← Book details Ƙauna Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 56

Sashe 8

Ƙauna Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin tsantsar farin ciki na ƙara riƙe wayar da kyau, bakina tamkar ya yage nace. "Wai don Allah da gaske yaya jay ka kusan zuwa, ka taho min da aunty zeey da julaibeeb, ka taho min da kayan daɗi irin na ƴan ƴan gayun indiyawan Nan don Allah yayaaaaa jayyyy" ko Numfashi ban tsaya shaƙa ba haka na dinga ziba abuna.
Daga cen kuwa murmushin yarintar teemah yake da har yanzun bata ganin ta girma, (kodan ita kaɗai ce mace kuma oho. Ya) ya faɗi maganar yana ɗage kafaɗunsa alamar oho ɗin nan,aunty Zainab dake jin zubar da fatiman take ne ta saki murmushi tare da amsan wayan tana kara ta a kunnenta, kafin tace."ki fara shiri yarinya tunda naga kina ƙaunar India zan taho dake idan mun zo", dariya ta ƙyalkyalce tare da cewa.
"Gaskiya bazan biku ba, idan na biku ummiena kuma ga zauna da waye?, kawai dai ku taho min da kayan daɗi na ƴan gata" baki ɗaya dariya suka fashe su dukansu yana zare wayar tare da kashe abarsa. Domin yasan tsabbb shirmen fatima zasu iya kwana suna wayar ma ita bata ƙiba. Tana jin ya kashe wayar ta nufo palonsu da tsananin zafin ciki don sanar da ummiensu jinin jiki ya kusa zuwa.
Turus taja birki ganin yaya Nurien a harɗe a parlourn yana zaune ƙafa ɗaya kan ɗaya. A take duk annurin dake kan kyakkyawanr fuskarta ya gushe, ko inda yake bata kuma kallo ba ta shige bedroom ɗin ummie, shi kuwa yaya Nurien bai ma san da shigowar ta palon ba don hankalin sa kachokam yana kan laptop nashi da yake video call shiɗa ɗan uwansa jay. Ahankali yake sakin murmushi sai kamarsa da fatima ta bayyana sakk. Ban san mene aka ce masa ba amma har yanzun murmushin na kwance saman kyakkyawar fuskarshi mai kama data Fatima, "kasan mutumiyar ka da rashin ji. Idan akace babu mai taka mata birki to birkicewar nata sai yafi haka, sammm ba'a son raina nake mata wasu abubuwan ba!, kasan ɗazu marinta ta sanya nayi!"
Ya faɗa a marairaice tare da dunkule hannuwansa yana harbin iska alamun shi ma marin ya taɓa ransa.
Cikin dariyar diramar su jay ya shiga ƙyaƙyata dariya yana tafa hannayensa, idonsa har wani ɗan ruwa ruwa suka tara tsabar dariyar.cikin yin dariyar yace, "wllh irinsu Fatima sune maganin masu halin ALIEYO Naaaaaa". Wata kafurar dariya yaya Nurien ya saki shima yana cewa "Ai a fannin mugunta kai BOSS ne babban yaya, yo in banda tsabar mugunta taya kake tunanin masu rawar kai irin su Fatima ka haɗa su da wannan murɗaɗɗen abokin naka, yo ai da sunan sa sorry indai kuwa haka ne babban yaya ".
Yayi maganar yana tuno abokin yayan nasu, da yake Nan tamkar me zuciyar ifiritan farko. Shifa zai iya rantsewa tunda ya mallaki hankalin kansa tare ya sansu da ƴaƴansu, amma zai iya rantsewa bai taɓa ganin koda farin haƙorinsa bane, tamkar wanne aka ma wahayi da shiga wuta. Yo shiga wuta mana mutum kullum ba fara'a.
Kallon sa kawai yaya jay ya tsaya yi, "ka gama dariyar naka ko akwai wata?" Yayi maganar da alamar tambaya. Shi kuwa dariyarsa yaci gaba dayi domin har ya hasko haukar da za'a buga, "Dan ƙari" ya faɗa yana sake sakin wata dariyar.
"Wllh zan kashe tunda hauka zaka min dan ubanka" yaya jay ya faÉ—a a fusace domin shima wani murÉ—aÉ—É—en ne ai, idan yaso ayi wasa da dariya idan kuwa bai soba yanxune yaci uban mutum.
Kimtse dariyar yayi (amma fa wllh zanso ganin wannan games ɗin) ya yi maganar a cikin zuciyarsa. wllh ya tabbata rana ɗaya sai ya kusan kashe ta da duka, don Fatima ba ƙaramar ƴar takife bace, ta wajen shegen tsokanar masifa da shiga shiri ba shanu, kata samm samm bata da yafiya ko kaɗan.
Haka dai suka ci gaba da firansu sama² domin shi gaba ɗaya ya tafiya duniyar tunanin zancen yayan nasu. (Wato yaya Jabeer ba ƙaramin mugu bane yaseen) ya yi maganar azuciyarsa. Ganin bakinsa kamar yana motsi ne ya sanya shi faɗin, "kace mene akie?"
"Ban ce komi ba babban yaya" katse video call ɗin kawai jay yayi daga cenñnn ganin baki ɗaya kamar hankalin ɗan uwan nasa baya jikinsa. Ware ido Nurien yayi ganin sha biyu saura.
"Ashe mun ɓata loƙaci haka ban sani ba" ya faɗa yana tashi tare da nufar bangaren sa.

★Washe gari★

Da farin ciki ta tashi ba kaÉ—an ba tayi missing na yayan nasu, kasancewar juma'a ne kuma ta fita daga makarantar Sakandire ya sanya ta fara gyaran gidan, bayan ta kammala gyara ko ina ta shiga kitchen ta haÉ—a musu dinner cikin abinda bai gaza 50 mini ba ta kammala komai.
Kasan cewar soyayyan dankelen turawa ta soya musu da ƙwai, sai lemon kwakwa data haɗa musu.

*******

******"Jay pls ka dawo gida haka nan mana, koba komi kazo kayi azumi a gida kusa da ummie" tamkar wanda aka sanya irin dolen nan ko aka matsa mishi yayi maganar.
"Hhhhh tunda yau ga wanda baida ra'ayin kansa ba, to duk na gano wayonka malam. Ka fito fili kawai kace kana son in dawo kayi missing kunun gyaɗar queen teemah 🥰 muna fhiki kawai" ya faɗa yana sakin dariya wanda ya tunzura aliey ya datse kiran baki ɗaya tamkar ba shine yayi ƙiran ba (da gaske ya rantoni fa) ya faɗi maganar acikin zuciyarsa.
Amnah dake jikinsa a kwance ne taɗan zame tare da ɗago kanta tace "laaa papiey uncle jay ɗin kane kayi waya dashi, amma shine koka sanmin shi!" Ɗan ɓata fuska yayi tare da kawar da kansa gefe yana yamutse kyakkyawanr fuskarsa tare da ce mata. "Mun ɓata ne ai yanzun, sai gobe damu shirya"

"To akan mene kuka ɓata papiey?"

"Sunanta daya ambata min"

"Sunan waye?"

"Shiiiiiiiiiiiiiii " ya É—ora hannunsa saman bakinta domin harya gaji da surutun da Amnah ta sanya shi, gashi shi É—in ba ma'abocin zance bane.

Badon taso ba haka ta haƙura ta ƙyale papieyn nata don tasan ba ƙaramin aikin sa bane ya yace ta tafi wurin ammiey, anan wurinsa tayi barci kwantar da ita yayi akan gadonsa toilet ya shi Yaɗan watso ruwa tare da ɗaure alwula,wanda hakan al'adarsa ne baya kwanciya ba tare da ɗaura alwula ba. Hasken ɗakin ya kashe yana kunna Electric kindle a take ɗan haske kaɗan ya bayyana.

****
Itafa tunda taji masoyinta farin cikin ta mai ƙaunarta yayanta jay zai dawo ta kasa zaune ta kasa tsaye, Allah Allah kawai take ya zo domin ba ƙaramin missing nashi tayi ba. saidai duk yadda takai ga nacinta yaƙi bata mata ranar da zai zo.
Dan dole haka ta haƙura ta zauna zaman zuba idon zuwansa ko yaushe.
Duk da ba wani shiri take da yaya Nurien ba, amma Saida ta tambaye shi ko yasan ranar da yayan nasu zai dawo.

A firgice ya tashi sakamakon wani irin mummunan famarki da yayi, Rumtse Idanunsa yayi qamm tare da qara qanqame jikinsa wuri guda,a ƙalla yaɗau minti biyu zuwa uku kafin ta yaki ajiyar zuciya.amma ba baiyi motsin kirkiba balle kuma ya iya furta wata magana.
Sosai mafarkin ya firgita shi, in banda tsuma babu abinda jikinsa ke faman yi sai uban zufar dake yanko masa.

kai tsaye bathroom nashi ya shige jin zuciyarsa na masa wani irin luguÉ—en masifa.
Shower kawai ya sakarma kansa yana daya kunna na dukan jikin sa yana fatar samun sassauci daga abinda yake ji acikin zuciyarsa.
Yanayin yanda ruwan ke dukan jiki da kuma kansa kaÉ—ai, ya Isa bayyana maka cewar lallai ba'a cikin tunani da kuma hayyacinsa yake ba. Domin duk yanda yaso da yayi zeroying mind nashi abun yaci tura. Ahankali yakai hannunsa ya kashe showern, tare É—aukar wata kakkaurar bathrobe É—in dake gefensa ya sanya a jikinsa.
Hannunsa ya É—aura akan handle É—in qofar, ya buÉ—e yayin da yake jin qirjinsa na amsawa aduk wani taku da zai yi.
idanunsa da suke a lumshe ya ware tare da ƙurama wuri ɗaya ido tamkar Anan ne za'a faɗa masa fassarar mafarkin da yai.

Ahankali ya riƙe kansa da Hannuwansa biyu da yake jin tabbas yana gaf da samun matsala, indai har zaici gaba da shiga irin wannan attack ɗin. kwanciya yayi daga jikin sopa domin yana ganin, tamkar daya koma ɗin mafarkin da yai zai kuma maimatuwa ne. "Ya Ilahi" ya faɗa yana ci gaba da tasbihi acikin ransa.

Ƙarar shigowar message cikin woyar sane ya sanya shi fuɗe idonsa, da suka gama galabaituwa sosae, Ahankali ya janyo wayar tare da shafa screen nata. Yake p
Kyakkyawa Pics ɗin Safiyya ya bayyana ganin sunan jay ne ya sanya shi buɗe saƙon ya karanta saƙon.

Duk da yanayin da yake ciki hakan bai hana ya É—an yi murmushin gefen baki ba, (Tijara kawai, malam da sanya mutum aiki)
Shi kaɗai ya ƙaraci mitar shi kafin ya kife jikin kujerar wani irin barci yazo yayi awon gaba dashi. Washe gari haka ya tashi daɗan sassauci yau kamm ko ina ha gaza fita haka yayi wunin gida sai Bayan sallar isha'i,ya ɗauki ɗaya daga cikin fitattun motocin ƙirar Lexus Rx baƙa wuliƙ. Wanda mutun ganin farko zai yi mata yasan ehhhhhhhhh lallei nera ba ƙaramin kuka tayi ba, wajen siyar wannan rantsatstsiyar mota.

Suna zaune kamar kullum a farfajiyar gidan ita da masoyinta rayuwarta Aliyu shureim nurul qalb ɗin ta. Sassanyan murmushin farin ciki dake saki domin daddaɗan zancen da yazo mata dashi, na cewar Nan da ƴan watan Ni ƙalilan zata zama mallakin sa, Uwar ƴaƴan sa Insha Allah.

Hannuwanta cikin nashi yaci gaba da dubanta yana jin tamakar ya buɗe zuciyarsa ya zire ta kawai a ciki, domin ya huta da azabtar dashi da soyayyarta take matuƙar yi. Dai-dai wannan loƙacin rantsatstsiyar mota baka wuliƙ ta sanyo kanta cikin haraban gidan. dummmm haka kawai zuciyarta taji tayi wani irin bala'in bugawa da ƙarfin masifa.
Chapter 8 · 0% Book details