← Book details Ƙauna Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 56

Sashe 22

Ƙauna Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ƙarar takun tafiyar da kaɗai baki sai kuma mayen ƙamshim sa na tabbatar da shine. (MUGU) Na faɗa acikin zuciyata tare da murguɗa baki a bayyane.
Zama yayi akan ɗaya daga cikin Royal sopar da suka ma parlourn ƙawanya, yana harɗe qafafunsa tamkar irin gawurtaccen sarki nan, tare da Lumshe idanunshi yana taune gefin lips enshi kaɗan. combat jeans black haɗe da black t-shirt ne a jikin sa, sosae kayan suka amshi jikinsa, tsantsar asalin kyawun sa ya bayyana acikin wannan kayan, wayarsa ƙirar Samsung Galaxy S22 ultra. yake ta aikin latsawa. ɗaya daga cikin glass cup ɗin dake jere a gaban sa ya ɗauka, tare da tsiyanyar kunun gyaɗar shi kana yakai bakinsa, a hankali yake shan kunun yayinda idanunsa ke alumshe.
Fitowar ammiey ne ya sanya Ni sakin ajiyar zuciya a ɓoye, zama tayi tana Fuskan tana da tare da Amnah dake barci a jikina. "Ohhh Amnah iyayen rikici keñan an samu tayi barci?, rikicin tafiyarki yazo mana da sauƙi ai kuwa kinga!" Ammiey tayi maganar tana fito da wayar ta, "hello Irfan idan kana kusa ina son ganin ka yanxu" banji abin da aka ce daga ɓangaren mai wayar ba, "Okk" shine kaɗai abinda naji tace tare da yanke ƙiran. Juwo tayi fuskarnan a haɗe ta fuskanci aliey cikin bada umarni ta jefa mishi car key nata.
”ka miƙa min Fateemerh gida dare na shirin yi” cike da bada umarni domin tafi kowa sanin halin abunta, yanxu yana tsinkata .
Sammm baraka taɓa gano ainihin abinda ke cikin zuciyarsa ba domin dai fuskar na'a yadda kuka santa,tsamm ya miƙe yana barin parlourn sai wani shan ƙamshi yake. Idan nace muku hantar cikin kanta Saida tayi rawa karkuce karya ne, amma haka na maze ban nuna ko ɗar ba, haka za kuma yanayi na bai sanja ba ko kaɗan. Aƙalla ya kwashi sama da 30mint nihar ma na fidda rai da fitowar san. Mukaji sautin fitowar sa.

Daidai kanmu ya tsaya fuska haɗe a daƙile ya furta "Let's go" sarai na jishi amma nayi tamkar ban jishi ba. Yana tsaye a kan mu tamkar irin sojojin Nan, kodan dama yafi kama da sojawa (wllh dama wannan me kama da samudawan farkon da sojan kaɗai ya dace bawai pilot ba) na faɗa acen kicin zuciyana. Ammiey tana amsar amnah dake bacci a jikina ta kuwa ƙanƙameni, tare da sakin kuka cikin magagin barci "ina ne zaki tafi ki barni new Mamie" tana ɗan turo mucilon bakinta gaba.
Abu kamar wasa saiga ƙaramar magana ta zama babba, domin sam Amnah taƙi zuwa wurin ammiey tace saita bini. Tun ammiey na aikin lallami harta gaji ta kyale ta.
Shi kuwa boss ln kota kanmu bai kuma bi ba yayi waje abinsa.
numfashi ammiey ta sauƙe ahankali tama rasa miye zatace ma, "to kawai inaga kuje ALIEYO ya dawo da ita inaga hakan shine kaɗai mafitanmu a yanxu."
"shikenan Ammiey babu damuwa hakan ma yayi" shi kuwa boss ln muna fitowa coumpaund na gidan idonsa a kaina, cikin halin nan nashi na ko in kula ya dauƙe kansa a kaina, tare da maida wa kan ammiey. "What wrong?ammiey" kanta ta kauda gefe tare da cewa "nice nace su tafi kawai"
Cikin ràshin gamsuwa da hukuncin ammieyn fuska haɗe yace "why Ammiey?, akan wane dalili?"
"He doesn't show any control over your daughter ALIEYO" tana faɗar hakan ta koma ciki bayan ta ɗamka min wata ƙatuwar leda irin ta shopping mall ɗin nan. boyayyiyar ajiyar zuciya na saki gami da daidaita zamana, zuciyana cike da Jin zafin kalamansa a kaina.
Haka yaja motar , A tsakiyar harabar gidan mu yayi parking. Yaƙi bude min kuma yayi shiru abinsa saima latse latsen da yake faman yi a wayarsa.

hannu nasa da nufin buɗe motar na fita sai naji a rufe take, hakan yasa na juyo kaina na kalli inda yake, sai naga kansa kife yake ruff akan shegiyar wayarsa. Ganin idan zamu shekara a hakan ba buɗe min zaiyi ba hakan yasa na ajje rashin kirkina gefe nace ya buɗe min. Da farko nasha bai jini bane, ina ƙoƙarin yin wota maganar naga ya buɗe min in. Ahankali gudun kada Amnah ta tashi dake barci na kwantar ta kusa dashi. Da ɗan sauri na na juya zan fita a motar naji an riƙo hannu na, da sauri na juyo Amnah ce na gani riƙe da hannun nawa.
Ɗan ranƙofowa nayi gareta sosai Nima ina kama hannuwanta duka biyun. kanta na ɗago dake zubda hawaye,goshina na manna kan nata. Sosae ta saki kuka tana faɗin wai baxan fita ba. hannu nasa bisa fuskarta kana nasa ƴar yatsa na ma nuniya Ina share mata hawayen cike da lallashi.

ita kuwa Amnah har yanzu hawaye da kukanta take famar yi.
A hankali ya buɗi baki murya cen ƙasan maƙoshi tamkar maiyin raɗa ya furta "Shiiiiiiiiiiiiiii AMNEEE!, bana son ganin wannan hawayen naki"
sai ya kuma rangwafowa kansa kaɗan kana ya lumshe idanunshi. Kafin ya shiga motsa jajayen laɓɓansa, alamun yana son furta wani abu ne. Amma tsabar miskilancinsa ya hana shi faɗar maganar, ɗan rungumo ta jikinsa kawai yayi. yayinda hannuwana ke gogar tamtsen hannun sa daya tallabe kan Amnah.
Baki ɗaya jikina ya soma wani irin tsuma yayinda dana tsurawa kwantaccen gashin dake nan luff kwance saman ƙeyarsa idanu. Ajiyar zuciya ta soma saki alamun wani barcin yayi awon gaba da ita keñan. Ajiyar zuciya na saki inama Allah godiyaa, domin dama a matse nake yaseen. Ina fita naji dakakkiyar muryansa ya ratsa har tsakiyar kaina.
"Ita kuma ledar fa?, ko na miki kama da bawa ko É—an dokonki?"
A tsawace yayi maganar duk kasancewar shi ba mai yawan haniya bane. Amma kuma tamkar ana busa sarewa haka naji fitar sautin nashi.

Jiki na rawa na buÉ—e motar tare da É—aukan ledar ina fita da hanzarina, shi kuma yaja motar da mugun gudu yana barin cikin anguwar.
Shigana parlourn babu kowa domin an shiga salla ne dama, ɗakina na shige bayan na biya ɗakin ummie na ajje mata ledar da Ammey ta bani. Wanka nayi na sanya kaya mara nauyi na fito Parlourn xuwa loƙacin kowa yana parlourn.
Da yaya Vijay na fara haÉ—a idona a cikin parlourn,Wani irin taussassan murmushi ya sakar min.wanda ya sanya babu shiri nima na sakar masa nawa murmushin.
Ahankali na tako zuwa tsakiyar parlourn, har zuwa loƙacin kuwa inajin idonun yaya jay a kaina. Satar kallon yaya Nurien nayi shi ɗin ma idonsa ƙyar akaina. (Innalillahi wa'inna ilair raji'un,miƙe shirin faruwa dani a karo na biyu?).
Nayi maganar da iyaka zuciyana babu mai jina. Ɓangaren su ummie da Abba na ma dai bata sanja sani ba, duk da wannan kallon mai kama dana tausayi-tausayi suke bina, banda yaya Nurien da naga shi naga har wani ɗan murmushi yake saki, loƙaci bayan loƙaci.
Cika nayi fammm sosea ganin harna ƙariso d/table in babu wanda yace min uffan. Ganin ina shirin juyawa ne ya sanya yaya jay cikin azama damƙar tsintsiyar hannuna, tare da furta .
"What happens to you Autarn ummu?"
Bakina na ɗan turo gaba tare da zame hannuwana a nasa ina cewa "zan ɗan duba wani littafi ne kasan nan da kwana biyar insha Allah ina makarantar gaba" ido sosae ya tsira mata tare yana hango iyaka zallar haƙiƙanin gaskiyar dake cikin idanun nata.
Shifa sammmm yama manta da wani zancen karatun da zataci gaba harga Allah. Zaunar d ita yayi tsakiyar su ba tare da kowa ya kuma cewa komi ba suka soma yin dinner nasu. Kowa da abinda yake saƙawa a ƙasar ransa dangane da al'amarin dake shirin kutso musu kai.
Duk da kuwa kowa tarin farin ciki ne dan ƙare a cenñnn cikin ƙarƙashin zuciyarsa, saidai idan suka auna a mizanin sukan hango tarin ƙalubale dangane da wannan al'amarin. Sudai addu'a shine nasu da haka dai zaman nasu na yau ya tashi.

________★★★_________

*ALIEYO*

Ahankali yake drive'rn nasu cikin dalleliyar motar ammiey da bai daɗe da sai mata ita ba. Cikin nutsuwar data zame masa jiki yake drive'rn tare da bin sautin karatun Alqur'ani dake tashi a cikin motar. Suna ƙarasawa gida loƙacin harma an shiga Masallacin Amnah kawai ga ajje ma ammiey yana barin parlourn, alwula ya daure tare da ƙaton masallacin dake manne da ƙofar gidan nasu.
Sai bayan sunyi sallar isha'i kafin baki É—ayansu su wnufi cikin shimfiÉ—eÉ—en estate nasu. Suna shiga dining area suka nufa nan suka yin dinner nasu a tare cikin farin ciki da tarin annushuwa.
A hankli ya miƙe yabar kan dining in fuskar nan a tamke sammm babu annuri, a kan 3 sitter ya zauna yana pressing phone nasa, Domin wasu abubuwan masu muhimmanci yake aikawa ta cikin wayar.
kyawawan ƙafafunsa ya mike yana mai ɗaura hadadden throwpillow akan ɗan shafafen cikin sa.

"ALIEYO!" Abba ya ƙira sunan shi kai tsaye babu alamun wasa a tattare da shi,da sauri ya tashi daga kwanciyar da yayi, Alama ya masa da inda suke zaune, hakan ya sa babu musu ya taso yana nufar su cikin tafiyar nan ta cikakkun mazaje.zama yayi ƙasa dab da ƙafafun Abba yana tonƙoshe ƙafafunsa, yagama bada dukka hankulansa gareshi. Ahankali ya ɗan saci kallon ammiey itama ran nan haɗe Sammm babu alamun wasa tattare da ita.

"Kana jina ko ALIEYO?. Da sauri ya ɗago jin sunan da abban nashi,ya kuma ƙiran shi dashi kai tsaye domin da wuya kaji yaƙirashi da sunansa kai tsaye saboda sunan mahaifin sa gare shi.
Sosai gabansa ya shiga faɗuwa domin ya tabbata tunda yaji Abban nasa ya kira cikakken sunan so to kuwa tabbas ko wanne irin saƙo za'a bashi mai girma ne.
A nutse ya jinjina na ma Abban nasa kai, duk kuwa irin yadda yaji gabansa na mugun bugu.
Ammiey ce ta dube sa cikin tsuƙe tata fuskar.
"Tunda kai bazaka fidda matar aure ba mu mun yanke shawarar zaɓa maka mata"
Cike matsanancin tashin hankali alieyo ya dubi mahaifiyarsa yana furta.

"Au me? Aure!aure kuma ammiey to wace zata ma aure ni?"
Baki É—aya baya a hayyacin sane cike cushewar tunani yayi maganar tare da soma harmutsa tulin sumar dake kwance luff a saman kansa.
Chapter 22 · 0% Book details