← Book details Ƙauna Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 56

Sashe 9

Ƙauna Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Baki É—aya ita shi motar suka zubama ido ganin irin wannan motar har cikin gidansu, cikin tsananin farin ciki zeey ta fara yowa waje. Wani irin ware ido Fatima tayi ganin aunty zeey É—inta. Ai da wani irin bala'in gudu ta nufeta wata iriyar kyakkyawar runguma ta mata, tare da buga tsalle ta sake ta Tana nufar gaban motar. Babu tunanin komai a ranta ta ta buÉ—e gaban motar Ba tare data san waye a mazaunin driver ba ta wani faÉ—a jikinsa.
Tare da ƙanƙame sa tana sakin dariyar farin ciki tare da cewa.

"I miss you fiye da billions dollers my JININ JIKI ♥️🤍♥️"

Wani irin ɗaukewa numfashinsa yayi ganin mace kwance ɗare-ɗare acikin jikinsa. Cikin wani irin masifar ɓacin rai da zallar takaicinta ya buga mata wata razananniyar uwar tsawar data sanya ta buɗe Idanunt, tare da toshe kunnawanta da duka hannayen ta. Tarrr idanunta masu kama dana mage suka faɗa cikin na mutumin da bata taɓa ganin irinsa akaf cikin duniya. Da wani irin bala'in ƙarfi tayi ƙoƙarin janye jikinta.

Wani irin riƙi tsintsiyar hannunta yayi tare da dawo ita dab dashi har hucin Numfashinsa na bugar nata, babu zata babu tsammani taji sauƙar wani irin lafiyayyan mari a saman fuskarta.
Tare da tunkoɗa waje da wani irin azababben ɓacin rai ya figi motarsa ya fice daga harabar gidan baki ɗaya. Su kuwa yaya jay zeey tana fita shima ya fito yana fita ita kuma Fatima iyayen hankali ta banka kanta cikin motar da tajaza ma kanta shan mari a karon farko.
Duk cikin su babu wanda yasan abinda ya faru, kawai dai sunji ƙarar saukar mari ne, cikin sauri jay ya juyo gareta yana tallafarta ganin sai tangal tangal take tana Neman faɗuwa. Tana jin ta jikin mutum ya wani irin fashe da kukan azabar raɗaɗin marin data sha daga ALIEYO. "Allah ya isana, Allah yasaka min!, Allah bazai taɓa barin ka haka ba saiya biya min haƙƙin na, shege tsinan.........

Tsittttt ta gimtse bakinta jin wani irin bugu da akamawa bakin nata......

FAN'S CLUB ƘAUNA BIYU

Nake cewa sai kuma Allah Ubangijii ya kaimu bayan sallah da aran rai da kuma lafiya, zamuci gaba daga inda muka tsaya.
INSHA ALLAH

*AMMEY LAYLERHNKU* mai ƙaunarku mai ƙaunar farin cikin ku take ce muku bye bye bye bye saimun haɗe Insha Allah.

Duk wanda yaji daɗin littafin yama mahaifina adda'a Ubangijii ya jaddada rahamarsa a gareka mahaifin da bana da kamar ka. Adda'oi Na ba zasu taɓa dena zuwa gareka, har nima sai randa Ubangijii na ya amshi tawa rayuwar.

Bissalam 🙏🙏🙏🙏🙏

Allah Ubangijin talikai ya sadamu daduk wani Alkhairinsa dake cikin wannan wata na RAMADAN

*~ALLAHUMMAH BALLIGNA RAMADAN KAREEM 🤲🤲👋~*

08104493215

*💘🌺ƘAUNA BIYU 🌺💘*

~Heart touching love, with love a side 🤍🤍~

Page 11&12

*BY*
*AMMEY LAYLERH*

✯ *~🌠 OFFICIAL MIRRAH 💫~*

*Alhamdulillah forever and always 👏*
_________________________

♥️🤍♥️

Ɗago kanta tayi don ganin waye ɗalle mata baki, idonta ta sauƙe akan yaya jay kansa ya jinjina mata alamar ehh shine mai bugun. Da sauri Aliyu shureim ya ƙara so wurin yana kama hannuwanta cikin nashi, fuskarta ya ɗago da niyar share mata hawayen dake kwance saman fuskarta, da wani irin sauri yaja baya ganin shatin kwanciyar yatsun hannu kwance a saman fuskarta. Ganin yadda ya yine ya sanya yaya jay dubansu su duka.
"What happens" ya tambaya yana mastowa gare su, cikin firgici Aliyu ya shiga nuna masa fuskar Queen kafin cikin in'ina ya shiga faɗin. "Waye shi?, akan wane dalili zai maran min fuskarn matata?, dubi yadda ya kumbura mata fuska, dubi yaya jay!" Yayi maganar yana juya masa fuskar Queen. Shima sosae zanen yatsun hannun alieyon daya gani kwance saman fuskar fatiman ya taɓa shi. Sai dai Samm bai bari hakan ya bayyana a zahirance ba, yasan kaɗan kenan daga cikin aikin alieyonsa da aka ci ma Sa'a bai tattaka taba, domin zai iya rantse wa yafi kowa sanin halayen Alie karan kataf.
Kama hannuwanta yayi zuwa ciki Aliyu ne yabi bayansu da jakankunan kayansu, zuciyarsa na masa wani irin zafi. Sosae yaji yana jin haushin wannan abokin yaya jay É—in, duk da kuwa bai ga koda mai kama da fuskarsa bane. Amma yaci alwashin duk randa suka haÉ—u saiya rama mata marin fuskar Queen É—in shi da yayi wannan alkawarin sane.
Ita kuwa dama tuni aunty zeey ta shige ciki domin kukan da julaibeeb ke mata, dole tayi cikin gidan ta barsu tsaitsaye a wurin. Suna dab da shiga main Parlour yaya Nurien da bai san da xuwan yayan nasu bane, Saida aunty zeey ta shiga aikuwa da gudu ya fito cikin tsananin murnarn zuwan ɗan uwan nasa, hannun teemah ya saki yana buɗewa ƙanin nasa hannayensa, rungume juna sukayi cikin tsananin murna da farin ciki. Kai tsaye teemah kan ummie tayi tana faɗawa jikinta tare da sakin wani sabon kukan. "Auta miye hakan?, me saya samm baƙya sanin kin girma ne?" Ummien tayi maganar tana janyeta daga jikin ta, da sauri kuma ta dawo da ita ganin zanen yatsu kwance saman fuskarta, "me ya same ki haka?, waye ya miki irin wannan marin?" Cike da kaɗuwa ummien take tambayar ta.

Kukanta taci gaba dayi, yaya Nurien ne ya matso kusa da ummien yana tambayar abinda ya faru shima, ganin yadda fuskar Shalelen nasu yayi wani irin jaaa da kumburi.
"Nima ban san shi ba!, don kawai na faɗa jikinsa nasha yaya jay shine ya buga min marin, ya hankaɗoni waje". A tare ummie da yaya Nurien suka dubi yaya jay, shi Nurien irin kallon da yake duban shi daban sakamakon ummie da take buƙatar ƙarin bayani. Sumar kansa ya ɗan shafa kaɗan.
"Rashin hankali ta masa shine ya buge ta"
"Wai waye ka faÉ—amin mana kake min wata kwana-kwana"

ÆŠan risinar da kansa yayi tare da faÉ—in.
"Ummie ALIEYO Naaaaaa ne"
Ajiyar zuciya mai É—an qarfi ummie taja tana komawa zaune, don ko kaÉ—an bata kawo shi É—in bane "Yana ina?" Kai tsaye ta tambayi jay É—in.
"Ya fice a zuciye"
"Kuma shine ka bar shi ya tafi dan kaima baka da hankali!, bayan kafi kowa sanin halin sa, amma ka barshi ya fita a irin wannan yanayin" tayi maganar tana duban yaya jay.

"Afwan ummienmu, wllh kafin ma musan abinda ya faru harya bar gidan babu damar na bishi kuma"

"Shikenan Allah ya kiyaye "shine kawai abinda ta iya faɗi tana Adda'ar Allah ya ya tsare shi acikin zuciyarta. Domin bata manta irin halin daya shiga ba a loƙacin mutuwar matarsa.
Kasancewar ita da ammiensa aminai ne sosae ta dalilin abokantar dake tsakanin Æ´aÆ´ansu mai girman gaske. Yaya Nurien ne ya dubi queen tare da sakin dariya tuno da zancen yayansu na ranar, sai gashi tun ba'a je ko ina ba haÉ—uwarsu na farko ya kasance duka ne, ido kawai yaya jay ya zuba masa suna haÉ—a ido ya kuma sakin dariya yana barin parlourn a guje ganin irin kallon da yaya jay yake mishi.
Aliyu da tun É—azu yake zaune kansa a É—age ne ya É—ago kansa tare da duban yaya jay.
"Yaya amma dai ba za'a barshi haka ba dole a ɗau mataki,Wllh bai daki banza ba dole nabi mata haƙƙinta" ummie ta dube shi a tsanake tace "kayi haƙuri Aliyu duk bazai kaimu ga haka ba, shiɗin babban abokin yayan kune, kuma daɗi da ƙari kasan mutuniyarka ba hankali ke gare ta".
Ajiyar zuciya kawai ya saki yana ficewa a parlourn.
A tsanake yaya jay ya shiga gaisawa da ummien nashi, cikin fara'a dajin daÉ—i ummine ta amsa shi tana faÉ—in, "ai nasha wannan karon ma bazaka zo mana azumin ba kamar wancen karon"

Da murmushi a saman fuskarsa yake faɗin...."ba dole na dawo ba tunda wannan uban ƴan miskilancin yayi missing kunun gyaɗar queen, kinsan a duniya babu abinda yake burgeshi a fannin abinci sama da kunun markaɗaɗɗiyar gyaɗa" ƴar dariya kawai ummie tayi tana faɗin. "Shi kuma gashi da ƙin kai, kace badan mu kazo Bama mu daina murnarn zuwan ka"
"A ahhhh na tuba ummiena nace Allah,wllh dama nayi zuwan shi kuma ya isheni da ƙarafin na dawo, kuma nasan duk akan kunun nan ne"
Dariya ummie taci gaba dayi domin lallei alieyo halinsa sai shi. "Kuma wai kin san wani abu ummie"
"A ahh saika faɗa babana" ummien ta faɗa tana ƙara dubansa.
"Wllh taka nas ya sanya ammienmu gaba Saida yasa ta markaɗa masa gyaɗar, amma data dama mishi ɗan iska sai yaƙi sha wai babu daɗi kamar na gidan nan".
Sosae suke cin dariyarsu su biyu ita kuwa teemah tana jinsu duk haushin su ya ishe ta, ganin babu wanda ya kuma bi ta kanta duk cikin su. Kwafa taja a ranta tace (aikuwa zaici ubansa wllh bazai ƙara sha mana kunu ba, kuma ai dama nice mai so!, kuma nice mai damawar to Nima na daina son kunun daga yau). Duk acikin zuciyarta take wannan maganganun, kafin ta tashi tabar musu parlourn tana nufar ɓangaren aunty zeey.

♥️🤍♥️
Chapter 9 · 0% Book details