← Book details Ƙauna Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 56

Sashe 7

Ƙauna Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Assalamu alaikum ƴan uwa ina muku fatan Alkhairi, tare da Adda'ar zaɓin abinda shine mafi Alkhairun mu garemu. Tabbas dukkan ayyuka suna tabbata ne da niyya,kuma Lallai ko wanne mutum yana samun sakamako ne na abinda yayi niyya, Ubangijii Allah yaci gaba da zama gatanmu,rufin asirinmu, yaci gaba da haskaka dukkan al'amurranmu cikin amincinsa.
Ina taya ƴan uwa musulmai murnarn zagayowar Watan RAMADAN,wata mai cike da tarin falala, a sabo da murnarn wannan wata na RAMADAN mai tarin albarka, NI! AMMEY LAYLERH nace na sadaukar da littafin KAUNA BIYU daga paid zuwa free. Allah yaci gaba da zama gatan mara gata, yaci gaba da haskaka goben mara gata, mara galihu acikin al'ummar musulmi. Sannan littafin *ƘAUNA BIYU* na mai dashi Free inshallah duba da yadda al'amurra suka tare suka ma duniya ƙawanya, kowa yana naiman abinda zai rufama kansa asiri ne, dashi da iyalansa bissalam🙏🙏🙏.
Sannan pls waɗanɗa suka riga suka yi payment sumin magana, zan dawo musu da kudaden su pls karku barni da haƙkinku, kana kar kuji kunyan yimin magana. Wllh idan har baka min magana ba to kusani nikam nace ba gata kuka min ba😮‍💨.
Duk wanda yaji daɗin littafin yama mahaifina adda'a, domin ya kai ladan ƙabarinsa👏😭, Allah ya jiƙanka Abba Naaaaaa mahaifin da bana da kamarka acikin duniya😭🤲🤲
__________________________

♥️🤍♥️

Idanunsa ya lumshe da sake buɗewa su akan Amnah dake jingine da jikin Ammiey,tana mata rigima domin bata jin daɗi asthmar tane ya tashi. Shi yasa yau bata wani tashi da kuzarinta da karsashinta kamar kullum ba. Suna haɗa ido yaji wani irin raunin da ganinta ya sanya mishi, na ƙoƙarin taso mar, Amnah da ganin papieyn ta ya sanya ta a farin ciki ne ta taso ya gudu zuwa wurin sa, hannayen sa kawai ya buɗe mata domin ya san mine take shirin yi, tsamm ya rungume princess ɗin nashi zuciyarsa na masa wani mahaukacin bugu. "Papiey" ta ƙirayi sunan shi cikin maraitacciyar murya.wanda hakan ya sanya alieyo ɗago haɓarta ya zuba idanunsa, cikin muryan shirin yin kuka tace.
"Papiey new Mamie"
    Yanda tai maganar a hankali cikin rauni ne, yasa kaɗan ya rage zuciyarsa yin bindiga, amma ya daure cike da son nuna jarumta yana ƙara ƙanƙa meta sosea a cikin jikin sa.
Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, gaba ɗaya ji yake komai ya cinkushe masa. dole ne yana buƙatar ƙara ƙadaice kansa, domin gudun kada iyayen sa su fashimci rauni da kuma halin da yake ciki, zare ta yayi daga jikinsa samm baka isa kai tsaye ka fashimci halin da yake a ciki ba, amma a baɗani da zaka ga irin tarin raunikan dake chunkushe a cikin zuciyarsa, da kuwa tabbas saika tausaya masa. Upstairs nashi ya juya cikin domin zuwa yanzu wani irin azababben zafi da ciwo yaji zuciyarsa na masa.
Da kallo Irfan ya bishi yana ji inama ace ana iya ɗauke damuwar wani, da kuma ciwon wani,da shi kuwa tabbas shine zai ɗauke duk tarin abubuwan yayansa bama tare da shi kansa ya san da hakan ba. Idanunsa ne ya ciko da hawayen tausayin ɗan uwansa, yana duban iyayen nashi. Sosea ya fashimta halin da suke aciki suma kasancewar su masu saurin gano damuwowin kowannensu ta cikin idon kowannensu, haka shine dalilin da yasan shi fasa ƙaraso wa palon yin dinner da fito. Kukan Amnah ne yaja wo hankulansu baki ɗaya "duk loƙacin da zan yima PAPIEY Na maganan sabuwan momie kora ni yake a wurin sa!, ya tafi ya barni. Shi kenan ni bani da mamie kenan irin mamien su afnan!"
Da sauri Irfan ya rufe mata bakinta shima yana danne nashi bakin da ɗaya hannun sa domin kuka yana dab da subce masa ne. da sauri Abba ya miƙe a cin abincin da yake yana fita a gidan baki daya, rungume kanta yayi sosea yana tuna da Safiyya mahaifiyar ta, irin tsananin mutuncin ta, kara, kawaici, yafi kowa sanin irin baƙar wahalar data sha a hannun yayansa, bata taɓa barin laifin mijinta ya fita,taci ɓakar wuya sosea kafin taji daɗin zama dashi, domin aliey dama cennn wani irin murɗaɗɗen hali gare shi.
Cikin Amnah shine sanadiyyar sanja komae na zamantakewar aurensu.
Wani irin mahaukacin so yake mata wanda shi abin wani bin har mamaki abin ke basa, idan ya duba rayuwarsu ta baya da kuma yanzu.
Sau tari yasha raya kamar Allah ne ya jarabci yayan nasa da masifar son ta, sai kuma da yay zurfi ason nata Allah ya dauke rayuwar abar sa.sunyi kuka sunji ciwon mutuwar Safiyya domin macece da sammm bata san tashin hankali ba, sammm bata iya koda kwatankwacin hakan ba, kai duk mahalukin daya haÉ—a zaman takewa da Safiyya dole ta shiga ransa farat É—aya. Innalillahi ya shiga nanata acikin zuciyarsa domin mutuwar safiyan ba kaÉ—an ba ta daki duk ahalin nasu.
Yana son yin magana amma ya gaza, ammiey ce tayi ƙoƙarin zare ta daga jikin Irfan ɗin, tana yin bedroom nata da ita.

★★★

Akan kyakkyawan madaidaicin frame ɗin ta ganin sa ya sauƙa, cikin tariyar sassarfa ya isa wurin photon rinannun idonsa da baki ɗaya suka gama rinewa ya zubawa photon, wani irin zazzafan Numfashi ya fesar tare da kifa kansa jikin ginin ɗakin, cikin azazzaben mikin dake taso masa na rashin matar nashi, ya ce.
"Why? Me ya sa!, me ya sa, me yasa kika tafi kika barni,Why does death do this to me? Why does it come to cut our love?, whyyyyy" yayi maganar wani irin hawaye na saƙko mishi.

Tamkar wanda aka zabura ya mike a zabure, kalamanta ne suka shiga dawo masa cikin brain nashi.
"Alfarma ɗaya zan nema a gareka Lovie kada ka taɓa zubar min da hawaye yayin daka tuna dani acikin zuciyarka ABU FATEEMERH!, wannan shine babban gatan da zaka min". Sune kalaman ƙarshe daga gareta, itace maganar data zama kalmar ƙarshe ɗaya ji daga gare ta.

Toilet ya faɗa yana sakar ma kansa ruwa, yana fatan abinda yake ji a chunkushe a kirjin sa ya ragu ko da kankani ne, sai dai baya jin akwai wani abu da zai rage masa yadda yake ji ɗin ko da kuwa kaso ɗaya ne cikin ɗari na abinda ya danne dukkan wani tarin farin cikin nashi, wanda yake jin ba zai taɓa dawowa daidai ba. Ganin tamkar kamar ma ƙara tunkuɗo masa abubuwan ake ne ya sanya shi nufar gyms nashi.
Da sauri-sauri yake motsa jikin duk ya hada gumi sosai, be tsaya ba sai da yaji ya gaji sosai sannan ya tsaya,wani irin bazaraten mutum ne buɗaɗɗe da baka gane hakan kai tsaye, idan har baya cikin riga. Cikin zafi-zafin da ke nuna ba'a haiyacinsa yake ba yake sarrafa machine ɗin, idanunsa a rufe ruf ya kwashe tsawon loƙaci yanayi dan sai da yay sharkaf da zufa kafin ya kashe ya koma wajen ɗaga ƙananun ƙarafe, irin na riƙewa a hannun nan ko kana daga zaune zaka ɗaga, Nan ma ya ɗebi loƙaci yana yi kafin ya ajje ya koma ɗaga ainahin ƙarfe daga kwance rigingine. Haka ya ɗin ga ringa motsi jikin tamkar baya a hayyacin sa, Saida ya kwashi wasu lokutai kafin ya kashe komai.
goran ruwa ya ɗauko yana kwankwaɗe a take ya shiga sauƙe ajiyar zuciya mai karfin gaske.
Bethroom nashi ya ƙara koma wa yana sakarma kansa ruwa, haka ya shiga ambaton sunayen Allah duk wanda yazo kan harshen sa. Directly masjid ya nufa, shine bai dawo gidan ba sai wajajen goman dare, samm yaƙi aminta ya haɗu da koda mutam ɗaya ne daga cikin ahalinsa. Cikin Sa'a kuma loƙacin da yake dawowar babu kowa a palon haka ya shige bangaren sa.

LKY SPORT PYJAMAS ya sanya tare da amless irin mara hannun Nan, luntsumeme gadonsa ya haye tare da adda'oin kwanciya barci, idanunsa a lumshe kansa a sama haka komai tiryan-tiryan na rayuwarsa da suka daÉ—e da zama shuÉ—aÉ—É—u suka ci gaba da bijiro masa.

★★★
★ ★★
Chapter 7 · 0% Book details