← Book details Ƙauna Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 56

Sashe 28

Ƙauna Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gani yake ko uwar data haifeta ba zata kaishi SO da kuma ƙaunarta ba, duk wasu tarin ƙaddarorin da suka gitta masa SO da kuma ƙaunarta nanan daram acikin Rai da kuma rushinsa.....

_A tunaninku wacce yarinya ce Alie ya ruyu da SOYAYYARTA a cikin rai da kuma rushinsa?_

*💘🌺ƘAUNA BIYU 🌺💘*

~Heart touching love, with love aside 🤍🤍~

Page 29&30

*BY*
*AMMEY LAYLERH ✍🏻♥️*

✯ *~🌠 OFFICIAL MIRRAH 💫~*

Sadaukar ga my official Ƴan Amana Naaaaaa mutanen Amana kuyi yadda kuke so da Wannan page, idan kun so ma ku yagalgala abinku nidai na baku kyautar sa🤗🤗🤗

@⁨~♥️ masoyiya⁩
@⁨Amina Muddes⁩
@⁨Aunty bee Naaaaaa⁩
@⁨Free Life With Bbyna❤️🔐💋⁩
@⁨Maman Hanna⁩
@⁨Zainabu Abu⁩
@⁨+Farida yahaya71

Ina ƙaunarku Ma people Naaaaaa 😘😚
_________________________

♥️🤍♥️

*AMMEY POV*

Tun tana ɗaukar lamarin abin wasa har hakan ya fara damunta , ga kuma rigimar Amnah akan lallai ita dole sai ankai ta gun papieyn ta. domin yanxu magana ake ta wajen 3 Months keñan.

Ga kuma wata sabuwar rigimar taga Hajjo, domin yau kwananta uku da xuwa gidan wai a hakan ma don batasan halin da suke ciki da alieyon bane. Shi kuwa Abba zuba musu Ido kawai yayi yaga iyaka gudun ruwansu. Don tunda abin ya faru yana sane amma yaja bakinsa yayi shiru, tunda ya gane jalala kawai alieyn ke nema hakan yasa shima ya share al'amurransu yaci gaba da harkokin sa, tamkar babu abinda ke damunsa.
Tun ummie na ganin hakan me sauƙi ne gashi yanxu hankalin yafi na kowa tashi. $auƙinta ɗaya ma da hajjo bata san asalin abinda yake faruwa ba, tasan da tuni ta tashi hankulan kowa dake cikin gida. Don hajjo irin masifaffun tsoffin nan ce ga kuma alieyn shine ɗan gaban goshinta, ganin tunda tazo babu aliey babu Irfan sosae tasha mitar ta wai suna ƴaƴan musulmai amma su sallamawa masu jajayen kunnuwa ƴaƴansu.
Kasancewar shi Irfan É—in Immigration ne, shi kuma aliey pilot.
So dama idan yanayin aikin ya sanja musu gashi dai suna gari ɗaya amma sukan sati fiye ma satin basu ganshi ba, saidai suji ta hanyar yin waya, wannan dalili yasa tunda hajjo tazo bata idon kowa daga jikokin nata ba, Wannan keñan.

Wata farar dattijuwa na hango zaune ko ince kishingiɗe saman sofa Idanunta lumshe hannunta riƙe da chasbahanta tana ja, kallo ɗaya zaka mata ka fashimci hutu ratsa ko ina ajikinta ga wani haske da Annauri dake fitowa daga saman kyakkyawanr fuskanta.

Shigowarsa keñan gidan ko bangaren mahaifiyarsa bai nufa ba, ya yi ɗakin daya san na grennyn sune.
Cike da É—okin son ganin ta ya faÉ—a É—akin cikin zumuÉ—i, Yana faÉ—in.

"Sweery Where are you?”

Shiru ta masa duk kuwa da cewar tana kallon sa, kafin ta ware large eyes nata wanda da dukkan alamu daga wurin ta aliey ya gada, zuba masa su tayi na Æ´an wasu sakanni kafin ta sake wani kayaceccen smile tana ware masa hannuwanta. Jikinta ya faÉ—a ita kuma ta shiga shafa samar sumar kansa

"OYOYO my na robar I miss you so much 😍 my yaron kirki ɗan albarka"

"Nima nayi missing ɗinkin hajjo na!, amma nifa gaskiya bana son kirana na robar da kike, nima kice min na ƙarfen kawai wannan shine magana uhummmm”.

Ummie ce ta shigo É—akin hannunta É—auke da lunch na yamma da takawo hajjo, Sammm bata yi tunanin ganin Irfan É—in ba tunda bata san da xuwan sa gidan ba.

“sannunki Fatsimatu Ubangijii dai ya biyaki wannan ɗawainiya da kike dani a gidan aljannatul Firdausi”

”Ameern”
Ammiey ta amsa tana gaida ta cike da girmamawa, da fara'arta take amsata.

Leƙen bayan Irfan ta shiga ganin shiru shiru babu aliey babu labarin sa, haƙuri ta gaza tace. ”Na robar wai ina na ƙarfen yake tun ɗazun se famar leƙar bayanka nake!, naga ta idda zai ɓullo”

Cike da mamakin jin hajjo na tambayar sa aliey yakai dubansa kan ammiey, kafin ya juwo da kallon sa kan hajjo. A take Brain nashi ta hasko masa wani abu. Duk irin yadda ammiey ta shiga ƙyaftama Irfan ido amma yai tamkar bai fashimta, har Saida ya zayyanema hajjo komai daya faru.

Domin shi nan a ganinsa ai hajjo zata iya hana auren kuma idan ta hana ya fasaya keñan har gaban abada,

”Innalillahi wa'inna ilair raji'un, yanxu Ni zaki munafurta fatsima?, duk kallon masoyiyar da nake miki ashe keɗin ba ƙaunata kike ba, tunda har zaku iya ɓoye min Alieyo ya faɗa”

Cikin son ammey ta kwantarma da hajjo hankali tace.
”pls don Allah hajjo ki tsaya kiji taya ma za'a ce me sunan manya faɗa yayi, kada fa ki manta shi pilot ne babu ƙasar da baya keta wa har inda bamu tunani shi yana ratsawa”

”yo ba dole nace an sace min mijina ba!, ki naji fa abinda Irfanu ya faɗa yace tun da ya ya tafi kowarsa ba'a samu, to Wllh zai haɗu dani.
Kuma aure ne babu fashi saidai ya mutu ƙarewar zuciya, ɗan me ƙaton kai da tsayi yawa daren mutuwa!, sai zuciya yawa ta kafuran farko, kai Irfanu zo nan zoka ƙiramin shi don uwatata”

Ɗan ɓata fuska Irfan ɗin yayi kafin yace ”haba Hajjo kina jin fa abinda nace miki sammmm woyarsa baya tafiya bara ma ki gani”

Yayi maganar tare da zaro wayar sa daga aljihun gaban rigarsa, tare da dialing na NO ALIEY yana sakata a handsfree.
Daga Irfan har Ammiey wani irin zaro Idanu suka yi waje ganin abin al' ajabin daya faru yanxu yanxu,

(NO na Aliey kuma ya shiga yau?)

Shine kaÉ—ai abinda suke faÉ—a acikin zuciyarsu.

___________★★★___________

Cenñnn ɓangaren ALIEY kuwa yana kwance tsakiyar lafiyayyan gadonsa yana barcin daya ɗan samu ya ɗauke sa, tamkar a mafarki haka yaji wayarsa na ringing.

”Ohhh my God!”
Shine kaÉ—ai abinda ya iya furtaw domin sammm yama manta ashe fa bayan ya gama wayar sa da Jay ya kotsa woyar nashi, kuma da yamman nan ya fita ya sai wata ya zuba sima siman sa, ya kuma manta shafff baiyi switch na wayoyin nashi ba. Wannan shine dalilin da ya sanya su Irfan samun sa.
Batare daya buɗe ido ba yasa hannu yana lalubar wayar da ƙyar ya iya ɗakko wayar don har ƙiran ta kusan yan kewa, da ƙyar ya iya ware lumsassun idonsa da barci ya fara cin ƙarfinsu.
Ba tare daya duba mai ƙiran ba yayi picking na call ɗin, tare da manna wayar da kunnensa yayi shiru yana jiran yaji wayo.

★★★

Wani irin kallo Hajjo ta shiga bin ammiey da kuma Irfan dashi, duk cikin su babu wanda ya Iya cewa ƙala, har sanda ta fusge wayar daga hannun Irfan. Tana faɗin ”ashe dama ku munafukai ne kuna son ku rabani da jikina don kunga ina son shi!, to Wllh ashir ɗin ku babu me rabani da Aliyu gadangana saidai mutuwa mutum yayi duk abinda zai yi.

A fusace kuma ta dawo da hankalinta kan wayar jin anyi pick call ɗin, tamkar a mafarki haka yaji sauƙar Muryar hajjo cikin hargowa.
”To wllh maza maza ka haɗo naka ya naka ka dawo gida, domin duk gudun ka da Wannan auren sai anyi shi babu fashi!, tunda a istiharar da nake maka kullum wannan auren ya gama bayyana min akwai tarin Alkhairuka a cikin sa, don haka babu fashi koda idan anyi zaka mutu!, to kuwa sai bayan an kai ma matar sannan saika mutun”

Shima a fusacen yace

"bazan dawo ba ɗin idan kuma kin isa sai kizo ki dawo dani naga ƙarfin ikon ki rikitatta kawai, ki fata a harkana fa ina haka ba Wllh zaki haɗu dank”

yana kai ƙarshen maganar batare daya jira amsar da hajjon zata bashi ba ya katse ƙiran, yayi wurgi da wayar yana jan tsaki tare da maida kansa yaci gaba da barci abinsa.

Wani uban salati hajjo taja tana fashewa da kuka.

”dama haka ɗan Adam yake ai tara yake bai cika goma ba, yanxun nan na gama faɗa da uwarka da ɗan uwanka amma abinda zaka saka min dashi kenan?, to Wllh bara ubanka yazo a yau ɗin nan saina saka shi ya dawo da kai, yo in banda lalacewa ma ace aure sauran shi baifi sati biyu ba, amma babu ango babu alamunsa dani kake zancen dan banza da faka faka kunnuwa irin na ƴaƴan masu jajayen kunnuwan cenñnn”

(Shi kuwa Irfan a cikin zuchiyar sa yake faÉ—in wlh yau Aliey da nine yayan ka da sai nayi maganin ka wallh)

Ammiey kuwa baiwar Allah ta mayi Shiru ta rasa abin cewa dan baga san mene zata ce ɗin ba, Saima tsintar kanta da tayi tana kunyar haɗa ido da hajjon. Sosae tayi ƙasa da kanta kafin cikin aro jarumta tare da tattare nutsuwar ta wuri guda ta furta.

”Don Allah Hajjo kiyi haƙuri wllh kusan kullum saimun ƙira me sunan manya amma sammmm woyarsa baya tafiya, ki tambayi abbansu ma kiji harda shima”

dafa kafaÉ—arta Hajjo tayi tana faÉ—in

”karki damu Fatsimatu nasan halin ki gaba ɗaya don haka kada ki damu da wulaƙancin da gadanga yamin, Ina zaune zai zo ya sameni a mazaunina. Ƙyaleshi ya gama guje gujensa aure dai na faɗa babu fashi, Ina nan kuma Bama zan koma har sai anyi wannan auren Insha Allah”

Ajiyar zuciya ammiey ta saki tana cewa ”Na goɗe hajjo Allah ya ƙara girma”

ita kuwa hajjo kallonta ta dawo kan Irfan tare da É—aure fuskarta wai kar shima ya e zai rainata kamar yadda yaji yayansa yayi.
Har wani hura hanci sama take kafin cikin izza fuskar nan babu wasa tace.
”Maza Abdul Malik ƙira min Muhammadu yanxu nan ka haɗani dashi”

Jiki a sanyaye Irfan ya amsa da ”toh” yana dialing NO na Abbansu.ring ɗaya Abba ya ɗaga wayar, yana faɗin
”A Malik lafiya dai naji ka haka, ko duk damuwar ALIEYN ne ya sanya hakan?”

”A ahhh Abba da dama dama Hajjo ce tace wai na ƙiraka mata kai”

”To! to bata wayar mana”

”toh Abba!”

Hajjo ya miƙama wayar tana amsa ko gaisuwar da yake kuma mata bata amsa ba cikin bada umarni tace.

”Muhammadu Nasiru!”

Cikin bada attention nashi baki ɗaya ya nutsu jin ta ƙirashi da cikakken sunan shi.

”Na'am Hajiya”

Wura hanci tayi sama tare da sake cewa

"shin na Isa dakai?, zan kuma baka umarni ka É—auka?"
Chapter 28 · 0% Book details