← Book details Ƙauna Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 56

Sashe 2

Ƙauna Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani kalan lumshe Idanunsa yayi tare da dafe daidai saitin zuciyarsa, "ina tsananin ƙaunarki sweet dreams, saidai inajin tamkar hakan bazai taɓa tabbata" da sauri yaya Nurien ya katse shi ta hanyar tararn numfashinsa. "Malam kawa mutane shiru zaka fara ko!?, wai kai wane irin mutum ne sai kace akan kane kaɗai aka fara soyayya , wllh na tabbata idan har kace haka zaka ci gaba da gina rayuwarka akan wannan ficilar yarinyar hmmmmmm" Sai kuma kawai yaja ajiyar zuciya tare da ɗan fesar da numfashi kaɗan,alamar hakan na qona ransa, domin yaya Nurien badai zafi ba.
Shi yasa sammm basa ga maciji shida oga Fatima.
ÆŠan murmushi kawai aliyu ya saki yana nufar inda ya tashi ya koma ya zauna, lumshe idanunsa yayi yana jin yadda zuciyarsa ke wani irin beating very fast, shifa gani yake shi kaÉ—ai Allah ya tattara ma duk wata nau'in soyayya ta duniya ya dasa masa acikin tsakiyar qirjinsa, shi kuma yake ma wannan baiwar Allah duka tarin soyayyarsa da zuciyarsa da rushinsa, shi kaÉ—ai yasan yadda yake ji akan mahaukaciyar soyayyar da yake ma Queen É—in nashi. Saurin ware lumsassun idanunsa yayi sakamakon famarkin da yayi daren jiya waye war yau, kamar Yanxu ne yake famarkin komae ya shiga dawo masa cikin brain nashi.
Tana durƙushe ta haɗe kanta da gwiwar ta tana wani irin kuka na fitar rai da tashin hankali, Ahankali yake qoqarin ganin ya iya buɗe koda idanun sane, amma ya gaza hakan. gaba ɗaya jikin sa yana jin babu wani wuri da yake motsi. Tsanani azabar kukan da take ne yasan shi ci gaba da qoqarin ganin ya buɗe koda idanun sane, babban burinsa bai wuce ace ya rarrasheta ta daina kukan nan ba. Da ƙyar ya iya buɗe Idanunsa a hankali ya soma ganin dishi dishi, inuwar wani abu dogo ya gani wanda bai san miye ba.
Ahankali ganinsa ya fara dan washewa nan yaci gaba dabin doguwar inuwar Nan, tarrrr ya sauqe ganinsa akan kyakkyawan bazaraten mutum min dake tsaye daga gefenta ya É—an bada baya, idonsa a lumshe hannuwansa duka biyu zube cikin aljihun wandon dake jikinsa, dammm haka yaji gabansa yayi wani irin mummunan bugu, qoqarin tasowa yake sai dai inaaaa ko ina na jikinsa babu inda yake motsa wa. Ita kuma har zuwa wannan loqacin kuka take wanda hatta da muryanta ya sauya zuwa wanda yaci kuka sosae, gani yayi wannan dogon mutumin dake tsaye saman kanta ya juyo Ahankali tare da kafe Fatima da idonsa daya sauya launi sosea, wani farin hanka ya miqa mata yana mata nuni data goge hawayenta, amma sammm taqi amsa. A galabaice ta tashi ta nufo inda aliyun yake a kwance tana ci gaba da kukanta, wanda tsabar kukan data sha idonta yayi wani irin jaaaa samansu ya É—an kumbura tare da kan hancinta shima daya É—an tashi kaÉ—an.
Tazo dab da shi tana shirin taimaka masa ya tashi yaga hannun wannan matashin nan ya zagaye saman ƙugunta da fararen hannayensa, tare da zuba mata lumsassun idonsa. qoqarin kwatar kanta ta shiga.
shi kansa bai san yadda aka yiba kawai ya tsinci kansa ta fara mata magana cikin qarfin hali da galabaituwa.

”Queen!”
Ya qira sunan ta cikin wani irin sanyin dashi kansa bai san inda ya samo shi ba, yaci gaba da mata magana.
”Queen wannan mutumin da kike gani shine mahaɗin rayuwarki, kamar yadda kema kece mahaɗin rayuwarsa!, queen ki karɓi wannan ƙaddarar da mahaliccinmu ya ƙaddaro miki, domin nasan a gaba dole zaki rabautaaaa” sai kuma wani irin tari ya turnuqe shi wanda yasa numfashinsa sarqewa yana qoqarin barin gangar jikinsa. Cikin azama ya dafe daidai saitin zuciyarsa idonsa daya kada yai jazur na azabar dake fusgarsa, amma duk da haka bai fasa faɗin maganar da yake son qarisa mata ba.
”kada kiyi butulci ga mahaliccin mu Queen domin nasan kinsan baya taɓa ɗaurama bawansa ƙaddarar da tafi qarfinsa!, kiyi haƙuri wannan shine ƙaddarar ki, wanda Ubangijii ya rubuta tun ran gini tun ran zane shine mijinki,cikon rayuwarki! shine uban ƴaƴanki ba Niiiii!” . Gaza qarisa zancen nashi yayi sakamakon numfashinsa da yaji ya ɗauke. "Innalillahi wa'inna ilair raji'un" ya shiga faɗa a bayyane yana jujjuya kansa da yaji ya sara mishi, " ya ilahi ya mujibud da'awati, wannan wani kalan bahagon mafarkine haka dahar na gaza fashimtar sa" yayi maganar zufa na yanko masa.

Yaya Nurien da kuma babban abokinsa Deen ne suka zuba masa ido duka suna kallon sa.
Cike da takaicinsa yaya Nurien yace, "aikin banza kana son kashe kanka a banza akan wata guntuwar yarinya qarama da a haihuwar kaji ka haifeta" kansa yaci gaba da jujjuyawa shima yana cewa. "ba zaka fashimta ba yayan mu Ni kaina bansan wacce iriyar soyayya nake ma Queen teemah ba " dake haka yake qiran sunan yaya Nurien da yayanmu tun da ya fara son Fatima. ”mtssssss" yaya Nurien yaja tsaki tare da tashi yana barin studion dan bazai tsaya sauraran wannan kayan haushin daga babban amini Kuma ɗan uwansa ba.
Da kyar ya ƙarasa Ayyukansa na cikin studio ɗin , wanda dama aikin bugu Sabuwar waqarsa ne da yake son saki cikin satin Nan Insha Allah,wajajen 6:40pm ya tattara komai ya adana, ya dau wayar sa da nufin qiran yaya Nurien sai kuma gashi ya shigo cikin madaidaicin stadio ɗin nasu, hannu aliyu ya miƙa masa tamkar ba yanxune suka rabu ba, shima hannun ya basa suka yi musabaha. Shima ƴan takardunsa ya tattare waje guda suna fitowa daga cikin studion, Aliyu ne ya rufe Nan suka dauqi hanyar gida kasancewar suna anguwa dayane, kuma maqotan juna.

★★★

Koda ta shiga cikin ko kallon inda Farida take ba tayi ba, saima qin zama da tayi a desk É—inta ta wuce desk É—in qarshe. Gaba É—aya ajin suka bita da kallo ganin yau kuma teemah ce ta shigo aji ba shegen surutun nan, koda aka tashe su ma ko kallon inda bestien nata take ba tayi ba tayi gaba abinta, da É—an saurinta ta qaraso wurin fatiman. "Mutum dai yace Allah É—aya, ayi mutum da shegen zuciya da kafiyar masifa da shegen taurin kai" ci kanki Fatima bata ce mata ba haka taci gaba da tafiyarta ita kuma Farida tana binta da tsiya takunta, haka har suka qarasa gida Farida ce ta fara wuce kasancewar gidan sune a farko, kafin itama ta shige nasu gidan.
Tana qoqarin buɗe ƴar qaramar qofar get ɗin taji daga ciki ma ana alamar za'a buɗe ɗin, dakatawa tayi tare daja baya domin bata raba ɗayan biyu Abba ne ko wannan iyayen zafin ran yaya Nurien. Shi ɗin ne kuwa da sauri tayi qasa da kanta sakamakon wata uwar harara daya dallara mata, cike da inda² tace " ya ya bar bar ka da da re" ko inda take bai kuma kalla ba sai ma alama daya mata irin zasu haɗun Nan.
Tana samun ya qarasa ficewa tayi saurin faÉ—awa cikin gidan. "MUGU" ta faÉ—a tana saurin danne bakinta gudun kada ya jiyota, (dan ma nasan ummiena ba bari zatayi ka dake niba)
Ta fada tana kara murguda baki kamar yana gabanta.
Da sallama ta shiga cikin palon nasu ganin babu kowane ya sanya kai tsaye É—akin ta ta nufa, cire uniform nata tayi tare da faÉ—awa cikin toilet ta É—auro alwula. Darduma ta shimfiÉ—a ta tada sallar magrib. Bayan ta idar ne ta fito palon inda abbanta ummie sai kuma yaya Nurien duk suna hallare a falon, domin yin dinner na dare, cikin nutsuwa ta shiga gaida iyayen nata tare da babban yaya Nurien. Duk amsata suka yi cike da kulawa da tsananin soyayyarta a garesu, É—aya daga cikin kujerun dake zagaye da É—an madaidaicin dinin table É—in taja ta zauna, nan ta shiga saving na kanta da kanta. A hankali cikin tsananin nutsuwa take tsaqurar shinkafa da miyar da taji kayan lambu take kaiwa É—an qaramin bakinta wanda saika iya rantse wa dededa qaramin cokalin roba, bai zama lallei ya shiga ba. Bayan sun kammala dinner É—in ta tattare baki É—aya palon kafin suka É—an taba fira a tsakanin su, irin ta zallar shaquwar dake tsakanin sun nan.

8:15pm.
Tana zaune saman darduma Alqur'ani riqe a hannunta tana raira karatu cikin kyakkyawar qira'arta, inda take bama ko wanne baqi haƙƙinsa ne, taji wayar ummienta dake maqale a wurin ta ta ɗauki sowa alamar ana qiranta, bata dakata da karatun da take ba duk da kai tsaye tasan waye mai qiran, haka baisa ta dagata karatun da take ba har Saida takai qarshen surur da take karantawa na suratul Ahqaf.
Bayan ta yi addaointa ta shafa kana ta nufi wayar tana É—auka daidai tana É—aukarn wayar wani qiran ya kuma shigowa, picking tayi tare da manna wayar da kunnenta.

“Assalamu Alaiki tauraruwa a cikin taurari”
Taji daddaÉ—an muryan nurul qalb É—in nata ya ratsa har tsakiyar kanta.

Saman gado ta fada tana murmushi tare da cewa.
"Wa'alaikas Salam birnin zuciyar Fatima barka da dare!"

“Na yi missing wannan daddaɗanr muryarn sahiba"

Ɗan ɓata rai tayi tare da cune ƙaramin bakinta guri guda haɗi da turo shi gaba, tace.

“Ba na ce ka daina ce min Sahiba ba?”

Daga cenñnn ɓangaren Aliyu kuwa ƴar dariya yayi tare da cewa .

“Yi hakuri Sahiba ba zan kara ba”

“Wallahi zan kashe waya ta”
Tayi Maganar cike da Æ´ar shogoba

“Yi hakuri na daina Queen yanzu dai fada min me da me Babyna tai yau?”

Wani irin murmushi ta saki tana jin sonsa har cikin cenñnn qasar zuciyarta. Kanta ta ɗaga sama alamar tunani, kafin tace.
"Nayi karatu sosea a makaranta Sannan munyi faÉ—a da bestie Naaaaaa!, yaya Nurien kuma ya harareni Nima na rama na nurguÉ—a masa baki na" wata iriyar dariya Aliyu ya tilliqe da ita tare da faÉ—in.
"Mai yasa Queen sammm bata jine kammm" itama dariyar ta saki tana rufe fuskarnta irin taji kunyar Nan.
"Ni ina ji mana, kawai kasan halin muguntar yaya Nurien sarai, ba sai na tuna maka ba ai kaima kanka ka san halin abokin ka sarai!" Tayi Maganar tana turo bakinta gaba tamkar wanda yake gabanta ko yake ganinta.

"A a fa queen kada muyi haka dake, ba na hana yima yaya rashin kunya ba?"
Chapter 2 · 0% Book details