← Book details Ƙauna Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 56

Sashe 30

Ƙauna Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya ƙare maganar wasu irin ruwa ruwa na tarun masa cikin idanunsa, hasalin blue ɗin cikin su na ɓoye wa.

"Bani da loƙacin ɓata ma laƙaci loƙacinsa zanyi biyayya wa wa iyayena ne kawai wajen AURENKA, Kana bana jayayya da mahaliccina akan abinda ya tsarama rayuwana, Amma ka sani tunda na rashin Aliyu shureim na zare duk wata alaƙa da ya shafi komi ma na wannan duniyar bawai iyaka auren ka ba!” sharrrrr ruwan hawaye tuni ya wanke mata saman kyakkyawar fuskarta, da Allah bai amshi rayuwar nurul qalb ba da tuni nasan, ina ɗauke da cikin sa koma na kusa haihuwa, duk wanda ya zaɓi rayuwar aure dani to ya sani zai rayu ne kawai da iyaka gangar jikina!, amma zuciya da ruhina suna tare da nurul q.........
Wata iriyar razananniyar tsawa ya buga mata cikin ainihin zafin zuciyarsa ya kaima wuyanta uban shaqa da dukkan alamu ya fice a hayyacin sa, cike da tsananin ɓacin rai cikin hosky voice nashi yace.
”Ance miki Ni! ɗin sonki nake?, uhm-uhmm to ma za ki farka daga nannauyar barcin daya dauke ki, Bana jin akwai wata halitta acikin duniyar da zanso zata kuma birgine bayan Matana *SOFEEYERH* ,therefore, if you hope to find a husband, you should remove it, because I am stronger than you, I passed the class of a girl like you”

Ɗago kanta ta yi ta zuba masa narkakkun idanunta, sai kuma ta ɗauke kai ba tare data furta komai ba, saima ƙoƙarin janye jikinta da take daga yadda ya haɗeta da jikin ɗakin. Da wani irin azababben kallon ƙasarn ido ya shiga bin ta dashi, idanunsa har wani sheƙi suke na ruwan da suka tara a cikin sa, jin yadda sautin fitar numfashinsa ke sauƙa gefen wuyanta shi yafi komai ɗaga mata hankali, jinta take a mugun takure ga wasu abubuwa da taji suna neman tafiya da numfashinsa. ganin yadda take ta ƙoƙarin janye jikinta a nashi ne ya sanya shi ƙarasa haɗe gab ɗin dake tsakanin su ta haɗe jikinsa da nata, haɓarta ya ciro tare da zuba mata sexy eyes nashi, yana binta da wani kallo masu tarin ma'anoni. Idanunta ta shiga kif kiftawa, tana kare matse jikinta dake manne da nashi jikin.
Wani irin kafirin murmushi ya sakar mata loƙacin da yake raba tazarar dake tsakanin su, yana mata wata alamar da bansan mene yake nufi ba da yatsun hannunsa. Har ya fice a sittin room ɗin, durƙushe wa tayi a wurin tare da sakin kuka me azabar ƙarfin gaske,
”na shiga uku na lalace Ni Fatima, me wannan azzalumin yake nufi dani ne?, Ni kuma haka salon tawa ƙaddarar take daga wannan sai wancen Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”

Fareedah ce ta faɗo sittin room ɗin jin kukan queen, ilai kuwa ita ɗin ce ta gani durƙushe tana rera kuka, cikin tashin hankali fareedan ta nufe ta tare da faɗin.
”sweetyn meya same ki, meya hfaru dake? Mene aka miki?” cikin sheshsheƙar kuka tace.
”lovie mine ma bai same ni!, tabbas nasan Nima na kusa mutuwa, tamkar yadda yaya Aliyu ya tafi ya barni ina gab da bin bayansa” a ɗan ruɗe fareedan ta shiga faɗin, ” sabo dame zaki ce hakan?, bayan muna ta murna kin sami lafiya kana zamu sha bikin ki kuma, ke nifa yanxu ma xuwa nayi mu shiga koda kasuwa ne. Kinsan loƙacin bikinku da yaya Aliyu ma tun iyazu muka fara shiga kasuwa”

Kanta ta shiga girgiza mata kafin cikin kukan taya kuma kufce mata ta shiga faÉ—in.
”Da ban banci tsakanin wannan auren da kuma wance fareedah, ke a tunaninki har akwai wani abu daya saura a cikin rayuna da kike tunanin zan yi shi don nishaɗin kaina, bayan mai bani farin cikin baya raye!”
loƙaci ɗaya ta kuma fashewa da wani irin raunataccen kuka, tsayawa fareedah tayi tana kallonta girgiza kanta tayi jin yardar queen ke kuka tamkar ranta zai fita, tabbas tana matuƙar tausayin ƙawar nata kuma ƴar uwarta domin kuwa abar a tausaya ma ɗin ce, tabbas ƙaddara ce mai ƙarfi tazo ta gitta rayuwarta. Loƙacin da take tsaka da nishaɗantuwarta.

jiki asanyaye fareedah ta ƙaraso gareta tana zama kusanta, murya a raunace a kuma tausashe tace.

"Kiyi haƙuri sweery ki ɗauki wannan ƙaddarar kamar yanda kikayi abaya don Allah don Annabi karki saka abin nan aranki ki jawoma kan ki wani sabon ciwon, bayan wanda kike a ciki ki taimaka kiyi haƙuri pls sweetheart, Insha Allah ba zaki mutu ba domin kuwa akwai dubinki wanda tarin ƙaddarorin su suka zarce naki, kuma suke rayuwa, ke fa iyaka saurayi kika rasa, wasu faiɗe ake musu da ƙarfin masifa daga ƙarshe ciki ya bayyana amma kuma hakan bai hana su rayu da abinda suka haifa ɗin ba har suyi rayuwarsu cikin farin ciki, wasu kuwa zasu rasa uba uba ɗan uwa ƴar uwaa, miji ƴaƴa, wasu zaki same su da tarin kalubalen ƙaddarori iri iri wanda da zakiy gamo dasu da kinji taki ƙaddarar ba a bakin komi take ba.
UWAA itace mafi ƙololuwar da idan ka rasata har gaban abada ka rasata keñan, wanda kafff duniyar ko za'a tara dubanta to kuwa tabbas babu kamarta!, haka ma mahaifi, Shine duk wani ginshiƙin rayuwa da ɗawaini ta ƴaƴansa, wanda akace randa babu shi tofa shikenan baka da wani saurin gata saina Ubangijiin sammai, wasu ƙaddarar su barace barace, wasu makafi ne wasu guragune!, wasu kutarai ne, wasu wasu kowa yana da nashi salon ƙaddarar, ke kuwa fa iyaka mijin da ake shirin aura miki kika rasa, wanda ayau idan Ubangijii yaso zai baki fiye ma da wanda kika rasa ɗin, harma ana tafe ki iya mantawa dashi acikin rayuwarki dama duniyarki baki ɗaya, shin ina alƙawarin da kika min kodai kin gaza ne, shin ina nasihun da ummie take miki kina nufin har wasiyyar yaya Aliyu Naaaaaa kin haɗa kinyi fatali dasu Fatima?”

Kasa shuru queen tayi dan ji take kamar yanzu ne komai ya faru, ji take zuciyarta na yimata wani irin soya tabbas tasan zafin ƙaddara domin kuwa ta zana mata nata salon ƙaddarar acikin tsakiyar ƙirjinta, wanda tasan har gaban abada hakan bazai taɓa gushewa daga cikin zuciyarta ba.
da kyar Fareedah ta samu ta rarrasheta tayi shuru gudun kada wani sabon ciwon ya sameta bayan wanda take ciki, kana bata son kowa ya fashimta halin da take ciki.

Tisa ƙeyarta tayi har bakin toilet ɗin dake cikin sittin room ɗin tayi, fuskarta ta wanko tare da tsane ruwan Kafin su nufo hanyar fita. Turusss duka su biyun suka ja suka tsaya ganin yaya Nurien tsaye a bakin ƙofar fitar alamun yaji komai keñan, jiki a mace suka dago kai suna kallon sa. Da ido suke roƙarshi ya fashimci su kar wanda yaji abinda ya faru tsakanin ta ALIEY, shi ina sammm ma bai fashimtar Yaren su, idanunsa yawo kawai suke akan fareedah, jin shiru shiru yaƙi ce musu komai ne ya sanya su ɗan dago kansu, ai kuwa caraff suka kama yayan nasu ido duka biyun kan fareedatu baiwar Allah. Wani irin kasa tayi da kanta tana jin tamkar ƙasa ta tsage ta shige.
”Kin iya lallaɓa soyayyar wasu amma Ni har yanxun kin gaza lallaɓa nawa soyayyar”
Sune kalaman da suka shiga cikin kunnuwansu, dake ma har an bashi fareedan tun tuni amma firrr taƙi tace ita ba zata yi aure yanxu tabar queen ɗin ba, wannan shine dalilin jirkinta auren nasu da kuma queen ɗin ta samu shine fa aka haɗe bikin nasu. Nan da sati kai biyu masu zuwa. A kunyace ta zame hannunta dake cikin na queen, kafin cikin fakar idanunsu yiffff ta fice a gidan da dan gudu.
Dama kuma tunda zancen bikinta da yaya Nurien ya tashi ta rage shigowa gidan kunsan abinka da kunyar nan irin ta sirikai. Sosai queen ke ƙyakyata dariya don ba ƙaramin dariya fareedan ta bata ba, wannan abu shine dalilin daya sanya queen mantawa da batun wani Aliey.....

*A week later*

Sosae abubuwa suke tafiya cikin tarin farin ciki, inda aka kai kayan lefen yaya Nurien gidan su fareedah wanda yaya jay ne yayo oder nasu tun daga Indiya, kayane na gani na faÉ—a akwatuna takwas aka mata kaya kuwa sai kun gansu, aikuwa ranarn mutuwar Aliyu shureim sabo ya dawo musu, haka suka ringa É—auke kwalla daga saman fuskokinsu.
Don sun san da yana nan sai yafi kowa murna da wannan auren Allah Sarki dama haka rayuwa take saidai muce Ubangijii ya jikan Aliyu shureim.

Haka dai abubuwan suka ci gaba da wakana, biki nata ƙara kusantowa ƴan uwaa na nesa harsun fara zuwa gidajen biyu ko nace uku.

Ɓangaren Aliey kuwa shi har ya manta da wani lamarin aurensa, Sai Ranarn dasu Oum Anum suka sauƙa a ƙasar 9j ita da ahalinsu na Madina, wajen su shidda suka zo Sarki julaideen wanda ya kasance shine babban yayansu sai kuma Oum Anum yaya ga ammieyn sai kuma Oum abiddeen wacce ta kasance ƴa ta uku sai kuma ita ammien wacce ta kasance autarsu, Su huɗu ne suka kasance a wurin mahaifiyarsu AYUSSHA wacce suke ƙiranta da MAH!. Sai ita anun ɗin da suka zo da ita, da da farko tasha bikin Irfan ne zasu zo sai daga baya take jin ashe bikin alieyo ne.
Ranarn har rufe kanta tayi a ɗaki tasha kukanta, domin ba ƙaramin so take ma alieyon ba shi kuma Samm bata gabansa, a waya ma data fiye damunsa blocked nata yayi.
Yanxu haka bikin ta saura baifi wata É—aya ba amma duk da ta gaza cire Aliey daga cikin rai da ruhinta.

Cikin nutsuwar sa yake saƙƙowa Samm fuskarnan ko ɗigon annuri babu, yana sanye cikin wasu haɗaɗɗaun trouser blue black wanda suka ƙara haskaka fatarsa suka kuma bayyana ainihin ƙyawunsa.
hankali kwance yake saƙƙowa hannuwansa zube cikin aljihun wandon sai baza ƙamshi uban ƙamshi yake,
Chapter 30 · 0% Book details