← Book details Ƙauna Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 56

Sashe 20

Ƙauna Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

”don Allah yaya Vijay da gaske kake?” queen ta faɗa tana marairaice, murmushi aunty zeey ta saki tana faɗin ”idan baki shirya ba mu saimu wuce ai ko julay” tayi maganar tana kallon julaibeeb dake riƙe da hannun baban shi. Rungume aunty zeey tayi cikin farin ciki tana faɗin, ”wllh nasha da wasa yake min rabona da zuwa shop harna manta wllh”. Kafin ta sake ta ta nufi ɗakinta a guje cikin mintunan da basu gaza biyar ba sai gata ta dawo cikin shirin fita, inda ta sanya riga da wando na Pakistan ire-iren waɗannan yaya jay ɗin ta ya siyo mata a India.
Sallama sukawa ummie suna fita coumpaund na gidan suna daukar hanya.
A wani ƙaton plaza A&A motarsu yayi parking, kana kallon wurin zaka san ba wurin zuwan kowa da kowa bane, kasan sai wane da wane sai wanda yaci yasha kana ya tasa kai ne kaɗai keda hurumin shiga cikin plaza ɗin. duba da irin rantsantstsun motocin dake fake, da kallo kawai queen kebin wurin da kallo domin ita dai tasan bata taɓa zuwa wurin ba, iyakarta shoprite dadai sauran wurare. Dab da wata narkyakkiyar Bugatti Chiron suka faka motarsu, a nutse suka fito yaya jay yana ɗaukar julay a kafaɗarsa, cikin girmamawan dake nuni da alamun sanayya tsakanin sa da ma'aikatan suka suka gaisa, suna shiga cikin hasalin plaza ɗin. A take cikin queen ya bada sautin ƙugi, ganin uban jami'an dake kewaye da wurin rike da manyan bindugu a hannunsu.
Wani abu kaɗai da bansan miye ba yaya jay ya nuna musu, a take cikin girmamawa suka yi solid na yaya jay tare da basu hanya bayan an jona musu na'urorin gwaji, kafin su keta cikin ƙaton plaza ɗin. Garin kalle kallenta su yaya jay suka ɓacema ganinta. Tana rike da ɗan keken da take dibar duk abinda ya mata. Bakinta ta ɗan tura gaba tana ƙunƙini ita kaɗai, tare da soma tafiya tana bin gefin dogon benen dake da tsayi da zurfi kenan.
Rolex ɗin dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa ya yake dubawa a nutse, don ƙa'idar sace yin komi akan loƙaci tamkar yanda ya gindaya konace yari ga ya tsara ma Rayuwar sa yin komi akan time nashi, don aganinsa bashi da loqacin ɓatawa loqaci loqacinsa, komi yana yinsa ne akan loƙaci sa ba tare da wani ya shiga cikin woni ba, donshi mutum ne mai tsananin bin kowacce ka'ida acikin dukka lamuransa.
Wasu haɗɗaɗu kuma tsadaddun track Suit ne a jikin sa blue black, sai SKY blue denim jacket daya daura a saman tsadaddun suit ɗin, ƙafafunsa sanye da wasu tsadaddun white sneakers shoe.
Baisan da xuwanta ba kawai dai yaji an bangaje shi. ganin ba tare da antsaya ko an bashi Haƙuri bane ya sanya ƙafarsa tare da farɗo ta baya.
wani irin gigitaccen ihu ta saki wanda ya janyo hankalin duka jama'ar dake ƙasan benen, sammm baiyi tsammanin ƙasan zataji ba hakan ya sanya cikin sauri ya sanya hannunshi ɗaya ya sanya tallafi daidai kanta, ɗayan hannunshi kuma yakama daidai waist nata yana janyota, kai tsaye saman faffaɗan qirjinsa ta faɗa wata iriyar ƙatuwar ajiyar zuciya ta sauƙe loƙacin data jita jikin mutum, hakan yasa ba tare data tantance ko waye ba ta sanya duka hannuwanta biyu tana zagaye ƙungunsa tsammm, tare da ɗaura kanta saman ɗamtsen hannunsa.
Baki ɗaya jama'ar da suka bada attention nasu a wurin suka shiga sauƙe ajiyar zuciya , donba ƙaramin faɗuwa zatayi ba inda Allah bai kiyaye ba,Ciki kuwa har da yaya jay da kuma aunty zeey.
Ahankali yazare hannunshi daga kan waist nata yana yanyeta a jikinsa tare da tsayar da ita akan qafafunta, idonsa kan fuskanta yana kallon yanda ta ƙanƙame idanunta gam gam cikeda tsoro pink lips dinta nawani irin shaking dayasa dimples nata na lomawa da ƙyar ya motsa motsa lips nashi wajen furta, ” You again?”
Muryan dataji yadaki dodon kunnuwanta yasanta buÉ—e idanunta don gasgata muryanrn data riga ta zauna a kanta daram tamkar wacce aka naÉ—e muryan a tsakar kanta.
idanun nan nata manya masu kama dana mage ta shiga buɗewa akan kyakkyawar fuskanshi ta sauƙe ganinta, jitay numfashinta ya makale ganin fuskanta dab da nashi ya zuba mata wannan firgitattun idanunsa yana kallonta.
Cikin jin tsanar rashin kamun kanta ya ɗauke saman kyakkyawar fuskarta da kyakkyawanr mari, cikin takaici ya furta. ”You are the one who knows the donkeys, and is calm and self-controlled”. da azabar ƙarfi ta dafe saman fuskarta tana sakin wani irin raunataccen kuka, a kuma daidai loƙacin Amnah dake tare da ammiey suka iso wurin.
Dai su yaya jay na ƙarasor suma cikin sauri ammiey ta tallafi queen tare da shigar da ita jikinta. Cikin kulawa ammiey ta ce ”Hi Stop crying,what happened to you?" Kanta ta shiga jujjuyawa a jikin ammien tana kuma sakin wani kukan, Amnah da sai loƙacin ta kula da ashe Fatima ce ta ƙarfi tace, ”laaaaa waye ya saka new Mamie na kuka na haɗa shi da papieyna ya rama mata ammiey?”
Ta ƙare zancen da tambayar ammeyn, papieyn nata ammiey ta nuna mata tana cewa ”He is ganan a gabanki” ta faɗa a fusace tare da kama hannun Fatiman tana yin wurin motarnta da ita cikin wani irin mugun ɓacin rai.
Da sauri yaya jay yabi bayan ammiey da sauri shida aunty zeey. Kama hannun papieyn ta tayi tare da cewa ”da gaske papiey kaine ka doke ta new m… ”AMNAHHHH” ya faɗa cike da wani irin mugun tafasan zuciya yana dunƙule hannun sa tare da kaima iska naushi yana surarta a fusace. Coumpaund na plaza ɗin ya nufa cikin rawar jiki duk inda ya ratsa sai kaga masu tsoron plazan na rusunar da kansu cike da girmamawa. Yana zuwa parking lot motar ammiey na barin wurin, luuuuuu idonsa yayi kafin ya buɗe da tsananin ɓacin ran ganin akan wannan ballazar yarinyar ammien shi tayi fushi dashi, ta tafi ta bar shi.
Wayarsa ya ciro yana dialing wata NO, ko mint 1 ba'ayi ba ɗaga daga cikin soldier's ɗin nan ya kawo masa car key na motor jiki na rawa, fisge key na motorn yayi a fusace tare da nufar wata sabuwar bakar Benz yana faɗawa ciki tare da mata key yana janta da wani irin bala'in gudu.da sauri Amnah ta ƙamƙame jikinta wuri guda tana rarraba idanu ganin yadda yaja motar da mugun gudu.
Cikin ƙankanin loƙaci ya isa gida a haukace ya shiga dannawa me gadi hong, wanda yasa a firgice get man ɗin tashi yana wangale ƙaton get ɗin, da sauri yaja baya ganin tamkar aliey zai yi ciki dashi. Ko gama daidaita parking baiyi ba a matuƙar zuciya, dade da Amnah baba

*💘🌺ƘAUNA BIYU 🌺💘*

~Heart touching love, with love a side 🤍🤍~

*🌠OFFICIAL MIRRAH 💫*

*WRITING*
*AMMEY LAYLERH ✍🏻♥️*

Page 21&22

*Alhamdulillah forever and always 👏*

Wannan page in sadaukarwa ne gareku my fans nawa allah yabar ƙauna 🥰🥰🤎

________*
_________★★★_______

♥️🤍♥️

Baba mai gadi ne ya fito da ita. Cikin ƙunar zuciya yake taka step bibbiyu ko ganin gabansa baya yi tsabar bala'in ƙunar zuciyar sa ke masa.cikin tafiyar sassarfa yake nufar upstairs nashi, yana shiga bedroom ɗin ya fesar da wata zazzafar iska daga cikin bakinsa, har yanzu bibbiyu yake kallon komai yana jin yadda bedroom ɗin ke jujjuya masa.
Lumshe rinannun idanunsa yayi domin har zuwa yanzun itane acikin ƙwayar idonanunsa, yana jin yadda zuciyar sa ke yamusta masa, idan harya hasko yadda ta wani zagaye ƙugunsa ta kuma kwantar da kanta saman ɗamtsen hannunsa, ji yake tamkar an rura masa wuta ne ne a cikin zuciyarsa ne.
Kana yana yin yadda zuciyarsa ke harbawa da masifar ƙarfi ne yasa, ya wani irin taune ƙasar laɓɓansa da ƙarfin masifa.
Domin kuwa har yanzun ya gaza mantawa da haɗuwarsu na farko, yadda ta faɗar masa saman jiki, ta wani cukuwkuye shi. Sake rumtse idanunsa yayi sakamakon yanda yaji zuciyarsa ta bala'in buga da ƙarfin masifa.

Sosai wannan karon ya buɗe rikiɗaɗɗun idanunsa da har zuwa yanzun suke ganin komai dishi dishi, kai tsaye bedroom yana haɗa ruwan wanka acikin babban jakuzzie me tsananin sanyi,wai ko hakan zai sa yaji sassaucin ƙunanr da zuciyarsa ke may. Sassanyar ajiyar zuciya ya saki loƙacin da yaji ruwan sanyi na ratsa gaɓɓan jikinsa. Shiru yayi yana sauƙe ajiyar zuciya akai akai tamkar irin wanda yayi gudun wasan tseren nan.
Koda ya fito daga bathroom ɗin kuwa wani farin towel ne ɗaure akan waist nashi,yayin da gaba ɗaya gargasan jikinsa suke a mimmiƙe, Cikin takunsa me ɗauke da wata iriyar izza da kuma zallar ƙasaita ya shige cikin clothes nashi. Da sunayen Allah cikin bakinsa da yake ta faman jerawa, maida idanunsa yayi yana kullewa tare da ware su wanda kuma hakan alamace dake nuna cewar ya sami cikakkiyar nutsuwar da yake buƙata......
Chapter 20 · 0% Book details