← Book details Ƙauna Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 56

Sashe 17

Ƙauna Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A girmame aunty zeey ta shiga gaida ummie cikin farin ciki ummie ke amsata tare da amsan julaibeeb tana masa wasa har dare suna nan amma abin mamaki loƙacin da dasu yaya jay zasu tafi ƙin binsu tayi tace ita yau da ummienta zata kwana.
Tafiya suka yi akan gobe Insha Allah ya dawo ha É—auke ta, da haka suka bar gidan. Bayan anyi sallar isha'i babu jimawa da tafiyar su yaya jay Abba ya shigo, shima sosae yaji daÉ—in ganin fatiman. Cikin nutsuwar daya zame mata jiki ta gaida Abban nata. Kwanciya tayi akan kujerar parlourn. Ummie ce ya haÉ—a ma Abba dinner É—an kallon inda fatiman ke kwance yayi tare da faÉ—in.

"Ina tausayin yarinyar nan wallahi."
Abba ya faÉ—a cikin raunin murya
"Adda'a zamuyi mata."
Mama ta faÉ—a a sanyaye itama tana duban sashen da fatiman ke kwance
”insha Allah zamu ci gaba da mata addu'ar kamar kullum “
Ya faÉ—a a sanyaye ya shiga cin abincin duk kuwa da ba wani dadin cin yake ba sakamakon karya zuciyarsa da Fatima da ganin fatiman ya haifar masa.

"Allah yayi miki albarka, Allah ya taimake ki, ya kare ki da kariyar sa."
"Amin Abba Naaaaaa."
Ta amsa hawaye na taruwa a idon ta, ”Ina fatan a duk yanayin da kika tsinci kanki ki zama me haƙuri da juriya da amsan ƙaddarar data zo miki a irin ko wanne loƙaci Fatiman Abba kinji,ki amshi ƙaddarar rashin Aliyu domin kada ki butulcewa Ubangijii, shine ya fimu sanin abinda ke ɓoye, Ubangijii ya Miki zaɓin miji na gari!”

Wannan karon ummie ce ta amsa da ameern ɗin. Sun jima a parlourn kafin Abba ya miƙe yana barin parlourn, ummien kuma kai tsaye ta nufi inda Fatima ke kwance inda bacci ya dauke ta akan doguwar kujera, Ahankali ta shiga gashinta tare da adda'oi a bakinta, gudun kada ta farka a firgice, da salati ta farka cikin tsananin jin daɗi ummie ta miƙar da ita tana nufar ɗakinta da ita, sosae ta tofe ta da adda'oin kwanciyar barci kafin ta bar ɗakin bayan ta sakar mata net.
Washe gari alhamdulillah ta tashi da ɗan kuzari, domin itane ma ta shiga kitchen ta haɗa musu kayan karin kumallo. Gefe guda ta ɗebi markaɗaɗɗiyar gyada bayan ta dameta da ruwa ta tace abarta ta ɗora tukunya wuta ya tafasa lafiyayyan kunun gyaɗar ta. Saidai ya ɗan tafasa sosea kafin sauke ƙasa tana kawo hasararta ta ɗaure dashi, tare da matsa lemun tsami guda biyu a ciki. Take kunun ya tubke yayi kauri iyakar yadda take buƙatar shan abunta, sugar ta zuba sama sama domin Samm kunun markaɗaɗɗiyar gyada idan sugar ya masa yawa garɗinsa baya fita yadda ya kamata. Wanke kayan da duk tasan tayi amfani dasu tayi, kafin ta jere musu lafiyayyan yamballs ɗin data musu wanda yaji uban kwai na bala'i. Samm shi yasa ummie bata son Fatima tace zata musu Indai abinda ya danganci suya ne, domin ba ƙaramin ɓarnar ƙwai take mata ba.
( LoL 🤗 wllh ina bayanki ƴar gidana musamman da kike son duk kalan abinci kan dana fi so Nima 😋 ehhhhhhhhh mana My Delicious baaaa ♥️ )

★★★★
***********
*ALIEYO*

Misalin _12:15pm_ flight nashi yay landing na passengers a babban airport na ~Muhammed V International airport Casablanca ƙasar Morocco~

cike da takun nan nasa na izza da ƙasaita tamkar mai tafiya a saman iska tsabar yanda yake wani ɗaga ƙafafun da sauke su a nutse. Fuskar nan samm babu alamar yama san minene yaran murmushi, haka ya shiga saƙƙowa daga upstairs na jirgin a nutse.
        Sautin takun sawayensa da ke shelanta ma passengers nashi isowarsa wajen ne yaja hankalun mafi yawan jama'ar dake kewaye da airport ɗin. Ɗan fesar da numfashi yayi loƙacin daya ji rurin woyarsa, hannunsa na dama ya cure guri guda yana harbin iska, kafin cike da ɗan ɓacin rai ya zaro wayar daga cikin aljihun sa yana picking call in.
”You will be booked hotel Sir.” abinda aka faɗa kenen daga cikin wayar, a fusace ya mayar masa da amsa a zafafe yace. ”dake garin na uba nane ba!”
ring na Daimond dake maƙale da yatsarsa ya ɗan shiga murzawa a zafafe, yana jin wani irin ciwo ciwon kai na taso mishi. Directly cikin jirgin ya koma. Abinci bai dameshi ba Sam sam, rabon dayaci abinci tun lunch na safe da yayi sai coffee da yake yawan sha akai akai.Kwantar da kanshi ya yi a jikin ɗaya daga cikin kujerun jirgin yana lumshe rinannun idanuwanshi da suka kaɗa sosae a tashin farko.
*Kewa*
Wata iriyar kewa yake ji lokaci É—aya yanayin sa ya nemi birkicewa, sabi da wani irin azababben kewar Sofeeynshi daya tuso shi farat É—aya. Sunayen Allah ya shiga ambata cikin ransa. Ahankali komai ke dayake ji ke raguwa a nutse ya tashi akan kujerar yana nufar VIP na jikin jirgin,zaune yakai kan kujeranshi mai juya wa, yana jan É—an madaidaicin plask tare da tsiyanyar coffee a mug Ahankali yake yake sipping coffee É—in dake left hand nashi yana latsa laptop da right hand nashi dake kan É—an madaidaicin sterm din dake gabanshi.
yanda gaba ɗaya ya tattara hankalinsa ga screen ɗin laptop ɗin zai baka tabbacin abu mai matukar muhimmanci yake yi. Dan sai loƙaci-loƙaci ya kan ɗan ɗauka mug ɗin ya kai bakinsa ya maida ya ajje mug ɗin, hankalinsa kacokam na kan abinda yake yin. Cikin deep saund idanunsa lumshe bayan ya kammala shan coffeen
Ahankali ya shiga motsa lips nashi.cikin daddaɗar muryansa ya fara fitar da wani colorn waƙa irin my sanyin nan a ƙalla ya ɗauki lokuta masu ɗan tsayi daga yadda yake in. Kafin wani irin wahalallen barci ya ɗauke shi anan cikin jirgin. Domin samm yau ɗin kwata² baya da buqatar zuwa hotel don abin ya fara sire mishi. Alerm clock ɗin daya seta wayar da asubahi ne ya farkar dashi. A wahalle ya shiga motsa lips nashi alamun yana addu'ar tashi daga barci ne. Kafin ya fara ƙoƙarin ware lumsassun idanunsa s wahalce.

A gimtse 🫰🫰🫰 🤗 fan's

Nagaji haka nan nima😔

*BY AMMEY LAYLERH ✍️*

08104493215

*💘🌺ƘAUNA BIYU 🌺💘*

~Heart touching love, with love a side 🤍🤍~

Page 19&20

*BY*
*AMMEY LAYLERH*

✯ *~🌠 OFFICIAL MIRRAH 💫~*

@Alhamdulillah forever and always 👏

______________________________

♥️🤍♥️

Ahankali ya shiga buɗe sleeping eyes nashi da sukayi masa nauyi kana kuma suka ƙanƙance, dishi dishin da yake gani acikin su ne ya sashi maida idanun nasa ya rufe, sosai yaji kansa na wani irin bala'in sara masa, dan haka yakejin gaba ɗaya jikinsa yayi weak ga kuma wani irin fitinannen kasala haɗi da ciwon kan da suka sauƙar mishi loƙaci guda.
Hannu yasa yana ɗan dafe kansa dake yi masa ciwo kaman zai rabe biyu,still rinannun idanunsa dake a lumshe ya buɗe tare da sauƙe ganinsa cikin jirgin.
Ahankali ya ɗan motsa jikinsa tare da soma ƙoƙarin ɗaga kansa da yakejin yayi masa nauyi sosai, wanda kuma yasan hakan bai rasa na saba da kewa da kuma tsananin tunanin Sofeeynshi daya kusan kwana yiba.
jingina bayansa da jikin kujerar yayi tare da sakin ajiyar zuciya yana miƙewa da ƙyar tare da nufar bathroom ɗin dake cikin jirgin. Shower ya sakamar kansa tare da tokare hannuwansa da jikin qofar wurin, haka ruwan shower'n ya shiga dukan jiki da kuma kansa.jin numfashinsa na neman ɗaukewa ne ya sanya shi janye jikinsa da ƙyar. idanunsa jajur alamar har yanxu komai nanan daram a yadda yake jin komai ɗin.
bathrube ya saka ma jikinsa ya nufi wurin bag da kayansa ke ciki,sauri sauri ya shiga shirya kansa cikin wasu fararen kaya irin na matuƙan jirgin nan, p.cap ya ɗauka ya saka a saman sumar kansa sosai yayi wani irin azababben ƙyau baka ganin komai sai jajayen laɓɓansa wanda suke fidda wani irin shining na tsantsar ƙyau.
walking slowly yake tafiya fuskar nan babu walwala samm ko kaɗan a saman kyakkyawar fuskarshi, pray made ya shimfiɗa tare da fara nafilfulin daya kanyi wasu luƙatan, bayan ya idar da nafilfulin yayi sallar subhi. 7:15am daidai ya shiga saƙƙowa daga cikin jirgin, wanda zuwa loƙacin tuni passengers da yake da wanda zai ɗauke su daga nan xuwa Dubai har sun fara hallara. Kai tsaye wani haɗaɗɗen eatery ya nufa cikin tafiyar nasa mai kama da ƙasaita. Ko mint 1 baiyi da zama ba wata baturiya tazo dab dashi cikin harshen English take tambayar sa mi yake buƙata, cikin kamewa da kuma basarwa ya amshi ɗan madaidaicin littafin dake hannun ta yam potatoe sai kuma coffee kawai yayi oder domin kafff cikin abinsu iyaka abinda yake iya ci keñan.
Sai kuma pizza dominos in banda su babu abinda yake iya ci daga sauran jagwalgwalonsu. Cikin 3mint wannan baturiyar ta kuma dawowa tana ajje masa abinda ya buƙata ɗin, cikin tsentseni da danne zuciyarsa ya shiga tsaƙurar abincin da spoon. Ko halp baici ba ya ture train tare da ɗaukan coffee ɗin, duk uban turirin da yake haka ya shiga sipping nashi cikin kwanciyar hankali, Atm nashi ya bada suka chaji kuɗinsu kafin su bashi yayi gaba.
10:15am jirgin su yayi landing daga ƙasar Morocco zuwa Dubai.

********
*Queen teemah*

Tunda ta idar da sallar subhi ta gaza koda motsa wa,wasu irin zafafan hawaye ne kawai ke faman zirya saman kyakkyawar fuskarta. Ahankali ummie ta zauna dab da ita cikin tausayawa domin tasan wannan hawayen baya rasa nasaba da Aliyu shureim wanda shidai tashi ta riga tazo ƙarshe, Cikin tausasa harshe ummie tace.
”haba Fatima ashe har yanzu ba zaki ɗauki dangana ba!, ashe zaki zama mai jayayya da mahaliccinmu!?, ya kamata zuwa yanxu ace komai ya wuce acikin zuciyarki. Yanzu ba loƙacin kuka bane Fatima! ninasani zaki samu wani wanda zaifi Aliyu tsananin ƙaunar ki, ki tabbata soyayyarki da Aliyu shine ƙaddararki, rabuwa dashi shine jarabarki. Insha Allah Ubangijii zai baki miji wanda yafi Aliyu shureim zama Alkhairinki.”
Chapter 17 · 0% Book details