← Book details Ƙauna Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 56

Sashe 29

Ƙauna Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daidaita zamansa yayi tare da zare hular kansa yana ajje ta gefe, Saida ya furzar da iska mai É—an zafi kafin cikin tsantsar biyayya a gare ta ya furta.

”Kin wuce duk waɗannan Abubuwan da kika lissafo a gareni Oummu Naaaaaa,umarni kawai zaki bani kai tsaye ba tare da kinsha wahala wajen tambayarta matsayin ki gareni ba!"

Wani É—an Lumshe idanu tayi kafin cikin kwarin gwiwa kuma ta furta.

”§O nake ka ƙira aliey a cikin daren nan nake son ganinsa a gabana a yau ɗin nan idan har da gaske na Isa dakai ɗin, kamar yadda kake ikirari ”

Wata zufa ce ta shiga karya kowa Abban cikin tsananin tashin hankali kuma yace. ”Oummuna duka fa wayoyinsa basa tafiya duk ya tare duk wata hanyar da yasan zamu neme shi Oum ”

”karka damu Muhammadu yanxu nan na gama waya dashi har ya gama zageni tasssss har da cemin munafaka muguwa algunguma , kai zagi dai babu irin wanda wannan tijararren yaron nan bai yimin ba yau”
A fusace Abban yace "shi alieyon ne ya zagemin ke haka?"

"Tasssss ma kuwa Muhammad" ta faɗa tana ƙara fashe masa da kuka. Jikin Abba har rawa yake wajen rarrashin Hajjo kafin ya katse ƙiran, yana dialing NO na ALIEY.

Yana tsaka da barcinsa Ring na woyarsa ya kuma tada shi, a fusace wannan karon ya janyo wayar da shirin ya bugawa wannan masifaffiyar hajjon worning, akan ta fita a rayuwarsa. Cikin rashin sani ba tare daya duba waye mai ƙiran na,domin samm ko a idon zuci bai taɓa zaton ƙira daga abban nashi ba ya manna wayar da kunnensa, cikin wannan dakakkiyar muryansa ya furta.

”Wai bana miki ki ƙyaleni ba, aike ba uwata bace da zakina bani umarnin kai tsaye, idan kuma kin isa saiki zo ki jani, ki dawo dani ki daura min auren!”
Ba tare daya bari ko hutawa yayi ba ya kuma faɗin, ”Saura kuma ki haɗani da ammiey ko Abba Wllh saina.......

”Saika kashe ta ko?”

Da wani irin bala'in ƙarfi yakai zaune yana gyara zaman wayar a kunnensa, jin Muryar da sammm bai kawo ta ko kicin lissafinsa, cikin Abba har rawa yake wajen furta.

”Ni idan na Isa dakai to ayau ba sai gobe b Ina son ganin ka a cikin ƙasar, tunda ita bata Isa dakai ba!, Ni data Isa dani ta bani umarnin Ni ma kuma ina mai baka umarni, dade da second ɗaya ban yarda ka ƙara ba mara kunyan banza kawai” kittt Abba ya yanke ƙiran

Sosai namomin jikinsa suga shiga rawar razani da tashin hankali, gumi kuwa tuni ga wanke shi sharkafff. Tsananin tashin hankali ya gama bayyana a tare dashi.

(Kai wannan tsohuwa anyi ƴar haddasa bala'i) Ya faɗa acikin zuciyarsa, Kafin kace A tuni harya shiga tattara tarkacensa dangin su system wayoyinsa sai kuma sauran muhimman abubuwan sa, xuwa loƙacin kuwa 6:15pm.

Tuni yayi boking na flight wanda zaije 9j kai tsaye, domin sammm a yadda yake cikin tashin hankalin nan baya jin zai iya tuƙi. Kasancewar sa sannan tuni har an kammala mashi komi cikin abinda bai wuce 15 minute ba Aka gama shirya masa komi.

Around 20 minutes
Sai gashi ya fito sanye cikin jallabiya gold color mai masifar kyau da tsada, Tsintsiyar hannunsa ɗaure da agogon Rolex, Jikin sa sai fidda ƙamshi tularensa yake mai masifar ƙamshi da daɗin shaƙa, fararen sawayensa sanye cikin Black cover shues masu masifar ƙyau da tsaɗa, fuskarnan babu ko ɗigon annuri a samanta, tafiya yake cikin hanzari abinda ba ɗabi'arsa ba kenan tafiya da sauri yana tafe yana duba watch ɗin dake ɗaure saman hannunsa ganin zaiyi lett flight nashi.

Tun da ya fito harabar hotel É—in escort É—in dake tsaron hotel É—in suka zagaye shi suna daidaita rantsatstsun motocin da zasu masa rakiya zuwa airport. A jere a kuma nutse lafiyayyun motocin ke tafiya suuuuuu suuuuuu suuuuuu akan shimfiÉ—eÉ—en titin dake luwai luwai. Cikin abinda bai wuce 10 mint ba sai gasu a cikin airport na Hamad International airport.
7:12pm jirgin sa ya lula daga New York zuwa ƙasar NIGERIA.

★★★

Duk inda ka gilma acikin harabar airport ɗin na malam Aminu Kano sojoji ne kawai ke kai da komo, Tamkar rana haka wurin ya kasance an zuwa wasu uban jami'amai tamkar wanda shugaban ƙasa ne zai sauƙa.

A cenñnn gida kuwa babu wanda yasan da batun zuwan na ALIEY kuma dama hakan ɗabi'ar sane, saidai kowa ya buɗe ido ya ganshi a washegarin ranar. Wasu shimfiɗaɗdun motoci ne guda uku suka ɗauke shi zuwa gida, Abba da har zuwa wannan loƙacin ya gaza runtsawa ne ya ɗage labulayen window na ɗakinsa dake upstairs, jin motsin taɓa get ɗin da get man yayi. Wata iriyar ajiyar zuciya ya sauƙe yana sakin labulayen tare da komawa yana kwanciya.
Wata nannauyar ajiyar zuciya mai ɗan qarfi shima alieyn ya saki, drictly part nashi ya nufa bathroom ya shige yana watso ruwa few minutes sai gashi ya fito ƙugunsa ɗaure da towel, sai kuma mini dake hannunsa yana tsane tattausan gashin kansa. Daidai saitin bangaren gefensa na hagu na gano wani irin azababben zanen tatto machine. Wanda aka yi sa cikin style Wanda da dukkan alamu zanen na haruffan suna ne, saidai sammmm na gaza gane ko minene ainihin sunan, domin da yaren Italiyanci ne akayi kun ga kuwa babu damar fahimta.

Washegari bayan duka sun gama hallaruwa a cikin dining area suna yin dinner na safe. Wani irin daddaɗan ƙamshim da suka san mutum ɗaya ne mamallakin sa ne ya bune baki ɗaya parlourn. Kafin Ahankali takun tafiyarsa ya fara ratsa kunnuwansu, tamkar wanɗanda aka ba umarni haka baki ɗaya suka juyo zuwa bangaren saman upstairs. Da wani irin gudu Amnah ta miƙe tana nufar papieyn ta sama ya cirata duk da baya cikin mood mai daɗi.

Cikin tafiyar nan nashi yaci gaba da tunkaro parlourn, zuciyarsa naci gaba da bugu, Amma ya danne hakan yaci gaba ta tafiyarsa xuwa garesu, wani irin wagaje baki Hajjo tayi tana miƙewa tsaye tare da faɗin.
”oyoyo na ɗan albarka, yaron kirki" ta faɗa tana sakin murmushi. Kallon ikon Allah Abba ya tsaya yi wato idan kace zaka shiga faɗan Hajjo da alieyo sai kaji kunya a take a gurbin guri, Shi kuwa nan gashi an barshi a sama jira yake Alieyn yazo yaci mutuncinsa.
Shi kuwa Boss In ma wani irin É—auke kai yayi ba tare da ko ya kalli inda take ba ya kauce mata, zama yayi tare da Amnah a jikin sa ya shiga gaida iyayen nashi, kadaran kada han haka suka amsa shi sosae ya damu ya kuma ji babu daÉ—i.

Bayan sun kammala breakfast in tsabbbb yana shirin tashi yaji maganar Abba kamar daga sama. ” daga nan inason ka zarce gidansu Jabeer ka gana da matar da muka ma”

Dammmmm haka gabansa ya bada sautin bugu, ji yayi zuciyarsa ta dunƙule waje guda ba tare daya ko ya iya cewa komi ya daga kansa yana ficewa a parlourn bayan ya ajje Amnah.

Cikin ɗaya daga cikin rantsatstsun motocin sa ya ɗauka har maƙalallun nashi zasu take masa baya ya dakatar dasu ta hanyar ɗaga musu hannu, cikin soft voice nashi ya furta musu.

”Hi guys wait for me at home, I'll be back”

Aikuwa Cikin bin umarnin uban gidan nasu suka juya zuwa cikin ƙaton harabar gidan, buɗe mai door ɗaya daga cikin securityn wurin yayi shi kuma ya sanya kansa cikin moton yana janta da wani irin mugun gudu.

_______*Ina zaune bayan mun kammala breakfast Alqur'ani ne a hannuna ina karantawa. Yaya Nurien ya shigo yace inada baƙo a sitting room, da sauri na ɗago ina binsa da idanuna da suka ciko da ruwan hawaye tare da faɗin.

”Ni! Kuma yaya?”

Kansa ya gyada min yana yin gaba sama da ten minutes na gaza koda motsa wa ne ganin bana da alamun tashi ne ya sanya ummie yimin magana, don dole na miƙe ina rufe Kur'anin, ba tare dako gyara fuskana ba na nufi sitting room namu jiki a sanyaye.
Da wani mayataccen ƙamshi na fara cin karo, ƙamshin dana rasa ina ne na taɓa jinsa, gabanane ya ɗan faɗi amma haka nayi ƴan mazanci na kutsa kaina cikin qaton ɗakin saukar baƙin mu.

Kyakkyawar sumar dake kwance saman ƙeyarsa ne ya fara min welcome, yana kishin kiɗe ya bada baya. Sallama na kuma yi a karo na biyu nan ma shiru, na buɗe baki zan kuma yin wata sallamar ya juyo baki ɗayansa.
Wata iriyar zabura nayi ganin mutumin da nake fatan ko a hanya kada ƙaddara ta kuma haɗamu, ina shirin barin ɗakin naji yasha gama na saurin rumtse idanuna nayi domin ban manta marukan da nasha daga gare shiba.

Ranƙofowa yayi kaina tare da dago fuskana cikin wani irin sautin daya nemi hautsinani yayi amfani wajen furta.
”Shawarar da zan baki itane kawai kice ke baki sona, domin kinsa ke bakiyi color da matan aure ba kibi komai a hankali, ki kuma saka a ranki wani ramin rijiyar yafi gaban tsallakawar yaro bane saboda faɗin bakin gareshi, kuskure kaɗan zaka iya afkawa ciki ka halaka”

A fusace Nimaaaaa.........

Hhhhhhhh tofa

Chakwakiya nidai kawai nace mu haÉ—e a page na gaba

*BY AMMEY LAYLERH ✍️*
*💘🌺ƘAUNA BIYU 🌺💘*

~Heart touching love, with love aside 🤍🤍~

Page 31&32

*BY*
*AMMEY LAYLERH ✍🏻♥️*

✯ *~🌠 OFFICIAL MIRRAH 💫~*

__________________________

___ Afusace nima na juyo tare da buɗe masa girman idanuna duka wai ko zai ɗanji tsorona LoL 🤩.
"uhummmm to da kyau amma kai mine zai hana kaje kace ka fasa a farke wannan ƙaddararren auren naka, ko anfaɗa ma niɗin ina sone uymmmm dubi ka gani a sanadiyar auren ka dubi yacce na koma!”
Tayi maganar tana ɗaga hijab nata. A take tsayayyun breast nata suka ɗan bayyana ta samar rigar ta, wanda ita harga Allah tayi hakan ne domin ta nuna masa yadda ta rame over. Saurin kawar da kansa gefe yayi yana wani irin taune ƙasar lips nashi da ɗan ƙarfi.
Tamkar wanda aka fusga ko irin ya kwato maganar nan yace.

”Da dukkan alamu harkin tsorata kenan? Tun ba'a je ko ina ba, ina mai ƙara baki shawarin ki sanja ra'ayin ki a kaina, domin Ni ba tsaren aurenki bane kana ina da wacce nake SO ki fashimta”
Chapter 29 · 0% Book details