← Book details Ƙauna Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 56

Sashe 31

Ƙauna Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dining ɗin babu kowa sai iyaka Anum data kafe sa da Mayun idanunta tamkar ta cinye sa danye, barka da dare ta mishi amma ko kallon inda take baiyi ba, zama yayi kan ɗaya daga cikin kujerun dining ɗin, ganin ya zaune ne yasa anum saurin jawo pilet tana shirin sarving nashi. Yatsunsa biyu ya ɗaga mata tare dayin ƙasa dasu alamun ta barshi keñan, cike da mayen son dake ɗibarta gare shi cike kuma da kissa cikin sexy voice ta furta.

”LIEYOH! What's wrong with me?and all the things that you do not understand and do not understand, why LIEYYYY?”

Tamkar ya shaƙeta haka yake ji saidai sammm bazai iya hakan ba, shifa a rayuwarsa ya tsani mace mara kamun kai, da bayan mutuwar SOFEEYERH ita aka so aure masa, amma rawarn kan yarinyarn da kuma rashin ajinta yasa sammm yaƙi aminta da batun, wanda hakan harya kaisu ga samun saɓani tsakanin family nasu, akan hakan har matsala ya samu tsakanin Abbansa da kuma ammieyn. Tun daga loƙacin kuma basu kuma masa batun aure ba sai akan wannan.

A hankali ya miƙe yabar kan dining bayan ya kammala shan coffee ɗin fuskar nan a tamke, parlourn ciki ya koma yana zama kusa da Irfan kan 3 sitter wanda shikuma Irfan yana kan 2sitter yana pressing phone nashi,

Da wani irin kallo tabi bayansa tana kammala yin dinner Sannan itama ta miƙe tana dawowa parlourn samun wuri tayi ta zauna kusa da Irfan, hannu Anum tasa ta buɗe ledar dake gaban Irfan ɗin. wanda amfanin da yake da wayarsa ne ya ɗauka hankalin har haka,kayan ciye ciye ne gasu nan chips, bugger sai kwalayen picanto, dominos pizza shawarma da sauran wasu tarkacen kayan maƙulashe, Sai ɗayar ledar dake ɗauke da fried meat (tsiren nama) da yaji kayan haɗi sai uban ƙamshi yake yi, miyan bakinta har tsinkewa yake wajen buɗe ledar baki daya ba tare da neman izini ba ta fara antayama cikin ta.

Tsammm ya miƙe yana nufar upstairs nashi tsaye kan windown na ɗakinsa Ahankali ya furzar da iska mai zafi abakinsa, yana jin sammm babu daɗi acikin ransa. A hankali yabar jikin window'n yana komawa kan hadadden gadonsa yana kwanciya flat wasu irin abubuwa masu girman gaske na kai da komo acikin brain nashi,

Sai yanxun ma na lura da irin gyare gyaren da aka kuma ƙawata bedroom ɗin dashi, baki ɗaya ɗakin ya ɗauki wani irin azababben kamshinsa tuni ƙamshi da kuma sanyin A/ CN dake ratsa shi wani irin daddaɗan barci yayi awon gaba dashi.

Mutuniyar taku kuwa Hajjo hr zuwa loƙacin tana gidan domin dama tace bata tafiya har sai anyi bikin Shalelen ta, ɗaki ɗaya duka tare da MAH wanda akwai tsohon ƙawance dama tsakanin su tun na ƴen matanci, kasancewar mahaifin su hajjo ɗin irin me kuɗin nan ne yake ɗaukar family nashi suje ƙasar Madina suyi hutu, hajjo kuwa daga ƙarshe ma Acen tayi karatun ta, wanda shine har suka aure suna raya zumuncin dake tsakanin su, duk kuwa da cewar suɗin ƴaƴan sarauta ne.
Ahaka ahaka ana tafiya harya suka kai ga suma sunyi aure sun hayayyafa har takaisu haÉ—a zuriya, domin ita ammien Æ´ar cikin masarautar garin Madina ce Æ´ar sarki YOUSOUF Jikar Sheikh Abduljabbar.

Wannan keñan.

Bangaren amare kuwa ciki da woje Mama ke gyaran su, a hakan ma Saida taci uban ta kana ta amince ake gyara tan, takanas Mama ta ɗakko AUNTY AISHA ALIYU GARKUWA take tsuma ƴaƴan nasu cike da woje da irin haɗaɗɗun maganunnuwanta irin nasu sanyi, gyaran breast, na ƙarin sha'awa, na saƙko da ni'ima nan take haka dai aunty aysha Aliyu garkuwa ta shiga gyaransu Queen da fareedah, ko ganinsu ba'a yi duk wani shige da ficen daya kamata ƙawayensu ne ke zirga-zirga tsakaninsu. Gashi yau sora kwanaki uku cifff bikin ta kama yau muna Laraba keñan. Aunty zeey kuwa tun sati biyun bikin ta diro kafin daga baya yaya jay shima ya biyo jirgin ya dawo.

__________★★★___________

Malam bahaushe ya kance rana bata karya saidai uwar É—iya taji kunya, Masu iya magana kance da sannu sannu ana tafiya saidai a daÉ—e ba'a jeba, to sai gashi yau Allah ya kawo mu É—aurin auren Aliey da kuma queen fareedah da yaya Nurien.

♥️🤍♥️

Hayaniyar da kuma surutan dake ɗan tashi sama sama ne yasashi ɗan buɗe lumsassun idanunsa tare da yunƙura wa yana tashi zaune Acen ƙasar zuciyarsa ya furta.
(Shi keñan yanxu babu damar mutum ya sake, abin ma sai yakai ga anbiyoni har ɓangarena!)

Yar ƙaramar tsoki yayi domin yasan cewa, idan ba hajjo da kuma Oum Anum babu wanda ya isa shiga masa bangarensa, dan ko Anum ta san mine take yi dade da wasa bata taɓa gigin shigo masa koda parlour bane.

Saƙƙowa daga kan gadon yayi tare da wucewa cikin bedroom nashi kai tsaye, yana tsakar ma kansa shower, Saida ruwan ya dake shi sosae kana ya tara ruwa acikin bathtub wanka yayi sannan yayi brush, duk da cewar kuma yanajin yunwa sosai amma bayajin zai iyacin wani abinci, domin shifa komi tsaya masa yayi cakkk tunda aka fara hidimomin bikin ya killa ce kansa babu ma wanda ya gana bare a dame shi, saima wasu daɗan waƙoƙin ɗaya ringa bugawa wajen guda uku.

Ahankali ya murɗa handle na ƙofar bathroom ɗin toilet ya fito, jikinsa sanye da white bathrobe.

# Turus haka yaja ya tsaya yana ƙarewa mutanen dake Zazzaune zama irin na sarauta da kallo

# MALEEK TOUFIQ, na cikin littafin KAREN BANA, na AMMEY LAYLERH
# JALAAL AREEF na cikin littafin (JALAAL AREEF) na AMMEY LAYLERH ABDULMALEEK KUWAIT {AK} Na cikin littafin MIKIYA shi ɗinma dai nawan ne Ni AMMEY LAYLERH ✍️ {REAL MIRRAH 🫰 Sai kuma yaya jay wanda ya kasance babban abokin ango, kana kuma yayan ango

Inda ko wannen su yake sanye cikin rantsatstsun shiga ta alfarma, ta masu juya masu gidan rana.

Murmushi mai taushi MALEEK TOUFIQ ya sakar masa tare da tasowa ya ƙaraso kusa da shi Hannunsa yasa yaɗan bugi shoulder na Alieyn.

Cikin yanayinsa na wanda bai saba magana ba yace.

”Congratulations dude”
Kawar da kansa gefe yayi yana mamakin ta yadda akayi suka san da batun auren nashi,
(jay É—in ka)
Zuciyarsa ta bashi amsa kai tsaye,hakan yasa yayi saurin kallon sashen da yaya jay É—in ke zaune, murmushi ya sakar masa tare da gaÉ—a masa kai alamar aikin sane wannan É—in.

Cikin farin ciki JALAAL AREEF ya
Taso cikin hanzari ya jawo Alieyn É—an sauri yana faÉ—in.
”Hurry up and get ready, we don't have time malam”
JALAAL AREEF ɗin ya faɗa daidai yana daidai tama Aliey tsaiwa gaban ƙaton mirrorn ɗakin.

Shi kuwa AK tunda suka fara maganar su A bai tsoma tasa ba, domin duk yadda kuke tunanin zafin zuciya taurin rai irin na Aliey wannan ubansa ne a komai ma, Kuma sau biyu suna haɗa ido ko wannen su ya basar LoL 🤗 Ni kuwa AMMEY LAYLERH nace wannan wanne irin abu ne lafiyar zuciyarsu ƙalau kuwa?.

Ganin yadda suka tasa shi gaba ga kuma yadda suna tsatstsare shi da idone yasa babu yacce ya iya haka ya shiga gyara jikinsa, Bayan ya kammala ne kuma ya gyara beautiful beard ɗinsa da kuma tarin tumilin sumar dake kwance saman kansa, wacce ya fake ta a ƙeyarsa.

Haɗaɗɗun tsadaddun tularukansa ya shafa ganin kuma yana shirin shigewa cikin closet na kayansa ne zai ɗebi kaya, yasa yaya jay saurin miƙa masa set ɗin wata haɗaɗɗiyar white getzner da aka killacesa cikin wani haɗaɗɗenn kwali.

”Just accept it and complain later”

Ya jay yayi saurin tararn numfashinsa domin yasan kaɗan dag cikin aikin alieyonsa ne yaƙi sanya kayan. Ganin irin roƙon da jay ɗin nasa ne masa ta ƙasan idanune ya sanya shi amsar kayan jiki a sanyaye.

ÆŠan kallon jay É—in nasa yayi Kamar zaice wani abu saiya fasa kuma, tare da komawa cikin clothes nashi.
Lumsassun Idanunsa da yau dama yake jin su kuma sauya yanayin su ya ɗan lumshe saboda ganin wata haɗaɗɗiyar getzner da aka ƙawata ta da ɗinkin riga da wando sai kuma babbar riga, wanda akayima irin wani fitinannen aiki da aiki na musamman.

Jiki a mace ya miƙe ya fara shirya kansa cikin wannan rantsatstsiyar getzner nan

Yah Ilahi ba ƙaramin kyau kayan suka masa ba wanda shi kansa saida yaji hakan ajikinsa. Aikuwa kyawun nasa bai sake bayyana ba saida ya mirza wata haɗaɗɗiyar hulan dake matsayin ta kayan me ratsin blue colour still itama. Black socks ya sakama fararen ƙafafunsa, tare da zura wasu haɗaɗɗun classic shoe sauki ciki masu kalan blue suma. wanda suka kuma bayyana haɗewarsa da kuma kyaun kwalliyarsa.

Still ya kuma janyo wata tsadaddiyar rolax yana É—aurawa saman tsintsiyar hannunsa.
Sassanyan turaren ya É—auka yana kuma feshe jikinsa, shima harya gaji da wannan abubuwan domin kuwa hakan ba karamin takura sa yayi ba.

Kyawawan idanunsa ya É—an lumshe jin yanayin bugun zuciyarsa naci gaba da sauyawa, Ahankali ya shiga tafiya da takunsa mai cike da tsantsarn izza yana fitowa cikin parlourn.

Wani irin fitinannen ƙamshinsa daya daki hancinsu su maleek ne kuma yasa duk suka maida kallonsu ga kofar bedroom ɗin harda AK da sai yanxun ya ɗago yana ɗaura idanunsa masu launin madara akan Alieyn, cikin yanayin isa da kuma izza tsammm ya miƙe tsaye cikin taku ɗaiɗai ya nufo Alieyon, cikin tsantsar zallar miskilancin sa tare furta

”Wow Masha Allah”

Ya faɗa yana ɗan rungumo sa zuwa cikin jikinsa kansa ya ɗago wanda sai a loƙacin sukayi ido biyu dashi, ɗan murmushin gefen baki ya sakar masa yana ɗan buga bayansa cikin cool voice nashi ya furta.
”Thanks eagle”

Hannunsa ya kamo tare da yima su maleek alama akan su tashi su tafi, haka suka fito gaba É—ayansu kowannensu kallo É—aya zaka masa kasan cewa kuÉ—i da Hutu da kuma kyau na kai musu.

Cikin Wata haɗaɗɗiyar Bugatti Chiron blue black suka shiga, shida yaya jay da AK ne abaya, sai maleek da kuma Jalaal areef dake gaba wanda shine zai driving nasu. Sai kuma motocin escort nashi dama na sauran abokansa suka rufa musu baya, yadda kasan shugaban ƙasane a ciki haka narkakkun motocin suka jera suna tafe a tsari, bakajin ƙaran komi saina gittawarsu suuuuuu suuuuuu suuuuuu shine kaɗai abinda kakeji a shimfiɗeɗen titin.
Chapter 31 · 0% Book details