← Book details Tmw Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 83

Sashe 58

Tmw Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Shine sunan data gani ya kira kuma har Lokacin Tana kan layi, kishi ya gama Rufe mata ido yasa ta kara wayar a kunne ni kuma daman n sandare da mamaki tunda kunnuwana sun jiyomin muryan Assadiq yana mgana kafin na gama Tunanin tare da waye ya ke mgana naji muryan Sultana cikin Masifa ta na fadi'n"To tsohuwar kilaki, mai kwacen mijin wata macijiyar da bata ramin kanta, kin kwace min miji na kyaleki duk da haka bai isheki ba sai kuma yana tare dani ki rika kiransa kina masa barikin da kika saba ko?
A fusace Sadiq ya mike yana fadin"Ke sultana bani wayata, kada ki zageta fa"
Ammh sai ta koma da baya ta cigaba da chabamin manganun Tozarci da cin Mutumci ni kuma ban maida mata martani ba.
Illah hakurin da na bata na kashe wayar, ina Tunanin me yasa Assadiq ya kirani yasan cewa yana tare da matarsa?
Acan kuwa Sultana ta Rotsa wayarsa da kasa ransa shi kuma ya baci Haushi ya kwashe shi ya tsinketa da mari nan ta durkushe ta na kuka shi kuma ya duka yana Tattara wayarsa cikin Huci.
Sultana na Dafe da kunci tace"Ni ka mara Yaya Sadiq?
A fusace yace"Kirani da Abubakar dina, zai fi min da kirana da kike da yaya bana so."
Cikin kuka da hawaye tace"Akan wata banzar bazawarar matarka ka mareni? Akan matar da ka sameta a sauran wasu ka tozartani?
Cikin Idanuwanta ya kallah kafin yace"Eh a kan wannan bazawarar da kika raina a kanta na mareki, kuma daga yau ina so ki sani in kika Kuskura kika kara kiranta da banza sai na ci miki mutumci sunanta Hasiya ba bazawara ba, in bazaki Darajata ba a kallah ni ki bani Darajar da Allah yace ki bani, kuma gargad'ina da ke shine na rantse da wanda raina ke hannunsa in baki shiga Taitayinki dani ba sai na jefar da Rayuwarki a cikin Rayuwata sai lokacin ne zaki gane ke din banza ce a wajena."
A fusace ya kwashi farfasshiyar wayarsa zai wuce cikin daki sai kuma ya dakata ya Juyo yana kallonta ya nuna ta da yatsa Lokaci daya yana Fadin"au na manta ban fad'a miki ba, ita wannan bazawarar da kike  ganin kin rainata  ta fi min ke sau Dubu wlh"
Daga haka ya Buga iska fuu ya Shige dayan dakin ya Bango kofa ya bar Sultana Zaune a saman cafet ta na gunjin kuka.
Tun tana kuka da karfi har ta gaji ta koma yi a sannu kanta ya fara sara mata, nan ta yi barci bata sani ba Sanyin Asuba ya tada ita taja kafafunta ta Shiga dakinta.

Fuskarta ta kalla a madubi har in da ya mareta ya tasa, ita ba marin ne ya dameta ba sai da yace wai Hasiya ta fita a wajensa sau dubu, ita yanzu ashe a banza ya ke kallonta?
Dakyar ta yi sallah sai kukanta ya Dawo Sabo.
Ta rasa wazata tunkara gashi ta bata rawanta da Tsalle a wajen Umma.
Kuma bata isa ta tunkari gidansu da wannan mganar ba kilama Babanta sai ya kara mata.
Daga karshe ta kira Surayya ta na kuka ta gayamata abunda ke faruwa
Saboda tasan su Sajida ba abunda suka isa su yi, tunda Sadiq ba jin mganarsu ya ke yi ba gwara Big sis din.
Surayya kuma Hankalinta ya tashi jin harda duka da safiyar nan duku duku ta yi Driving zuwa gidan  a Haraban gidan ma suka hadu da Sadiq ya Dawo masallaci Tunda ya ganta yasan Sultana ce ta kirata ko d'ar bai ji ba shi daman fa ya gaji gwara a san abun yi yarinya karama bazata zo ta hanashi Zaman lafiya ba, ina bata isa ba wlh.
Tare suka shiga gidan tana Tambayasan ina matar gidan? Yace shi bai sani ba ta Dubata.
Ita ta shiga dakinta ta sameta ta na kuka.
Sultana ganin Surayya yasa ta kara jiniyan kukanta.
Dakyar ta lallasheta ta yi shuru kuma ta nuna mata wajen marin taga ya Kumbura.
Duk da Sultana ta fadin duk abunda ya Faru Surayya bata tsaya anan ba ta tarasu tare tace kuma Sadiq ya yi mgana.
Yace shi bazai ce komai ba in har ta bari ya yi mgana sai ta raina kanta.
Abu daya ya sani ya gaji da zama da ita Tunda tana zargin baya yi mata adalci gwara ta fad'i abunda ta ke so ya yi mata kowa ya Huta.
Sai Tsoro ya kama Sultana jin abunda yace ta fara kuka Dakyar Big sis ta lallashesa ya fadi laifin da take yi masa.
Ya ce na farko bata darajashi, na Biyu ta raina shi na uku ta dauki wasu ta fifita sama da shi, na hudu kishinta na Hauka na Biyar ta na zarginsa da bata zama lafiya da shi.
Nan fa Surayya ta yi ma Sultana fad'a Sosai ta kuma sakata ta duka ta bashi Hakuri tare da alkwarin zata bar komai da ta ke yi zata kuma gyara dakyar yace ya Hakura ammh in ta kara ya rantse da kansa zai sakata a Mota ya maidata shinkafi.
Tunda ta raina Umma itama yanzu bata da kima acikin Idanuwanta.
Shima Sultanan ta fadi na shi laifin maganarta daya ne baya sonta yafi son Matarsa a kanta kuma yana yin mata kaza itama baya yi mata.
Mgana dai duk na zarge zarge da kishin Tsiya.
Surayya dai nan shima ta nuna masa ya gyara sannan tace kada ta kara jin ya kara kai hannu Fuskar Sultana matarsa ce ba Jaka aka aura masa bq shima ya ce ya yi kuskure bazai kara ba kuma ya bata Hakuri a gaban Anty Surayya, sannan shima yace ta ja mata kunne ta daina zagin masa mata yadda bazai bari siya ta zageta ba shima bazai bari Ta zageta a gabansa ba.

Nan dai Surayya ta zaunar da su gabadaya ta yi ta musu nasiha itace sai Goma na safe sannan ta koma Gidanta bayan ta tabbatar ta gyara barakan dake Tsakanin su.
Ta dai yi kokarin kebewa ita da Sultana ta gayamata gaskiya ta daina Biye ma zugan kowa sannan kuma ta Rike sirrin mijinta ko Tambayanta akayi tace bakomai..sannan ta yi masa Biyayya ta daina ja inja da shi sannan ta gyara kanta da jikinta har maganin gyaran jiki tace zata aiko mata da shi don Allah ta gyara.
Ta kuma yi mata alkwarin zata gyara sannan tace ta shirya taje ta ba ma Umma Hakuri, ta yi fushi da ita.
A lokacin ta yi kuka ta nuna Nadamarta.
Kuma tana da tabbacin in taji shawaranta bazasu kara samun matsala da Sadiq ba, in kuma bata ji ba komai zai iya Faruwa.
Yanayin mganar Sadiq tasan da gaske ya ke yi ya gaji.
Kuma gajiyarsa daidai ya ke da Faruwar komai.

Sannan Surayya ta sakata ta karb'i lambar Hasiya a wajenta ta kirata ta bata Hakuri Hasiya tace ita bakomai bata riketa ba, kuma a gaban Sadiq din aka yi, sannan shima tace kada ya sake Doguwar waya in dai yana tare da d'aya daga cikin su Saboda a zauna lafiya.
To kamar dai Abun ya Dore Sultana ta gyara ta koma kamar Farkon auransu, sai ga shi har kwana ya kara sai Ranar Monday ya koma Abuja.
Sannan sun je tare ranar lahadi da Daddare ta ba ma Umma hakuri.
Umma tace ta yafe itama ta kara yi mata Fad'a sosai.
Kamar taga uwar bari ne tunda ko su Sajida sun kirata su ji Labari su kara zugata sai taki gayamusu komai.
Ammh fa kishin Hasiya da tsanarta na nan acikin ranta sannan Babban Burinta yanzu ta samu ciki itama ta Haihu.
Har ta fara damuwa auransu ya fi shekera ba ta samu ciki ba, shikuma sai yaga kamar abun ya fara taba mata Tunani sai ya koma yana lallashinta duk sanda yazo, ko kuma suka yi mgana ta waya.
Yana nuna mata Haihuwa ta Allah ce itama bai manta da ita ba ta yi ta addu'a zai bata.
Har fa asibiti ta saka sukaje aka auna su likita ya tabbatar da suna lafiya sannan ta yarda lafiyar kalau lokaci ne bai yi ba.
Saboda ta rage damuwa yasa ya matsa mata ta siya jamb ta zana kuma ta samu Score mai kyau.
Nan take ya nema mata Gurbin karatu a jami'ar Gusau.
Ta fara karatu a tsangyar B.A English.
Sai karatun ya fara Dauke mata Hankali da wasu abubuwan ammh kishi nan da zargi bata daina ba tadai rage da kuma nuna an yi mata ba daidai ba.
Shi kuma ya sha zaunar da ita yana fad'a mata tafi Hasiya zama acikin gata, ni acan a gidan haya na ke zaune, da ire iren mganganunsa yasa ta fara Fahimtar gwara ita tunda tana cikin gidan sa ne.
Chapter 58 · 0% Book details