← Book details Ƙauna Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 56

Sashe 26

Ƙauna Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sosai Abba ya tsureta da ido ko ƙyaftawa baya yi, ganin yadda Dr ɗin take ta mulmula baki alamun maganar da take son furta wa mai girma ce.
"A gaskiya nayi mamakin yadda aka yi ƴar ƙanƙanuwar yarinyar da bata fi 17 to 18 years ba ace ta kamu da hawan jini ba.
Amma da sauƙi kar ku tada hankalin ku zan ɗorata kan magani In shaa Allah za'a dace"
TundA ta fara maganar suke binta da IDO taya ma har zata yi wani tunanin kwantar musu da hankali bayan tace musu fatimansu na É—auke da cutar hawan jini. Sosai hankalin su ya tashi hannu na rawa ummie ta É—auka file É—in tana yin woje xuwa wurin su yaya jay.

Da sauri suka nufo ummien ganin yadda hankalin ta yake a tashe, yaya jay ne ya amshi file ɗin dake riƙe a hannun ta wani irin ja da baya yayi tare da kaiwa jingine da jikin ginin. File ɗin na faɗuwa ƙasa.
Saurin É—aukar file É—in yaya Nurien yayi shima dai hakan ce ta kasance a gare sa domin shi harma yafi yaya jay shiga shock É—in.

Saurin rufa musu baya sukayi ganin Abba da Dr na shirin shiga room ɗin da aka kwantar da ita. Koda shigarsu kwance suka tarar da ita hannunta ɗaure da kanular ruwan da aka ɗaura mata. Zuba mata Ido suka yi baki ɗayansu cike da tsananin tausayin ta taya ma za'a ce yarinya ƙarama kamar queen ɗin hawan jini ya kama ta.

Suna a tsaye jigum jigum saiga Mama ta faɗo ɗakin ita da fareedah ahujajan, zaune takai raɓas gefen gadon da queen ke kwance hannunta ta kamo tana haɗewa da nata, kafin hawaye irin mai ɗacin nan ya zubo mata na tsananin tausayin fatiman.
Ta sani har yanxu idan da wanda mutuwar Aliyu shureim bata saki ba to mafi ƙololu ita da queen ne, "kiyi haƙuri! Kiyi haƙuri Fatima Allah baya taɓa barin wani dan wani, da yana bari to da ya bar mana Aliyu shureim ɗinmu ya ɗauki tawa rayuwar!" Sharrrrr haka hawaye ya wanke mata fuska tuni.

Jin alamar damshim ruwa a jikinta ya sanya ta buÉ—e kunburarrun idanunta, Ahankali ta shiga buÉ—e su duk kuwa da nauyin da suka mata ga kanta da take jin tamkar zai rabe gida biyu.

Da sauri Abba da shine kaɗai ya lura da farfaɗowar nata ya kama hannunta ɗaya cikin kwantar da murya kaɗan yace, ” Sannu fatin Abbanta faɗa min mi ke maki ciwo yanzu? "
Kai ta girgiza alamun babu sai ya cigaba da cewa "to faɗa min minene ya saka ki damuwa har kika shiga wannan hali?Dr tace za ki iya samun sauƙin ciwon"

Da mamaki shiga kallon Abban jin abinda yake cewa, sai kuma tayi saurin duban gefen ta jin kamar motsin wani abu. Ganin Mama ce riƙe da ɗayan hannunta ya sata ɗan ware idon ta kafin ta shiga bin room ɗin da kallo karan kataf ta gama fuskantar komai sai yanxu ne komi ya shiga dawo mata cikin Brain nata lumshe ido tayi. Tana koma wa ta kwanta.

Ganin ta farka kuma daman ciwon da sauƙi ya yazo mata yasan ya Dr laylerh sallamarsu, tace zata na xuwa dubata akai akai sosai suka gamsu da maganar nata haka yasa suka tattara suka koma gida.
Kowa na ƙoƙarin ganin ta dawo normal nata.

__________★★★___________

# New York

Cikin nitsuwa yake tahowa sanye da farin rigar sport designer ta companyn NIKE mai É—auke da cap da dogon wando alaman daga street warming execise ya ke.
Ko ina ya ɗauki shirun safiyar ranar ga sanyi irin mai ratsa jikin nan sosai don haka a gurguje ya bude ya faɗa bathroom yana sakar ma kansa shower yau kusan 2 Months keñan da zuwan sa amma komai na nan a yadda yake saima ƙara hauhawa da abubuwan suke ya ɗan yi duhu kaɗan ba kamar sanda yazo ba.

*💘🌺ƘAUNA BIYU 🌺💘*

~Heart touching love, with love aside 🤍🤍~

Page 27&28

*BY*
*AMMEY LAYLERH ✍🏻♥️*

✯ *~🌠 OFFICIAL MIRRAH 💫~*

Yau page É—in nakine Zainabu mai tagwayen suna, na baki kyautar page É—in a matsayin gift na tayaki murnar zagayowar ranar haihuwarki.

# Happy birthday 🥳 🎉 to the most wonderful sister in the world!
# I hope your special day is as amazing as you are 🥰. May all your Insha Allah turn to Alhamdulillahi.

Happy birthday once again DEAR 💐💐💐💐💐💐💐

As gifts 🍢🍿🥂
____________________

# _LOVE ASIDE❤️‍🔥🔥_

♥️🤍♥️

Yau wajen kwanaki biyar keñan da sallamo queen daga asibiti, amma har xuwa wannan loƙacin komi bai sauya daga yadda yake ba. Saima zancen auren dake ta ƙara kusanto kansa a duk loƙacin da zataji ana maganar auren nan ji take Kamar zuciyarta zata faso ƙirjinta ta fito haka take ji a duk lokacin da maganar aurenta zai faɗo mata,ta kanji duniyar ta ƙara mata zafi da baƙin cikin zamanta a ciki, tabbas ta san da Ubangiji shi ke jarabtar bayinsa ta ko wacce siga, tasan tata ƙaddarar mai zafi ce zafin da mutan bazai taɓa tunanin ji ko gani a aikace ba sai har in ƙaddarar hakan ta gitta maka. To anan ne zakafi kowa fashimtar ya raɗaɗi da kuma zafin abin yake.
Wasu zafafan hawayen da suka kuma zubo mata ta share tana kawar da kanta gefe tare da karanta Addu'o'in da zasu sauƙaƙa mata zuciya. Cikin ƙudir ta Ubangijiin Rahama tuni taji zuciyarta tayi sanyi, a take wurin kuma barcin data kwana bata yiba ya ɗauke ta.
Bangaren ummie kuwa ganin shirun yayi yawa ne ya sanya ta miƙewa tana nufar ɗakin nata, tare da faɗin. "Fatima lafiyar kuwa daga shiga ɗaukar...... Sai kuma taja ta tsaya turus ganin ta kwance saman tiles ɗin ɗakin, tana barci irin wanda baka shiryarma zuwansa ɗin Nan, a Zahirance dai zaka iya ƙiransa da barcin wahala, ko daga yanayin yadda ta takure wuri guda, bata tashe ta ba illa binta da ido kawai da tayi, cikin tsananin tausayama rayuwarta.
Fita tayi daga ɗakin tana komawa kitchen nan yaci gaba da aikin ta cikin rashin kuzari, da jin babu daɗi aceñnn ƙasar ranta. Sosae Fatima iya barci na mamaki, koda sallar zuhr da Abba ya shigo yana tambayar ta ina Fatima tace masa rana cenñnn tana barci tun ɗaxun, Haka ma yayyenta duk wanda zai shigo saiya tambaya queen har ɗakin suka bita ganin kuma har loƙacin tana barcin ne ya sanya su barin ɗakin kowa yana kama gabansa.

3:47Pm
A hankali queen ta shiga buɗe idanunta da take jin nauyin su ya ragu sosae har ta buɗe su duka bakinta ɗauke da Addu'ar tashi a barci. ƙafafunta ta fara saƙƙowa ƙasa tana miƙewa sai kuma tayi saurin mutsitstsike Idanunta waiko gizo suke mata, ganin dai cewa da gaske tabbas anyi la'asr ɗin ne ya sanyata shigewa cikin bethroom. Alwula ta ɗauro wasi wasi falllll ranta, ita data kwanta tun wajajen goman safe har ma taya akayi tayi wannan uban barcin.
Da haka tai tarin tunaninnika ta shimfiÉ—a darduma tana tayar da Sallah, takai raka'ar farko ummie data kuma zagawota wata iriyar ajiyar zuciya ta saki tana zama daga bakin gadon fatiman.
A nutse take yin sallar, kai yadda take sallar ma shi kansa abin burgewa ne. Bayan ta idar ne ta juyo a É—an sanyaye tana duban ummienta, Ahankali ummien ta janyo kan queen tare da azawa bisa saman cinyarta.

”FATEEMERH!”
Ummie ta ƙira sunanta a raunace, ”Na'am ummie Naaaaaa‘ ta amsa tana mayar da dukkan wata nutsuwa tata wurin ummien tare da ɗago kanta tana fuskantar ummien.Ummieh da ta kafeta da ido ko kyaftawa ba tayi.
Jin yadda jikinta ya ɗauki zafine yasa wasu kyallar tausayin fatiman kama ummieh, Saida ta sauƙe ajiyar zuciya kafin cikin ƙarfin hali ta fara irin ƴan nasihun da ta kanyi mata a ƴan kwanakin nan.
”Mamana har yanzu na kasa yadda da kin karɓi ƙaddarar da Ubangiji ya jarabceki da ita, kin kasa amsar ƙaddararki a yan da ta zo maki Fatima!, ya kamata ki farka komene zaki a cikin wannan duniyar to la shakka Aliyu shureim bazai taɓa dawowa gareki ba, gidan wani zakije Sammm zamanku bazai taɓa iyuwa a haka ba, Idan har kika ce haka zakici gaba da ire-iren waɗannan Abubuwan to tabbas rayuwar aurenki ba zaki taɓa jin daɗin sa!, ba zaki taɓa ɗanɗanar tarin ni'imomin dake cikin auren ba”

Saida ta É—an dagata kafin taci gaba da faÉ—in.
”Ni! Uwace Fatima kuma akwai zuciya a tsaƙiyar ƙirgina, taya kike tunanin zan iya samun nutsuwa kina a wannan yanayin?, mun zaunar dake mun tambayeki ko auren ne baki so amma kince a ahhhhh!, to shin wai a ina hasalin matsalar take?, ki tuna da ke kaɗai ce ƴa ɗaya tilo mace a gabanmu da Allah tamu yayyenki biyu maza ne kuma Ni ɗin dai nice abokiyar shawararki.
domin ban yarda ba ban lamunci ɗibar sirrikanki kina baiwa ƙawayen yanxu da ba amana suka sani ba, idan sirrinki ya wuce to kuwa sai ƴar uwar ki fareedatu. Kuma ina so wannan yazam shine maganganun ƙarshe dazan ƙara zama yi miki akan wannan auren.ki cirema ranki damuwar komi ki rungumi Sabuwa rayuwar dake daɗa kusanto kanta gareki, ki rungumi ƙaddararki da hannu bibbiyu a duk halin da tazo mana hakan shike bayyana kwarai kacika cikakken musulmi na kwarai, wanda Ubangijiin sammai bakwai yace ayi koyi da masu haƙuri da kuma masu rungumar ƙaddara da hannu bibbiyu a duk yacce tazo musu, Ubangijiin Rahama da kansa yace Ni! Kuma nayi ma wannan bawa nawa alƙawarin bisanya ƙaddarar sa daga mummuna zuwa kyakyawa!. Ba buƙatar naci gaba Fatima domin zan iya cewa indai a wannan fannin ne Sammm bana da haufi akan ki, ya kamata ki dawo cikin hayyacin ki!, hankalinki ya dawo jikinki, Ubangijii shiya amshi Ran Aliyu shi kuma ya ƙara baki wani ALIEYON! godiya ya kamata kiyi ma Ubangijin talikai.”

Wata iriyar ajiyar zuciya Fatima ta sauƙe tare da ƙanƙame ummienta ƙammmmm, jikinta ya shiga kerma da mukyarkyata. Hawayen da take riƙewa ne suka sami damar zubo mata cikin Muryar da taci kuka sosae ta fara magana.
Chapter 26 · 0% Book details