← Book details Tmw Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 83

Sashe 21

Tmw Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar na falon Umma suma daga gaisuwa ya hade ransa ya duka ya gaida Mama ta amsa ta na ta kallonsa cikin mamakin ganin ko razana bata gani a tare dashi ba.
Daman kuma suna mganarshi ne ya Shigo sai suka yi shuru, suna ta maida yarda aka yi, Salima na kora musu wasu bayanan daga bakinta.
Mama saboda maganar na cinta sai da tace"Sadiq sai kuma mukaji wani al'amarin na ban mamaki?
Kai tsaye ya kallets kafin yace"Kamar na me fa?
Sai Mama ta kasa mgana, ta koma ta na kallonsa shi kuma kawai ya mike ya yi mata sallama ya fita.
Ya na fita Sakeena tace"Tabdijam yau akwai kallo a gidan nan"
Salima tace"Ya Sadiq ya iya lauya jibesa kamar baisan abunda ya faru ba."
Mama ta yi shuru saboda ta kasa mgana, Daman ita fa tasan Sadiq ba shi da Tsoro ba lalle su ga wani Razana a fuskarsa ba.
Shi ko ya na fita sai ya rasa ina za shi, saboda a wannan Lokacin ya na jiran Hukuncin Abba ne, Umma kuma daman yaga ta riga ta dauki nata.
Abu daya ya sani shine ya yi kuskuren yin aure ba da sanin iyayenshi ba.
Ammh bai yi kuskure domin ya yi aure ba, sannan zai Tabbatar da cewa an yi masa Adalci kuma an yi ma Siya itama adalci.
Yana Tsaye a haraban gidan, sai ga Subai'atu ta shigo gidan bayan mai adaidaitan da ta hawo daga tasha ya kawota da Sadiq ta fara cin karo ya na jingine jikin motar Abba.
Tun daga nesa ta ke hararansa shi kuma sai ya yi kamar bai gani ba ya tareta ya shiga yi mata sannu da zuwa.
Wani kallo ta yi masa kafin tace"Sai kuma idonka kenan Sadiq? Tare da bazawaarar matarka ta ka kake ko kai kad'ai kazo?
Sai da yaji wani iri, ammh sai bai yi mgana ba, shi fa daman yasan irin wannan Ranar ta na zuwa sai dai Shirya mata ne bai yi ba.
Sai kawai ya Daure Fuska kafin yace"Ni kadai nazo mana."
Saboda bayan Surayya da Saddiqa ba wanda yasan Hasiya ta zo.
Surayya tace kada Saddiqa ta yi zencen da kowa.

Kai Tsaye ta kallesa kafin tace"Kai yanzu kana karamin yaronka da kai har kasan kayi mata Biyu? Kuma ka rasa waza ka aura sai bazawara Sauran wani katon?
Kamar ya bata amsarta sai kuma ya fasa, yana jin zafin bazawarar da ta ke kiran Siya da shi sai dai shi yanzu fad'a ba nasa ba ne.
Shiyasa ya na tsaye Subai ta gama gayamasa dukkan maganganun da ke bakinta ta kuma zageshi son ranta shi da Siya sannan ta wuce cikin gida
Ransa ne yaji kawai ya fara baci, yana mamakin wai suna kyamatar Siya Saboda ita bawarawace  kenan susan komai da ya danganceta kenan.
Turkashi lalle akwai kura.
Gajiya ya yi da tsayuwa sai ya yi Tunanin ya tafi bangaren Abba, duk da shima kunya ya hanashi ya Kirasa.
Yana kokarin juyawa yaji Hon a bakin get sai ya dakata.
Mallam Tajudeen na Bude kofa yaga Motar Big sis, na shigowa gidan Saboda Hankalinsa na wajen Surayya bai kalli wacce ke gefenta ba ya Dauka cikin yan'uwansa ne dai.
Ammh kuma ya sha mamaki bayan Surayya ta faka Motarta ta fito, ta dayan bangaren yaga wata ta fito mai kama da Siya dinsa.
Kara waro ido ya yi sanda suka Doso sa, Hasiya na yin baya baya Surayya ta Rike mata hannu.
Abun da ya kara bashi Tsoro shine Tabbss Hasiya ya ke gani, ammh kanta na kasa ta kasa kallonsa Tunda ta Fahimci shine.
Na biyu kuma bakinsa na rawa yace
"Siya."
Ammh kamar ba su ganshi ba, ta gabansa Surayya ta wuce rike da Hannun Siya zuwa shashen Umma ko waiwaye.
Bakinsa a bude har suka shige kafin ya Rufe zufa yaji na keto masa ta ko'ina, sai kawai ya samu kansa da maimaita Hasbullahi wani'imal wakeel.
Ya kara Rikicewa ne sanda Motar Abba shima ta shigo gidan duk sai ya Daburce.
Ya Dauka shima Abba zai yi kamar bai gansa ba ne, ammh ga mamakinsa yana ganinsa shi ya fara washe masa baki ya na fadin"Magajin gida ashe ka iso."
Sadiq sai yaji kamar sai yanzu ne yake jin kara jin Guilty din abunda ya aikata.
Rumgumesa Abba ya yi yana masa maraba da zuwa, sannan yaja Hannunsa zuwa bangarensa suna tafe ya na fadin"Ya wajen aikin naku? Fata dai ba wata matsala ko?
Sai da Sadiq ya Hadiye miyau mai kauri kafin ya iya cewa"Alhamdulillah Abba."
Daganan ya ja bakinsa ya Tsuke, sai dai ya na ta bin Abba da kallo domin ya Fahimci yanayinsa.
Ammh ko a fuska bai ga wani alamun Sauyi tare da shi ba.
Ajiyar zuciya ya saki a Boye a kallah dai ya samu yar salama Abba bai Dauki zafi dashi kamar Umma da Sauran yan'uwansa ba.

*Janafty*
*TMWBK3007*

*TMW is a paid Novel, Pay 500 for regular or VIP N1K, Via 0552179550 Jamila Umar Gt bank, 09069067488*

Haba Babyn Habiby ya zaki zauna kina ta fama cutar infection, ke ce rashin sha’awa, ke ce jin zafi yayin tarayya, ke xche d’aukewar ni’ima, ke ce kai’kayi ki fitar farin ruwa da sauransu, an yi maganin asibiti da na gargajiya amma duka dai, tau share hawayenki ‘karshen matsalarki ta zo, da Honeydrops infection flusher ko cleanser pro sai kin yi dariya da godiya don zai wanke miki duk wata cutar sanyi. Akwai original sabaya ta gyaran breast su cicciko kamar baki shayar ba, akwai ta hips da mazaunai ki yi ma sha Allah ki samu kaya kema su miki d’as ki bar yawo da doguwar riga.

Na ce ba a nan muka tsaya ba muna da hadaddun kaya irinsu sweeteners, tighteners and wetners na tashin kan oga, wanda zai miki tukwicin dole, ke ko kurma ne sai ya yi magana ranar, don sumbatu ki dai samu abun rufe mai baki gudun ma’kota. Muna nan a garin Sokoto muna aike kowani gari kowacce kasa cikin aminci da rahusa. Kuna iya danna link din nan domin yi mana magana Kai tsaye https://Wa.me/2348167888934 ko kuma a kira 08167888934. Sai mun ji daga gareku isassun mata.

Shi dai Sadiq yana zaune ne kawai a falon Abba, ammh kwata kwata baya cikin cikakkiyar natsuwarsa.
Kunya tare da Nadama, da wani irin abu sun taru sun lullubesa da yasa ya kasa sakewa tare da Abba da ko a fuska bai nuna masa wani abu ba.
Sai ma jansa da Hira kawai ya ke yi, bayan sun gama Hiran aikin sai ya koma masa Hiran abunda za'a fitar Saboda azumi ya gabato.
Tun yana jin kunya har yazo ya sake ya na ba ma Abba amsa tare da shawarwarin da ya nema Daga bangarensa.
Ganin da ya yi Abba ya shanye duka abunda ya aikata sai Kunya ta lullubesa da yasa ya kasa zama a kan kujera sai gashi durkushe gaban Abba a kasa cikin wani Raunin murya yace"Abba don Allah ka yafemin, nasan na yi muku laifi."
Sai kuma ya kasa mgana ya koma ya sunkuyar da kansa kasa yana jin sai yanzu ne ma yaji meyasa ya aikata haka batare da ko sanin Abba ba?
Abba kuma shuru ya yi masa na wani Lokaci kamar bazai yi mgana ba.
Dalilin da yasa ya dago sai suka had'a ido da Abba da ya yi masa kuri da ido ya na kallonsa.
Sadiq ya kara marairaicewa ya na fad'in"Don Allah Abba ka yafemin, ni har ga Allah da kyakyawan Niyar taimako na yi wannan auran. Kuma.."

"Abubakar.."

Abba ya katsesa bayan ya kira sunanshi, da Sauri ya amsa har bakinsa na rawa, Abba cikin muryansa yace"Ni baka yi min komai ba magajin gida, tun ranar da na san kayi wannan auran albarkata ke tare da auran naka, ni laifi d'aya ka yi min da ya fi min ciwo fiye da auran da ka yi."
Abba ya karishe fad'a ya na kallon Sadiq da ke duke gaban Abba kamar zai yi masa sujjuda.
Cikin mamaki ya dago ya na kallonsa kafin yace"Abba wani irin laifi ne wannan, wanda yafi boye muku auran da na yi girman Laifi?
Mirmishi Abba ya yi kafin yace"Girman laifin shine har yau baka Fahimci irin girma da matsayin da ka ke dsshi acikin zuciyata ba Abubakar, girman yadda zaka iya yin abu mai girma haka batare da sanina ba, girman yadda ka ke tunanin ni bazan yi maka abunda ka ke so ba Matukar bai sab'a ma Shaari'a ba."
Sadiq yaji kamar ya fashe da kuka ya na kallon Abba yace"Wlh Abba.."
Abba sai ya dagamai Hannu kafin ya Cigaba da fad'in"Bacin raina d'aya da baka wareni cikin wad'anda za su zama Sirri kan sanin wannan al'amarin ba, Abubakar ko ba a zariya ba ko a birnin sin ne ka ga wata mace kana so batare da sanin kowa ba zan taka naje na nema maka auran ka, kuma nima zan iya sirrinta maka mganar har sai lokacin da ka so kowa ya sani, ai ni mahaifinka ne na fi kowa sanin kyakyawan hallayarka kuma ina da Tabbacin duk abunda zaka yi ko zaka aikatashi mai kyau ne"
Sadiq cikin murya kamar zai fashe da kuka yace"Abba na yi Tunanin baza ku amince ba ne, tunda akwai mganar Sultana."
Abba ya murmusa kafin yace"Ba wanda ya isa yaja da abunda Allah yace ayi, kai ai namiji ne kuma mijin mace Hud'u reras. Ba kuma wanda zai iya hanaka cike sunnar Ma'aiki Magajin gida, ni abu daya na ke so na muna maka shine ka yi kuskure ko a gaba ya kamata ka Fahimci ni nan zan iya tsaya maka a komai na Duniyan nan kuma na baka dukkan Goyan bayana sai dai in dan abun yafi karfina."
Sadiq na sauke Numfashin Salama yace"In sha Allahu Abba, nagode sosai Allah ya kara girma."
Abba ya amsa da Ameen Ameen ya na sake nuna masa kuskuran da ya aikata na Boye musu, tunda shi Lamariin aure ai ya wuce wasa.
Chapter 21 · 0% Book details