← Book details Ƙauna Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 56

Sashe 6

Ƙauna Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Babyna kin yi kyau sosai” naji fitar sautin daddaɗar muryansa ya ratsa har tsakar kaina. "Uyummmm" kawai nace domin Nima abinda neke shirin faɗar keñan ya rigani, "idan ana maganar ƙyau aka zo wurin ka ai angama kaine kattt nurul qalb" wani irin murmushi ya saki mai ɗan sauti yana zare hannuwa na daga tagumin da nayi. Ɗanfareriyar wayarsa ya zaro daga aljihun gaban rigarsa yana cewa "ban da dai son kaiiiii queen,duk ƙyawawan da suke nan a cikin duniya amma ki dubeni kice nine katttt" ya faɗi maganar tare da ce min "ga sabuwar waƙar dana fitar yau queen yau wanda nayi wakar ne sabo dake sarauniya" amsan wayan nayi da tsananin murna domin duka yawancin waƙoƙin sa akai nane yake yinsu. Play na danna wani irin amintaccen taken waƙar ne ya fara tashi,Kafin wakar ya fara tashi cikin Amon muryansa da kuma daɗi.

"SARAUNIYA KIKE"

Sai kuma aka nuno wata wata haÉ—aÉ—É—ar beb ta nuna shi tare da cewa.

"MAI MARTABA KAKE"

Rumtse idanunta tayi da ƙarfim masifa tana tsayar wa domin bata buƙatar ci gaba da kalla. A take wani irin azababben kishinsa ya rufe ta, itafa dama sammm bata wani yarda ya fara in joining da mata ba, ƙara yayi abarsa iyaka shi kaɗai ɗin sa. (Yanxu miye haka keñan) ta faɗa hakan wanda take tunanin a zuciyar ta tayi zancen. "Babu komi ƴar amshi cefa kawai queen sarauniya mata tauraruwa a cikin taurari" don yaga ranta ya ɓaci alamar hakan baiyi mata daɗi ba keñan. Domin zuciyarta da nashi guri guda suke a tare suke bugu duk yanayin da ɗaya daga cikin su yake to kuwa shima ɗayan koda baya kusa yakan ci hakan a cikin jinin dake gudana a jikinsa.
Wani irin abu yaji yana taso masa na mai kama da rauni rauni haÉ—i da ganin tamkar ya gaza ne, wajen kulawa da soyayyar rayuwarsa.
Ita kuwa tunda ta kife wayar ko kanta ta kaza É—agowa balle yasa ran zata mishi magana ma, zullumi kike queen akan tarin soyayyar da nake miki Fatima!, kinfi kowa sanin waye Ni!, mezan iya da abinda baxan iya ba ina tunanin duk duniya idan aka É—auke mahaifanmu munfi kowa sanin kanmu da kanmu!, da abinda zamu iya da kuma abinda ba zamu iya!, don haka ki daina zullumi ko É—ar akan soyayyata queen".

Ahankali ta dago kanta wanda zuwa loƙacin har idanunta sun ɗan sanja launi xuwa ja kaɗan da suka sirka.

Zullumi na ke da ɗar-ɗar ba!har abada Zaɓin raina shine zaɓi, bani da haufi akan zaɓarka da nayi a matsayin abokin rayuwa , na san bazan yi nadama ko dana sanin kasancewar ka gwanina ba, A duk loƙacin da nake tsara irin rayuwar zamantakewar auren da za mu yi, sai na ji wani abu ya tsaya min, ban san ko minene ba ban san mi hakan ke nufi ba, abinda na sani Kawai shine bazan iya buɗer idanuna ina kallonka da ko wacce mace ba acikin wannan duniyar. Idan aka ɗauke Mama da kuma bestie ba"

{ bestien Farida take nufi ƙanwarsa ita kuma Maman mahaifiyarsa take nufi, wacce ta kasance ƙanwa ga mahaifinta Allah yasa kun gane🤗}

hannunsa yakai kan nata hannun dake a kife

"Kishi ne" ya faɗi maganar idonsa cikin tsaƙiyar Idanunta da suka kaɗa sosae.

“Ba ni da tabbacin ko minene”

Hannuwanta dake cikin nashi YaÉ—an matse da karfi, tare da cewa.

“Ko ma minene ya tafi can ya bar min queen ita kaɗai domin bamu san yadda rayuwar gobenmu zata kasan ce ba!", wala Allah da nine zakiyi rayuwar, wala Allah kuma wanda zaki yi rayuwar dashi yana cennn dakon tsammanin juma yin zuwanki cikin rayuwarsa, ba ni baneeee”

Wani irin dokawa ƙirginta yayi a gigice ta ɗago kanta tana kallon sa, domin exctly irin wannan maganar ya faɗa mata cikin mafarkinta na ɗazu ɗazun nan.

(To wai mene yake shirin faruwa dani neeeee? Ina bazan jureeee ba!, baxan iya ba baxan taɓa ɗaukar hakan baaaaaaa NOOOh)

Tayi Maganar acikin zuciyarta tare da dafe kanta da hannuwanta duka biyun.
Tamkar wanda ya karanci zuciyar nata yace.
"Zaki iya ɗauka mana, dole zaki iya, zaki iya domin ba zaki taɓa sanja ƙaddara ba Fatima!"

A take ɓacin ranta ya gama bayyana kansa ta ɗago idanunta da zuwa yanzun suka fara zubar da ruwan hawaye tace.

“Ko da mafarki hakan ya kasance na tabbata ba zan yi zullumi ko ƙaddarar son wanin kaba!, Plsssss ka daina min ire-iren waɗannan wasar"

murmushin dake nan kwance saman fuskarsa ahar kullum ya saki

Yi hakuri wasa nake miki kawai na yi marmarin wannan fushin na ki ne, da tsoro kin san ni komai na ki burgeni ya ke, fushinki dariyarki duk ƙyau suke min, wani loƙaci idan ina gida ko stadio na kan ɗauki wayata nakan dauki loƙaci wajen kallon hotunanki, ina jin nishaɗin hakan sosae, Allah ya shiryaki min ke drama queen ". Sai a yanxu ya samu ta ɗan sassauta fushin dake saman kyakkyawar fuskarta tare da ƙawata ta da tarin farin ciki mara misalta, Cike da tsantsarn ƙaunarsa ta ce.
“Na san nafi ko wace mace a duniyar nan dacen masoyi, haƙiƙa ban yi kuskuren Zaɓenka a matsayinka na wanda zan rayu dakai ba, wani loƙacin na kan yi yunƙurin auna irin son da nake maka, amman sai na rasa silekin da zai dauki iya ɗaukar nauyin tarin son da nake ma, balle har na iya misalta kwatankwacin girman soyayyarka gare ni, sai dai ni kuma ina jin kamar akwai wata rana da son ka zai min illa, zai rufe idona na kasa gani a loƙacin da ganin yake da muhimmanci, ya maida ni kurma a lokacin da jin ke da matukar muhimmanci”

Wani irin azababben tausayin kansu da kansu ne ya kama shi, amma saiya ƙi barin hakan bayyanu gudun kada yaga gazawarsa da raunin dake kewaye da ilahirin gangar jikinsa.

"Rufe idonki"

Ya faÉ—a yana son kawar da wancen maganar data É—akko mishi.

rufe fuskar tayi kuwa da tafin hannayenta, sai ya ɗakko baƙar ledar dake gefensa ya mika mata.

“Bude idon ga zuciyar nawa nazo miki da ita"
Ya faɗa yana danna dariyar dake son kuɓce masa, dan yasan halin Fatima da shegen tsoro.
saurin bude idonta tayi jin tamkar ledar na motsi ne, wani irin razananniyar qara ta saki tare da wurgi da ledar dake hannunta. Atake ledar ta tarwatse saiga manyan kifaye suna ta mutsil-mutsil akan interlock ɗin dake shimfiɗe a tsakar gidan su. da sauri yaya Nurien dake fitowa ya ƙari so wurin da sauri jin uban ihun data saki. Yana zuwa bayyi wata wata ya fidda hannu ya ɗauketa da mari. Yana huce tare da faɗin "ke wacce iriyar mahaukaciyar zararriya yarinya ce ne?"
Wani irin azababben kuka ta saki tare da dafe saman fuskarta da take jin tamkar ba'a jikinta take ba tsabar raÉ—aÉ—in azabar marin data sha.

★★★

*ALIEY A*

lumshe luhu-luhun idanunshi yayi yana ƙara buɗe su, jin wayarshi na vibrating
bai buÉ—e idon ba, ya dauka Sannan ya manna a kunnesa.

"Ubangiji ya shirye ka ALIEYO, tafiya babu sallama babu magana kuma, babu cira hannu" aka faÉ—a daga cikin wayar.

A hankali ya tashi zaune daga kishin kiɗar da yayi yana kunna wutar ɗakin. yana jin wani yanayi, Tattaro nutsuwarshi Saida ya ɗebi wajen mintuna uku kafin daƙyar saman laɓɓansa ya furta.

"Jay I hope you are fine"
Shine kaɗai abinda ya furta domin sammm magana ba ma'abociyar yinsa bane. Daga cenñnn kuwa wanda aka ƙira da jay ɗin yace.

"Tsabar rashin mutunci ina tambayarka ka, amma kana ce min ina lafiya, a aahh bana lafiya, da bana lafiyar zaka jine ne banza miskilin tsiya"

Ɗan janye wayar yayi domin samm baya ƙaunar surutun da jay ɗin ke famar masa, tamkar zai fasa wayar ya fito.
"Ka gama"
Ya faɗi maganar yana datse ƙiran, yana komawa yadda yake wani irin kewar Sofeey ne ke taso masa, sammm a irin wannan yanayin baya da buqatar hayaniya, shi yasan ya yake keɓe kansa a killatancen wuri na daban. Duk ƙoƙarinsa nason kawar da tunanin dake neman addabarsa abin yaci tura, kansa ya jingina a saman sofar tare da lumshe Idonsa. Numfashi yake fitarwa Ahankali yayinda yake furta kalmar. " Innalillahi wa'inna ilair raji'un,² Ya hayyu ya qayyum" daga cikin bakinsa.

Ahankali nutsuwa ke sauƙar masa acikin zuciyarsa, yayinda yaji tarin damuwarsa na gushewa.sosea yaji sanyi da cikakkiyar nutsuwa da salama acikin zuciyarsa.
Gaban fridge bottle water ya nufa kai tsaye tare da ɗauko bottle water ya ɓalle murfin, ya kafa bakinsa Saida ya tabbatar ya shanye ruwan dake ciki tsabbb kana yayi wurgi da gorar. Wata iriyar ajiyar zuciya yake sauƙewa tare da sanya hannu ya dafe saitin zuciyarsa, duk yanda zuciyarshi taso sanya shi dogon nazari yaƙi aminta da hakan, haka kuma yaƙi bawa brain nashi daman yin tunani kamar yanda ya saba.

Ya jima a tsayen da yake kafin ya nufi bathroom, ya sakarma kansa ruwa. Ya ɗebi mintoci kafin ya fito jikinsa na faman ɗigar da ruwa, mini towel ɗin dake riƙe a dayan hannunsa na aikin tsanewa.
Wani farin trouser ya zira da t-shirt ita ma farar directly ƙasa ya nufa. Yana jin wani wasu irin abubuwa masu wuyar misaltuwa tattare dashi......

Shin mene yake shirin faruwa da rayuwar su Aliyu shureim ne da kuma queen teemahnsa?

Wannan wanne irin al'amari ne haka dake sanya ALIEYO acikin irin wannan tension É—in?

Shin yaya labarin zai kasance?, wanne irin tunani kuke game da littafin KAUNA BIYU?

Kunsan amsar tana ina?

Duka zaku sami amsoshin tambayoyinku ne a yayinda kuka biya kuɗin littafin ƘAUNA BIYU akan fara shi mai sauqi, ku biya ku mallaki naku domin ci gaba dajin daddaɗan labarin ƘAUNA BIYU.

ONLY 400# ta wannan account NO in.

3206656358
Maryam Nasiru
First Bank

Ko

8104493215
Opay
Maryam Nasiru

evidence via 08104493215 whatsapp only*

A gimtse 🫰

08104493215

*BY AMMEY LAYLERH ✍️*

*💘🌺ƘAUNA BIYU 🌺💘*

~Heart touching love, with love a side 🤍🤍~

Page 9&10

Last typing sai Allah ya kaimu bayan sallah 🤗

*BY*
*AMMEY LAYLERH*

✯ *~🌠 OFFICIAL MIRRAH 💫~*

نرجو أن يستمر الله سبحانه وتعالى في المشاركة في جميع شؤوننا
_____________
Chapter 6 · 0% Book details