← Book details Ƙauna Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 56

Sashe 4

Ƙauna Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amma fa ya qara zama miskilan masifa, Tun daga wannan rana ya soke komi da komae idan nace komae ina nufin komae ɗin kuwa na cikin rayuwarsa, inda ya qara zama wani irin miskilin masifa wanda dama cenñnn haka Allah yayi sa da tsabar miskilancin tsiya, sai ga wannan al'amari kuma sune suka taru suka qarasa zame masa jinin jiki.
Wata iriyar soyayya ALIEY yake nuna ma Amnah,wani irin gata yake bata na gaban kwatance,duk wata tarin soyayyar mahaifiyarta ya tattare ta duka ya dawo kanta. Inda yaga duk duniya babu macen da zai iya aura bayan Sofeeynshi, domin ya tabbata babu macen da zata taɓa kaiwa matsayin Sofeeynshi acikin duniyar, Sofeey mutum ce mai tsananin biyayya da bin tsarin dokokin sa, tana tsananin ƙaunar ganin farin cikin sa duk da kuwa cewar shi ɗin mutum ne mai murɗaɗɗen hali da azabar zurfin ciki.
Haka su ammiey da abbansa suna ji suna gani, ayaqi zaman nigeria dama kuma gashi PILOT, haka ammeynsa da mahaifinsa Suke ci gaba da binsa da addu'a da kuma fatan Allah ya kawo qarshen komai.
Wannan shine takaitaccen tarihin ALIEY A takaice.

(Miskilanchi
Idan aka ce mutum miskili ana nufin mutum mara sakin fuska. Mara surutu da yawan magana mutum mai aji wanda baya son raini mutumin da ba kowa yake kulawa ba.

Miskilanchi halitta ce ba girman kai bane wasu mutanen haka Allah yake yinsu.)

"Ya Allah" ammiey ta ambata sakamakon mutuwar safiyan da takejin ta dawo mata sabuwa fil, tamkar yanxu ne mutuwar.

Ita kanta batasan loqutan data ɓata a inda take zaune Amnah kwance a jikinta, sai ajiyar zuciya da take ɗan saki lokaci zuwa lokaci kaɗan. Qiran sallar magrib ta taji ana qira ne ya sanya ta miqewa tare da Amnah, direct bedroom nata ta wuce da ita bathroom ta wuce ita kuma cike da sanyin jiki ta ɗauro alwula tare da gabatar da sallah, ko ta kan dinner bata bi ba tana Nan zaune tana azkar har loqacin isha'i yayi, Nan ma ta gabatar da sallar.
Sai wajajen tara ta miqe tana nufar Amnah domin tashin ta tayi sallah.
Slowly ta shiga tashin ta tare da ambatar sunanta.

"Amnah! Amnah!!takwarana !!!"

Ahankali ta shiga É—an bude ido cike da magajin barci tace.
"Papiey na ashe dama da gaske kake zaka zo yau É—in"
Da wani irin kallon tausayi ammiey ta bita dashi, tana jin zuciyarta na qara raunana akan tausayin Amnan. "Cwty ki farka ammiey ce ba papieyn ki bane!" ÆŠan kucul bakinta ta turo. "To ki ce papiey na ya dawo gida don Allah ammiey na haka nan na gaji da kallon uncle Irfan kullum" tayi maganar cikin Æ´ar maganar ta me sanyi. domin sosea tayi missing na mahaifin nata. Sanin surutun Amnah ne ya sanya ammiey daukar ta kawai tana shigewa bathroom da ita wanka ta mata, kana ta sanya ta daura alwula kafin suka fito. Saida tayi sallar magrib da isha'i kana ammiey taja hannunta zuwa main Parlour, tamkar yadda ammien ta tsammata kuwa Irfan na zaune saman sopa laptop daure a cinyarsa yana faman sarrafa ta.

Zare hannunta daga cikin na ammiey tayi, da gudu tayi kan Irfan kai tsaye jikinsa ta faÉ—a cike da farin ciki,"barka da dare uncle" kanta yadan shafa tare yana faÉ—in. "Bakiy bacci ba baby?" Kanta ya É—aga mishi.
"Oya taso kiyi dinner kibar uncle yan aiki ne"
Babu yacce ta iya dole haka ta nufi ammien, don cika umarninta.

★★★
★★
★★★
*ALIEY*
2:20 na dare jirgin su yasauƙa 9j a garin Kano,wani irin numfashi ya fesar me ɗan zafi, loqacin daya fara taka step na mata kalar benen a tsanake. Cikin wani irin zallar izzar da yake da yaci gaba da saqqo wa zuwa babbar harabar airport ɗin.
bodyguard nashi biye da shi wayarshi ya amsa daga hannun É—aya daga cikin guards nashi, dialog nashi ya shiga kai tsaye domin qiran Irfan ganin har yanxun baizo airport É—in ba,bayan kuma tun kusan 40 minutes da qiransa ya shaida masa sauqarsa. Ji yay kawai an rungumo shi ta baya tare da cewa "Welcome back my cousin" Saida ya mola dan kansa kafin yace,"Welcome"

Directly wurin daya Parker motornsa suka suna,yana barin guards nashi a Nan kasancewar ruwan sane yawo dasu, ruwansa tafiya babu su. Cikin qanqanin loƙaci suka isa qayatacciyar anguwar SHARAƊA PHASE 01

A tamfatsesen
★ALIEY MAI MATA ESTATE★ motarsu ya Parker ko hong aliey bai bari Irfan yayi ba domin bayasan hayaniyar kowa a yanxun. Yana buqatar ya kaɗaice kansa shi qaɗai, Directly part nashi ya nufa
Hankali kwance cikin nutsuwa da zallar miskilancin haɗi da tsananin zafin nama yake tunkarar ƙaton ploorn nashi.
"ya ilahi" na faÉ—a loqacin da hancina ya shaqo min wani irin azababben qamshim wanda ya riga da ya gama kama É—akin, parlour ne haÉ—aÉ—É—e domin iya haÉ—uwa kam ya haÉ—u komi na palon ya kasance Milk and coffee colour ne.
Paulour ne mae tsananin girman gaske wanda yake ɗauke da da ɓangarori daban-daban, ko wanne ɓangare da irin qawatuwar da yake da kana idan mutum yana tafiya, yana kallon kansa da kansa ne ta cikin glass mirror ɗin da gaba ɗaya shine ya kasance a matsayin gini, wanda shi kuma na ciki kai tsaye yake sanin wanda yake tafen, shi kuma mai tunkarar ɗakin iyaka kansa da kansa kawai yake iya kalla.

***Kadaran kada han ya nufi upstairs nashi.
Tun kamin yakai ga qofar shiga ploorn qofar glasses mirrorn ta fara wani irin rubuta da red and blue colors, inda take rubuta ~welcome back ALIEYO MAI TAMA~
da wani irin style gwanin burgewa ga ba'abocin kallo.
Tattausan Tafin hannun sa ya kifa saman É—an zagayayyen glasses,kana cikin sillent voice nashi yace.

"I answered"

Zuuuuu glasses in yayi sama baki ɗayansa, subhanallah shine kawai abinda baƙina ya iya furta wa, domin wani irin mahaukacin ploor ne wanda yaci uwar na farkon haduwa da komi da komai, gaba ɗaya ploorn an ƙawatashi da wasu Italian fashion rug farare masu masifar ƙawatuwa da burgewa, ɓangare gudan bangon ɗakin gaba ɗaya anshafe shi da plasma wanda idan har ba sani mutum yayi ba, bazai taɓa cewa plasma bace loqaci guda.
Daga ɗayan gefen kuma wani irin haɗaɗɗan dining area ne inda aka masa adon ƙoyaye masu ɗan girma inda suka ɗan sakko qasa kaɗan da dining ɗin, ɗaya ɓangaren kuwa wani irin azababben beni ne wanda yayi wani irin lankwasa, wanda kai tsaye zai sada mutum da bedroom ɗin hasalin ɗakin kenan, gefe kaɗan da wurin kuma an ajje wani ƙaton dum lightning shima domin bada haske kaɗan, wanda idan ma'abocin wurin baison haske yakan sanja hasken ya zuwa dum light kamar dai da night kenan.wani makeken qaton photone manne da ɓangaren dama wanda wata farar mata mai kama da balarabiya ke jikin photon inda aka rubuta ~SOFIYYA MRS ALIEYO~
da wani irin style akayi rubutun, inda gefen photon kuma again wani photon ne dai amma wannan mutane biyu ne sakamakon wancen da take ita É—aya. Yana tsaye ita kuma ta É—aura kanta saman É—amtsen hannunsa,da É—an matashin cikin ta daya gama fitowa chass dashi kyakkyawar fuskarta qawace da murmushi, irin ta daga kan nan nata sama tana kallon innocent pace na mijinta.
wanda dukkan alamu suka gama baiyana cewa a qasashen waje ne aka É—auka photon domin baiyi kama da 9j
A kallon farko mutum yakan iya bama wannan ploor suna da aljannar duniya, domin iya tsaruwa ploorn ya tsaru matuqa.
Kai tsaye aliey yake taka mata kalar benen cikin sassarfa, babban burin sa a yanxun bai fice ace yaji shi cikin ruwa masu É—umi ba kana ya ganshi yana barci domin hutawa.

yana sanya kansa cikin hasalin bedroom nashi kuwa da wani irin haɗɗaɗɗe lafiyayyan gado naci karo, daga saman gadon kuwa wata haɗaɗɗiyar benc Centre ce mai lokoki wanda samanta akayi wasu qananun sink guda biyu a wurin, sai kuma tsakiyarsu akayi adon wata madaidaiciyar fulawa, ɗaya gefen bedside drawer ɗin kuma wani ƙaton Electric kindle ne, mai bama ɗakin ɗan qaramin haske da night shima irin wanda yake sassanja colors Innan.

Cikin muryarsa wacce ta zama slocoly loqaci guda ya furta "ALHAMDULILLAH" yana jin wata iriyar nutsuwa na sauƙar masa ta Musamman, tare da sanya hannunsa yana shafa lallausan sajen dake kwance akan kyakkyawar fuskarshi.
Sau cikin qafarsa ya shiga zarewa tare da fara ɓalle maɓallan gaban rigarsa, tare da zare dogon wandon trouser shima ya rage daga shi sai boxes da farar vest, direct toilet yawuce ruwa masu ɗumin gaske ya haɗama kansa tare da zuba tularen wanka acikinsa. Iumsassun idanunsa da akoda yaushe suke a lumshe ya kuma lumshe wa, jinsa cikin ruwan ɗumin gaba ɗaya ɗumi da kuma ƙamshim ruwan, suka taru suka kuma sanya mashi wata iriyar nutsuwa.

After 30 mint ya fito yana ƙamshim shower gel, ɗaure da farin towel ya fito fari tasss ,sai uban ƙamshi yake zubawa. clothes nashi yashige ya shiryo cikin tree kwata da riga armles ruwan sararin samaniya, mara hannu a tsanake ya zirah jallabiya, a saman kayan.
dadduma yaÉ—auko yashimfiÉ—a yatada sallar nifilfulun sa duk kuwa da cewar tsakiyar dare ne amma haka ya gabatar
Sallolinsa cikin nutsuwa, bayan ya idar da nafilfulin ne ya janyo drower na littattafan sa, Alqur'ani ya ɗauko *SURATUL MARYAM* ya fara karantawa cikin ƙyaƙyƙyawar ƙira'arsa, da zakin murya tamkar Sheikh sudues yake rairawa,bayan yagama karatun nashi...
Tare da bin addaoin da yakan yima Safiyyansa bayan ko wacce sallah, sai wajajen qarfe huÉ—un dare kana ya a tashi a wurin yana faÉ—awa saman haÉ—aÉ—É—en austra bed nashi.

Alarm clock É—in dake manne saman gadon ne ya farkar dashi, agajiye ya shiga ware gajiyayyun idonsa wanda samm barcin ba wani isar shi yayi ba, kansa har wani É—an ciwo ciwo yake masa.
Hakan ya sanya a nan cikin É—akin ya gabatar da sallar asuba nashi, yau ko azkar bai tsaya yiba ya kuma hayewa saman gadon sa tuni wani barcin ya kuma yin awon gaba dashi.

10: 5am
Chapter 4 · 0% Book details