← Book details Tmw Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 83

Sashe 16

Tmw Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sai da Saddiqa ta koma Shashen Umma sannan ta kira Surayya, nan ta ke fad'a mata ta kira Abba tace kada ya fita zata zo akwai maganar da ta ke so su yi da shi, sai yace daman yau ba da wuri zai fita ba sai an juma.
Sun Tsaida mganar Daga Umma sai Abba sai mama da Innani za su yi mgana daga baya in komai ya daidaita sai mganar ta fita ga sauran yan'uwa.
Tunda Surayya ko Sajida bata nema ba  a wannan karon ba Hurumin su ba ne.
Da wuri Surayya ta zo gidan Umma dai mamaki sai ya kamata tun ballatana da taga sun kule a daki ita da Saddiqa, da kuma sun ganta ta shigo sai su yi tsuru tsuru, Umma dai ta na kallonsu a ranta ta tabbatar akwai wani abu, tunda ta shiga su gaisa da Abba ya ke gayamata wayar da suka yi da Surayya.
Gabanta ke fad'i fatan ta d'aya Allah yasa ba wani abu na mara kyau ya samu d'aya daga cikin yaran ba.
Zuciyar Uwa duk sai ta firgice zullumi ya shiga ranta duk sai ta kasa sukuni.
Surayya da kanta taje Bangaren Innani bayan sun gaisa sun taba Hira, Innani na bata labarin Farida mai kirki ga ba ta da kiyuwa ba kamar su Siyama ba.
Har Innani na fad'in ba ta yi Halin uwarta ba, Surraya dai na jinta ta na faman dariya.
Da ta ga Hiran ta ki karewa ne yasa tace ma Innani zata rakata bangaran Abba za su yi mgana ne.
Innani ta karkace kai kafin tace"Shi Sulaimanun ne don zai yi mgana da ni, sai na je da kaina?
Surayya sai ta kasa mgana Innani ta fara masifa ta na fad'in"Shi kuma Sulaimanu lalacewa ne ko bakin duniya ce ta fara kamasa da ni ina uwarsa zai ce sai naje da kaina har bangaransa? Naga dai daga shi har matansa nan suke zuwa su tarar da ni, ko da suna da mgana da ni."
Sai Surayya ta Fahimci kuskurenta da Sauri tace"Yi hakuri Innani , bari mu muzo sai a yi mganar a nan bangaren."
Innani ta tabe baki kafin tace"Da dai yafi muku."
Dole Surayya ta koma ta fad'ama Saddiqa yadda suka yi da Innani, sai Saddiqa tace ba matsala sai ayi achan din.

Surayya ce tace ma Umma su je bangaren Innani su yi magana, Umma bata ce komai ba illah tace to kawai, Ita Mama Saddiqa ta je ta fad'a mata itama cikin mamaki tace lafiya? Saddiq tace suna fatan haka.
Abba daman ba shi da matsala shi ya fara ma isa bangaren Innani, ko da su Umma suka zo sun iske su suna Hira na Tsakanin uwa da abunda ta Haifa.
Ga dai Umma ga Mama ga Abba sai Surayya da Saddiqa ga Innani a gefe wajen mintuna goma falon ya Dauki Shuru ammh tsakanin Surayya da Saddiqa an rasa me fara cewa wani abu.
Sai da suka zo gabansu Umma suka ji sun sare, barin ma Surayya da ta zo da kwarin gwiwanta, Saddiqa kuma Daman tace ita bazata fara mgana ba tunda Surayya ta karb'i fad'an ita zata san yadda zata yi.
Innani ta gaji da zama sai ta kawai ta gyara zama ta na fadin"Wai me ya faru ne? Naga kowanne ya zauna ya yi shuru ko an yi mutuwa ne?
Abba ya yi gyaran murya kafin yace"Innani daman Surayya ce ke son magana damu kan wani batu da bamu sani ba"
Innani ta yi karamin tsaki kafin tace"Shine kuma ta taramu kamar wasu sa'anninta ta tsaya ta na kare mana kallo?
Da Sauri Mama tace"Ki yi hakuri Innani, ke kuma babbar yaya muna sauraranki Allah yasa lafiya, ni wlh kada ku kasheni da zullumin me ke faruwa?
Umma ta kad'a kai kafin tace"Wlh nima baki ji zuciyata ba, gabadaya na kasa sukuni don Allah ku fad'amana Abunda ke faruwa."
Surayya ta kalli Saddiqa itama ta kalleta, Saddiqa ta tsinguleta alamun ta fara mgana, Dakyar Surayya ta iya jarumtar fad'in"Umma Abba, Mama Innani, magana ce a bakina sai dai yadda zan fad'eta ne kuma ku fahimceta shine Fargabata."
Mama tace"Topha? Muna sauraranki in sha Allahu kuma zamu Fahimceki."
Surayya ta Sauke ajiyar zuciya kafin tace"Dama. dama akan maganar Sadiq ne."
Gabadayansu a tare cikin firgici suka Had'a baki wajen kiran sunan Sadiq.
Cikin tashin Hankali Abba yace"Me ya faru da Abubakar din?
Umma kuma da jikinta ke rawa da Sauri tace"Surayya ki fad'amin me yasamu Sadiq ne kada zuciyata ta Buga."
Mama kuma sai salati ta ke yi, Innani kuma kuka kawai ta saka ta na fadin"Mun shiga uku mun lalace wani mugun abun ne ya sama mar min jika na? Namiji kwara d'aya da Sulaimanu ya mallaka magajin wannan gidan mijin sulsana mun shige su, me ya same shi? Ko mutuwa ya yi ne ku ke boyemana achan Habujan?
Innani ta karishe fad'a cikin Ihun kuka.

Jin maganar Mutuwa da kuma yanayin Rudewarsu yasa Da Sauri Saddiqa tace"Ba fa maganar Mutuwa ba ce ko wani abu, Lafiyan Sadiq kalau babu abunda ya same shi."
A tare Umma da Abba suka Sauke Numfashi  mama ko sai da tayi hamdala.
Innani ne ta tsaya da kukanta ta na kallon su Surayya ta cikin gilashinta na wani lokaci kafin a fusace tace"To karya ku ke yi, in ba wani abu ya sameshi ba uban me yasa baku fad'i abunda ya faru ba tun dazu? Kun tsaya kuna ta raina mana wayau.'
Ta karishe fad'a cikin masifa, Abba dai jikinsa gabadaya ya yi sanyin da ya kasa mgana.
Umma kuma zuciyarta ne taji ya na gudu sosai kamar dai wacce wani abu ya sameta.
Cikin karfin hali tace"Zaku fad'a mana ne, ko kuwa sai mun mutu da zullumi.?
Da Sauri Saddiqa tace"Sadiq ne ya yi aure Umma."
Gabadaya sai falon ya yi shuru kowa na auna mganar Saddiqa.
Innani ce ta yi tsaki kafin tace"Ji wani shashanci daman ai kowa yasan magajin gida ya yi aure, daman dalilin dayasa ku ka taramu anan kenan? Kai sulaimanu yi tafiyarka sabgoginka yara nan wasa za su yi da Tunanimmu."

Surayya ta sauke ajiyar zuciya kafin tace"Innani ba wannan auren ba, kafin.. kafin ya auri Sultana to daman ya auri wata achan zariya."
Sai falon ya kara Daukan Shuru Surayya kawai a ke kallo.
Umma ta sandare a zaune, Innani kuma har gilashinta ta cire ta kara maidawa ta kara gyara kunnuwanta kafin ta kalli Abba ta na fad'in"Sulaimanu ko dai kunnuwana sun samu matsala ne?
Me nake ji Ana fad'a na wai?
Abba ya yi shuru bai ce komai ba, Mama ce ta kalli su Surayya cikin rawan baki tace"Ku yi mana karin bayani, bangane ba wani irin aure kuma?
Surayya kanta na kasa tace"Aure ya yi a garin Zariya tun Lokacin ya na bautar kasa, shekaru uku da suka wuce."
Mama ta Bud'e baki cikim mamaki kafin tace"Da gaske ku ke yi? Wani irin aure kuma ni Saratu?

Saddiqa ta gyara zama ta fara ba su labarin yadda akayi suka ga hoton Sadiq da Hasiya da yadda suka Bincika suka gano gaskiya da zuwan Surayya zariya ita da Sajida. Da kuma karin tabbaci daga bakin Hasiya tare da Shaidar ma cikin jikinta.
Mama ta koma ta yi zaman dirshan a inda ta ke  maimaitawa ikon Allah kawai ta ke yi.
Umma kuma kanta na kasa bata Dago ba, ammh a cikin kasan ranta mamaki ne da al'ajabi Abba kuma ba wanda zai iya cewa ga yanayin da ya shiga.

Innani kuma shuru tayi kamar bata ma afalon Inaga tsabar Mamaki ne ya hanata mgana wannan karon.
Abba ne ya yi gyaran murya kafin yace"Shi Sadiq din baisan kun san labarin ya yi Auran ba?
Surayya tace"Eh Abba, ya yi kokarin ya fad'amin ammh kuma ya kasa, daman tunda abun har ya fallasa naga ya kamata ku fara sani."
Abba ya jinjina kai kafin yace"Ita matar tace Tahir ya san da mganar auran?
Surayya tace"Tabbas haka ta ce ya sani"
Kafin Abba ya yi wata magana Umma ta d'ago ta na kallon Surayya cikin wani yanayi kafin tace"Shi Sadiq din da kansa ya yi aure batare da sanin mu ba?
Tsakanin Surayya da Saddiqa sai aka rasa me bama Umma amsa.
Mama ce ta rike hab'a kafin tace"Ni kaina ina ta mamaki, Sadiq fa? Me yasa Sadiq da hankalinsa da Tunaninsa da iliminsa sai ya aikata haka? Aure fa kuka ce? Kuma kun ce an dade ma tunda su Surayya sun je sun ganta har da ciki"
Chapter 16 · 0% Book details