← Book details Ƙauna Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 56

Sashe 12

Ƙauna Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A yau ranar Monday Aliyu shureim ya shirya tsabbbb cikin shirin tafiya Abuja, sosea yayi wani irin ƙyau fatarsa ta ƙara haske fiye da yadda ka sanshi, cikin shadda giztner milk color ya shirya inda shigar ta masifar yi masa ƙyau fiye da ko yaushe,ɗakin mahaifinsa ya nufa kai tsaye domin yi musu sallama, bayan sun gaisa yace.
"To Abba Mama ayafi juna zan tafiiiiiiiiiii" yayi maganar a raunacetare dajan fi ɗin sosea. Ajiyar zuciya mai qarfi Mama da sauƙe tare dacewa, "nifa Aliyu sai naji sammm tafiyar nan naka ya fita a raina, daka haƙura anan ɗin ma ai alhamdulillah babu ba sai kayi nesa damu ba!"
Shima ajiyar zuciyar ya saki yana jin baki ɗaya jikin sa yana neman mutuwa, amma babu yadda ya iya dole zai tafi ɗin ai dama. Cikin son ƙarfafa mata gwiwa yace. Babu komai Mamana Insha Allah!, ki sanya wa zuciyarki nutsuwa
kinsan tafiya da ƙarfen nasara babu tabbas ne acikin ta"
Kurrrrr haka Mama ta ƙure shi da Idanunta tanaji tamkar wannan shine kallon karshe da take masa. Abba ne yayi ƙarfin halin faɗin “Kin tsaresa da ido kuma kinƙi kiyi magana”. Shima cikin ƙarfin hali yayi maganar domin da gaske shima sammm bason tafiyar yake ba. Kodan shi kaɗai ne ɗa namiji garesu kuma bai saba irin wannan tafiye-tafiyenba ne Ohhhh.
Murmushi Aliyu yayi tare da cewa,
“mamana kodai na miki kyau ne?” yayi maganar again da murmushin nan kwance saman fuskarsa.
Jinjina kai Mama tayi still Idanunta na kansa tace.
“Sosai ma mai sunan manya sai naga kamar baka taɓa min ƙyau irin haka ba”. Murmushi yayi tare da Wara ido kana yace.
“Iyyeee yau Mamana ina kunyar da ake min dahar ake yabo na har haka”
Ummi kuwa still Idanunta na kanshi, fareedah data shigo gidan yanxu ne jin kamar maganar mamansu da kuma Æ´aÆ´anta ne ya sanya itama ta shigo É—akin,Ta kalli mamansu kana ta kalli yaya Aliyu shureim data tsirawa Idanu matsawa kusa da Maman nasu tayi tare da cewa.
“uhummmmm yaya Aliyu ɗan gata duk su Abba sunfi sonka akaina, to danma ai ka kusan tafiya ka barni daga Ni saini kaɗaina, kaga shike Nan sai nayi yadda nake so Nima a gaban su".
Sai'a sannan Ummi ta É—auke Idanunta daga kan Aliyun tare da mayarwa kan fareedan. Kallon fareedan Aliyu shureim Yayi tare da cewa.
“fareederh”
Cike da ladabi ta É—ago kanta kana tace.
“Na'am Yaya Aliyu Naaaaaa”
Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da cewa.
“dole ai dama koba ki ce na tafin ba zan tafi dole fareedatu, zan tafi nabarki dake sai su Abba da Maman.
Cikin yanayin damuwa fareedah tayi ƙasa da kanta lokaci ɗaya Idanunta suka ciko da hawaye yayin da taji zuciyarta yana masifar bugawa da ƙarfi tace.
"Nufa yaya da wasa nake maka, wllh nafi buƙatar kullum kullum nayi ta ganinka, domin kai kaɗai ne gata ne, kaine babban yayan da nake alfahari dakai, nufa ba irin wannan tafiyar nake nufi ba, idan kayi auren nefa nake nufi yaya Aliyu!, inason mu kasance a tare muyi kukanmu tare muyi farin cikin mu tare, kamin aure kamar yadda kasha faɗin cewa kaine zaka aurar dani ɗin, babban yaya."
Aliyu kuwa murmushi yayi tare da kallon fareedan kana ya cije labɓansa na ƙasa, tare da lumshe idanunsa yana sauraron bugun zuciyarsa, ajiyar zuciya ya sauƙe tare da buɗe idanunsa akan fareedan kafin yace.
“To ai ita rayuwar dama ƴar haka ce fareedah koda baki ce na tafi Ni san zan tafin"
Girgiza kai Mama tayi tare da kallon Aliyu cikin yanayin tsinkewar zuciya tace.
”wai duk mine ya kawo hakan ma Aliyu? don Allah duk Abar maganar Meyesa kake karya mana zuciya ne!?”.
Girgiza kai Aliyu Yayi tare da kallonsu wani irin tausayinsu da kuma ƙaunarsu na ratsa dukkan zuciyarsa, Iska mai zafi ya fesar daga bakinsa kana yace.
“Ba karya zuciya bane Mama Naaaaaa" ya kuma jannn n ɗin

A hankali Abba ya ɗaga idanunsa tare da kallon Mama da ta tsirawa Aliyu idanu cikin wani irin yanayi ko ƙyaftawa bata yi ajiyar zuciya ya sauƙe kana yace.
“Allah Ubangijii ya kare ka da kariyarsa, Allah ya bada Sa'a Aliyu shureim Ubangijii ya sauke ka lafiya, ya bada Sa'ar zuwa" yana faɗin hakan ya fice a ɗakin da sauri domin wasu irin al'amurra masu girman gaske daya gano dan gane da yaron nashi, kiris ya rage zuciyarsa ta fallasa asirin dake birnin cikinta. Wannan shine ma dalilin daya sa yabar ɗakin cikin sauri. Yana fita wasu wahaye masu zafi duka zubo masa, da sauri ya sanya hannun da yana sharewa.
Ahankali Aliyu ya maida kansa jikin kujerar da yake kai ɗin ya jingina, kana ya miƙe ware lumsassun idanunsa tare da kama hannun fareedah cikin nasa kana ya cije lips ɗin sa. "Ga Amanar ƴar Amana na Nan na bar miki ki kula min da ita, fiye da yadda zaki kula da taki rayuwar!, ki kula min da ita har zuwa sanda zan dawo, ko sau ɗaya kada ki taɓa barinta ta zubar da ruwan hawaye ata dalilin rashin..... Da sauri Mama ta rufe bakinsa da hannuwanta, wani irin sanyi jikinta da zuciyarta keyi cikin wani irin yanayi ta zubawa Aliyun Idanu. Anutse Aliyu ya buɗe Idanunsa dake lumshe ya sauƙe akan mama. Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da furzar da iska daga bakinsa kana yace.
“mama ya dai kike rufe bakin haka kika sani ma ko maganar ƙar.....
Cikin saurin Mama ta dafe ƙirjinta daya buga da ƙarfin gaske cikin raunin murya irin na wanda ke gab da zub da hawaye ta kallesa cikin tsananin rauni tace.
“Haba haba Aliyu ya kake mana haka karfa ka manta yau saura kwanaki biyar AURENKA kaida queen ɗinka, amma kake mana irin waɗan nan maganganun!, tamkar bai barin wasiyya”.
Wani irin murmushi ya saki me ɗan sauti yana cewa, "Mama to ita rayuwar nawa take ma, hmmmmmmm" kawai yaja ajiyar zuciya domin wani irin bala'in bugu da yaji ƙirjinsa nayi tamkar me.
Mama kuwa lokaci É—aya wasu hawaye masu masifar zafi suka fara bin kuncinta, domin Sakk irin Maganganun da yake faÉ—a mata cikin mafarkanta na Æ´an kwanakin nan.
Cikin yanayin tashin hankali Aliyu ya sauƙa tare da ƙara sawa gabanta ya durƙusa tare da riƙe hannun ta cikin sanyin murya yace.
“mamah kiya femin kiya femin kada ki zubar da hawayenki akaina, me ne nayi miki! dana chanchanci zubar hawayen ki akaina?”.
Damƙe hannunsa Mama tayi cikin raunin murya da alamun tashin hankali tace.“Meyesa kake karya min zuciya nida mahaifinka da ƙanwarka gata nan".Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da yin murmushi yayin da Idanunsa ke sheƙi kana yace.
“Toh yazanyi mamah inada ikon sanja ƙaddarata ne? dole nasan ƙaddara zatayi aikinta, kuwa ruwa, iska, tsanani babu wanda ya isa sanja ƙaddarar dake manne acikin zuciyarsa, da ina da dama da nine mutum na farko wanda zai fara sanja ƙaddararsa daga mummuna zuwa kyakkyawa.
Girgiza kai Mama tayi still Hawaye nabin fuskarta tace. "Babu babu babu Aliyu!, ina tsoron abinda zai faru dakai ne kawai, gaba É—aya kwanakin nan in yawan mafarkai akan ka Aliyu Naaaaaa marasa fasali, marasa kan gado"
”cike da matsanancin mamaki ya dago kansa jin ashe Mahaifiyarsa itama na ire-iren mafarkan da yake yi akan kanshi.amma saiya danne hakan gudun kada ya kuma tada wa mahaifiyarsa hankali, cikin sassanyan muryansa da tayi sanyi sosai yace. "Mamah Naaaaaa kimin adda'a da fatan Alkhairi zan tafi loƙaci na ƙara ƙurewa" kafin ya dubi fareedah data kasa koda kyakkyawanr motsi ne murmushin itama ya sakar mata tare da cewa "ki cika min alƙawarin da nabar Miki fa"
Cikin ƙarfin hali tace "I promise you yaya nayi alƙawari" tare da ɗamke Hannuwansa ta daura akan Ƙirjinta, sasea yaji yadda zuciyarta ke bugawa da ƙarfi, sai kawai ya sakar mata kyakkyawarn murmushin nan nasa yana turkusa gaban mahaifiyarsa. "Ki min addu'ar Mama ki yafe min duk wasu abubuwa dana aikata Miki na rashin daidai, danne zuciyarta dake Zillo tayi, nan ta shiga masa adda'oin neman tsari da gamawa da duniya lafiya, da nema masa gafarar Ubangijii.

Murmushi yayi cike da jin daÉ—in Addu'ar ta ya shafa sajensa, bayan ya amsa mata cikin farin ciki sai yake jin kansa sakayau tamkar É—an jariri sabuwar haihuwa.
Sosai fareedah ke dariya tana jin ƙaunar Yayan nata, miƙewa yayi tare da yiwa mamah Sallama kana ya fice bayan tayi masa Allah ya tsare.

Kai tsaye gidansu queen teemah ya nufa cikin nutsuwa kai tsaye ya tura ƙofar get ɗin. Shiru babu kowa, harya zaro wayar sa da nufin qiran ta sai kuma kawai ya fasa yana sanya kansa cikin gidan. Saida yayi sallama ummie dake zaune a parlour ce ta amsa sallamar tana faɗin. "Shekarau sai yau akaga damar shigo mana keñan, shigo wa yayi tare da ɗan shafa sajan sa yana cewa, ”Amin afwa ummienmu na daina daga yau insha Allah” ɗan murmushi tayi tare da faɗin. "Allah ya yarda Aliyu" acen qasan zuciyarsa ya amsa da ameern. Tsammm ummie ta miƙe tana faɗin bara na turo maka fatiman, "TO Ummienmu" yace yana jin ƙaunar ummien har cikin ransa, domin shi samm bai ɗauke ta a matsayin surukuwa ba a matsayin mahaufiya yake ɗaukarta.
Babu daɗewa saiga mutuniyar taku cikin zumbulelen hijjab ɗin, zama tayi dab da shi tana tonƙoshe ƙafafunta, idanunsa ya zuba mata waɗan da suka ɗan sanja launi.
Chapter 12 · 0% Book details