gidan ya yi min kyau, madaidaici da Shi da zamu shiga megadi na gaisheshi ya amsa yana gayamasa ni ce uwargidansa ga ya'yansa nan.
Megadin bahaushe ne ya yi ta saka ma su Asim albarka.
Bansan cewa Sultana bata so saukata a gidanta ba sai da muka iso muka iske ta Rufe kofar falo.
Sai dai ta manta yana da key din gidan tare da keys din motarsa ya ke a had'e da shi ya yi amfani ya Bud'e mana muka shiga.
Yadda na gane matar gidan bata maraba dani, shine har wutan dakunan takashe ko'ina Duhu sai da ya kunna Haske ya gauraye.
Nice na ke ta bin ko'ina da kallo shi kam yana rike da Asif shi ya shigar min da akwatinana dakin da ke yamma da falon.
Shima a kulle ne sai da ya saka makulli ya Bud'e.
Bakomai a dakin sai gado sai wardrope akwai kuma Tiolet aciki sai Cafet sai dai gadon karami ne ba babba ba.
Kamar yadda na lura gidan Bedroom guda uku ne, biyu suna waje daya Daga yana bangarensa na Dabam.
Yadda bai ce min komai ba nima ban ce masa komai kan Sultanar ba.
Shi ya taimakamin na yi musu shirin kwanciya.
Da yake da yamma Mama ta sake yi musu wamka tun a gidan ma suka Fara barci, nima sai yace na yi shirin kwanciya ya duka ya sumbaci kuncin su Asim sannan nima ya duka ya Sumbace.
Lokaci daya yana fadin"Sai da Safe Matar Assadiq.'
Nima ina mirmishi nace"Sai da Safe Mijinsiya."
Yana mirmishi yace na Rufe kofa kuma sannan na yi addu'a kafin Fitarsa har A.c da fanka sai da ya Tabhatar da ya kashe min.
Ni kuma sai na Shiga Tiolet na kama Ruwa na zo na yi shirin kwanciya bayan na yi addu'a na Tofe jikina da na ya'yana na Rumgumesu bayan na Rufe kofar da key ta ciki..ban ksshe wuta ba Saboda su Asim na motsawa suka ga Duhu za su fara rigima.
Barci na sha sosai sai Asuba na Farko ko da Assadiq yazo yana bugamin kofa a lokacin ina sallah ne.
Bayan na idar na tashi naje na Bude kofar na dawo, yaran nan sun yi barcin Dare ammh da Asuba nan suka fara kuka duk suka rikani.
Asssadiq kuma bai Dawo daga masallaci ba, kukansu har haraban gidan nan Ammh Sultana bata Fito ba.
Shine ya dawo masallaci yaji kukansu ya Shigo da gudu dakin yana Tambayar Ba'asi.
Cikin gajiya nace"Bansani ba, kawai a tare suka farka suka fara kuka."
Allah Sarki Assadiq haka ya Rikenin Asim da Asif a tare yace na had'a musu madaransu.
Ba ruwan zafi shi ya ce na fito muje kitchen ya nuna min komai yace na Dafa Ruwan zafi.
Haka ko akayi ya jirani na Dafa ruwan Dumi na Dama musu kowannen na cika masa Fidansa, falo muka Fito ni da shi Saboda yadda suka Rikitamu da kukansu shi yana ba wa Asim ni kuma ina rike da Asif ina bashi.
Bamu san Fitowarta ba sai ganinta muka yi a saman kan mu.
Kere kere tana kallon mu, ko Darajan yana mijinta bata gaishe shi ba sai nice na gaisheta ta yi kamar bata ji ba ta wuce ta shiga kitchen ta na sakin karamin Tsaki.
Kallona ya yi rai bace kafin yace"Kada ki kara zubar da  girman ki, ki gaisheta in bazata gaisheki ba ta bar shi."
Cikin nuna komai ba komai ba nace"Haba bakomai ai ni nazo gidanta."
Bai kara mgana ba ammh Daga gani ranta ya baci, muna zaune ta fito ta koma dakinta d'auke da Mug a Hannunta.
Allah ya taimakemu suna sha suka daina kuka daman rigima ce da Yunwa kuma.
Ban dauka Haka Sultana ta yi nisa da Tsanata ba sai Ranar, ko Abun kari bata yi mana ba ballatana Ruwan zafin da zan yi ma yara wanka Tunda Tanki ya lalace ruwa baya zuwa ta makewayi.
Bansani ba ko yaje ya yi mata mgana ne, naji tashin muryansa ya na yi mata mgana ammh ni ban ji nata muryan ba.
Sai da ya shigo ne na gansa ransa a b'ace yace ko zan shirya ya kaini gida ne can sai na karya nayi wanka suma yaran su yi?
Ni kuma sai nace haba ni zan iya yin komai indai yabani izini.
Shi ya rikemin yaran na shiga kitchen na Dafamana Ruwan Tea da Soyayyen kwai da Buredi da shi muka karya sannan na saka Ruwan zafi na yi ma yaran wanka yana tayani.
Bayan na shiryasu ya rikeminsu nima na yi wankan na shirya shima kuma sai yaje ya yi wankan ya shirya cikin manyan kaya tunda yanzu naga ya rage saka kananun kaya.
Har muka bar gidan nan Sultana bata fito ba, yana ijiye ni bai ko shiga gidan ba ya juya yace akwai inda zai je.
Naga ransa a bace ya ke na yi kokarin jansa da Hira ammh bai saki Jikinsa ba.

Ni dai bakina kanin kafata ban gayama kowa abunda ya faru acan ba,  bangaren Umma na sake sauka sai dai naje na gaida mama da Innani da ta yi ras da ita na dad'e a wajenta muna ta Hira Sai Abba shima da na jima a bangarensa muna gaisawa.
Sai can da rana sai ga Assadiq da Anty Surayya ta kawomin sinasir da miyar Naman rago.
Shi a lokacin yace zai kama hanyar Abuja ya kirani har mota ya ce min kada na rika biyema Sultana Don Allah kuma tunda baya nan na rika Tafiya da Siyama in gari ya waye sai mu dawo gidan su Umma.
Ni kuma sai naga ai wahalace cikin Sanyin murya nace"Ni dai ka barni wajen Umma Assadiq don Allah."
Cikin Fushi yace"To ni sa'anta ne da zan ce ga abunda za'ayi tace a'a."
Ni kuma ganin ya harzuka sai na Shiga lallashinsa ina nuna masa bakomai ya barni na zauna a wajen Umma sai yace min itama Surayya haka tace.
Dakyar ya amince na zauna wajen Umma, sannan anjuma na aika Farida da Siyama su daukomin kaya nace to.
Ko da Umma taji nan wajenta zan karishe kwanaki bata damu da Tambayar ba'si ba a tunaninta ko kila Saboda tafiyar Sadiq ne.
Ni kuma sai hakan yafi min kwanciyar Hankali Tunda ni bani son abun Rigima ko kankani.
Sai na koma kwana bangaren Umma komai yi min ake yi, hatta wankan su Asim kayansu sai dai a kawomin su an wanke su tas.
Ni ce ma ke yi ma Umma shara da wanke wanke da gyaran dakinta.
Shima tayi ta cewa na bari nice ban saba zama ba.
Sai gashi Umma har sai ta tambayeni me zan ci? Nace duk abunda aka bani zan ci.
Yara kuwa sai in suna kuka a kawoni na basu nono, madaran su kuma su Siyama sun iya had'awa bani da matsala.
Anty Surayya ta rakani da Umarnin Umma naje gidajen yan'uwan Assadiq, gidan Anty sa'ima da Sakeena sai gidan Anty Sadiya da Anty Sa'adatu har gidan Sajida mun je.
Ita dai sai wani yamutsan fuska take yi shiyasa bamu dad'e ba.
Washegari kuma ta zo gidan ta yini a bangaren Umma tana ganin komai.
Tana tashi daganan ta Biya wajen Sultana tace mata sai ta zauna bata Haihu ba  ga Umma can ya'ya yasa Hankalinta ya koma kaina ta fara ji dani kamar kwai a miya.
Aiko itama Sultana sai gata tazo gidan Ahalin tunda muka zo bata zo ba har sai da Umma ta mata tsiyan idonta kenan?
Sai tace wai bata jin dad'i ne.
Taganin ma Idonta ganin Umma ta goye Asim ta na ta kuma lallashin Asif da ke hannunta.
Gidanta ta yini kuma bata min mgana ba nice ma na gaisheta ta amsa kamar bata so.
Yara kuma ba ta taba Daukan su ba.
Tsaraban da na zo mata da shi na Humra na Dauko a gaban Umma na bata ta amsa a wulakance
Da farko ma kin amsa tayi sai da Umma tace"Karb'i mana Sultana."
Shiyasa ta karba ko ta gode batace min ba, nima ban nema ba tunda domin Allah na yi.
An kira sallar la'asar Daga ni har Umma muna salla, ni ina cikin Daki Umma kuma a falo take sallarta su Asim sun yi barci ta kwantar da su.
Shine suka fara d'aya na fara kuka d'aya ya saka kuka.
Suka fara yi kamar jiniya  Sultana na gefe kafarta daya kan daya ko ta daga kai balle ta Kallesu.
Cikin Tausayi Asim saboda kuka ya fad'o daga kan kujeran.
Umma na salla tunda suka fara kuka take Ihin ihim ammh ko ajikin Sultana.
Ni kuma na sallame ammh kunya ta hanani fitowa.
Inajin sanda wani cikin su ya fad'o ya Tsandara Ihun da kowa a gidan sai da yaji.
Chapter 54 · 0% Book details