← Book details Ƙauna Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 56

Sashe 45

Ƙauna Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"FATEEMERH!" Ya ƙira sunanta cikin wata irin sillent voice ɗinsa dake bayyana tsananin ƙaunar ta, "kinason zuwa ganin ummien mu ne?" da sauri ta daga masa kanta cikin tsantsar farin ciki " To shikenan zuwa anjima ki shirya saina kaiki" da wani irin farin ciki ta saka hannayen ta tana cukuwkuye jikinsa,kafin ta sakar masa wani zazzafan French kiss a gefen wuyansa, idanunsa ya lumshe yana jin yadda miss 😘 😚 ɗin ke ratsa ko ina na jikinsa.
Zame wa yayi yana kobciya tare da É—orata saman ruwan cikinsa, sexy eyes nashi ya zuba mata yanajin wani irin abu mai kama da magnet na fusgar shi zuwa gare ta.
Cikin zumuɗi ta tashi a jikin sa tana yin plate ɗin su ammiey, ammiey na tsaka da aikinta queen ya faɗa cikin parlourn ganin bata parlourn ne ya sanya ta binta kitchen domin ta jiwo motsinta a cenñnn. Cikin matsanancin farin ciki tace Ammiey ina angle har yanxun bata ba'a taso suba?"
"Kin san dake yanxu ka'in da na'in sun koma karatu keda ganin Amnah kammm sai goshin magrib"
Dan marairaice Idanunta tayi tare da furta.
"Ayya Ammiey dama fa nazo sanar mata ne papieyn ta yau dai munci gari ya barni zuwa gida"
"Ahhhhh inyeeeeee Masha Allah,kice yau dai kinci tiyya keñan, kuma gashi ƴar gaban goshin naki bata nan ba" bakinta ta ɗan tura tare da furta
"nikam da nasan za a barni fitar nan Allah da bata jeba"
Saidai ta ɗan murmusa tare da furta "In banda abinki Fatima aiba yau farau ba, kuma ba yau ƙarau ba wata ran in ba'a jeba wata ran sai aje"
Ita dai ba yadda ta soba haka nan ta haƙura badan taso ba, sai kuma ta kamawa ammeyn wani aikin suka ci gaba dayi tare.
A hankali ya sanyo kansa cikin parlourn yau kam complete cikakkiyar shigar hausa Fulani yayi. Cikin wani ɗanyen bowel na maza baƙi mai roɗi riɗi. Sai hular daya sanya wacce ta shiga da kayan, Tsintsiyar hannunsa ɗaure da wani rantsatstsen watch wanda ya haska farar fatar hannunsa. sumar nan ta sauƙa ta ƙasar ƙeyarsa sai wani irin maiƙon ƙyau take. Hannunsa zube cikin aljihun wandon, wanda dukkan alamu suka gama bayyana cewae wanka ma yayi. Ganin babu kowa parlourn ne ya sashi nufar kitchen ɗin kai tsaye. da sallama ya shiga cikin kitchen ɗin ammiey ce ta amsa shi, Idonsa na kanta ya furta, "Ammiey naje anguwa"
"To me sunan manya saika dawo" hannuwansa ya sanya ya ɗan shafi ƙasan ƙeyarsa. Yana yin woje cikin siririyar muryata ta furta "A dawo lafiya"
Wani irin daɗi ne yaji ya ratsa ko ina na jikinsa maimakon ya amsa sai kawai ya fice a parlourn ma baki ɗaya. Shi daya ya fita kai tsaye makeken boutique clothing store nashi ya nufa. Sosae yaji di kaya kamar hauka wanda har nima hakan kaina ya bani mamaki. daga nan kuma gidan Hajjo ya nufa yaje suka gaisa, ai kuwa yayi dana sanin xuwansa domin maganganu ta ringa ɓaro masa.
Tako ta ina inda ta shiga ce masa.

Ita fa bataji labarin samun ƙaruwa ba, in kuma shegen zafin kansa ya sanya shi gaza kusantar matarsa wllh zata haɗa shi da ubansa ya masa faɗa ya kusanci matarsa, Idan kuma baya da lafiya ne ya fito ya ya faɗa mata ta shiga jeji ta haɗo masa sassaken LoL 🤗
(Hhhhhhhh LoL 🤩 hajjon mu, wato zaki faɗa ma Abba yama Alieyo faɗa yayi sex da matarsa, LoL 🤗 🥰 nikam ina son ki Hajjo Naaaaaa)

Koda ya koma gida loƙacin tuni harta shirya cikin lafiyayyan leshinta ruwan zuma. Ta daura mayafinta me ɗan girma, Saida ta biya tama ammiey sallama kana ya ɗauke ta suka ɗauki hanya..
Cikin tarin nutsuwar sa yake mirza starring motar, hannunsa cikin nata hannun yana mirzawa, cikin wani irin silent voice yace da ita. " Da dukkan alamu Hajjo ta gaji da ganin ki babu ciki, don haka saiki shirya amsana a matsayin miji, ki bata jikokin da take da buƙata"
Hannunsa dake cikin nata ta matse da ƙarfi, tanajin yadda wani irin matsananci kunyarsa ya gama baibaiyeta. da kuwa ta kife kanta a cinyarta bata kuma yarda ta dago kanta ba, har suka ƙarasa gida.
Har gidan ya shiga da matarsa tunda dama gidan ba baƙonsa bane, a farfajiyar gidan yayi parking tun kamin ya gama daidaita parking nashi ta fita tana zurawa a guje cikin gidan, ummie tana zaune a saman kukera ta kunna kallo tana kallar Sunnah tv, domin gidan shiru yaya jay na India shima Nurien na gidansa , Abba Kuma na wurin aikinsa babu zata babu tsammani kawai saiji tayi an fado jikinta, hakan yasa a ɗan firgice ta furta "Subhanallah!"
Wata mahaukaciyar dariya queen ta kwashe da ita, tare da furta "I Miss you my ummiena, nayi kewarku ke da Abbana dasu yaya Nurien da yaya jay I Miss you All my family Naaaaaa" ta karasa maganar tana rungumo ummiena, ajiyar zuciya ummie ta saki tare da sakar mata murmushi, sai kuma ta juwo da ita tana zaunar ta kusan ta, "ohhhh Allah wai har yanxu kekam bakiyi hankali ba Fatima!"
Ummien ta faɗa tare da tsare ƴar nata da Ido. Bakinta ta ɗan tura gaba cikin shogoɓa da sakalci, tace "Ashe duk missing naku da nayi ke bakiyi nawa ba ummie!, tunda daga zuwana har kin fara min faɗa"
Ɗal taji an bugi bakinta hakan yasa ta ciro kanta, ALIEYO ta gani tsaye daf da inda take zaune. "Shiiiiiiiiiiiiiii " ya ɗaura hannuwansa saman bakinsa alamun ta masa shiru, Ita kuwa ummie murmushin jin daɗi ta saki. Zama yayi shima a ƙasan duk yadda ummie taso daya zauna saman kujerar ya ƙiya, don dole ta ƙyale shi a ƙasar, nan ya shiga gaida ta cike da girmamawa, A mutum ce ta amsa shi cikin sakin fuska bayan sun gaisa ya mike yana faɗin bara yaje ya ɗan dawo.
Ita kuwa nan suka buɗe babun fira ita ummienta, babu jimawa saiga Abba ya shigo gidan,shima Sosae yaji daɗin zuwan da tayi don tunda akayi bikinta yau kimanin watanni shida da ƴan kai ake magana. Cikin ƴar tsokanar daya saba mata yace "AHA Autar Abban ta keda abban yake shirin zuwa gaida ki a tunaninsa kinyi nauyi ne" kanta da sunne ƙasa ta shiga wasa da yatsun ƙafafunta. Ita dai ummie nata murmushi ne, Bayan anyi sallar la'asar ta shiga wurin Mama, sosae itama maman taji daɗin ganin Fatiman duk da kuwa cewar suna yin woya akai akai. Bayan sun gaisa itama Maman Aliyu shureim ɗin ta karema queen kallo tare da futar, "Yo ke ai ina nan inata haɗa lissafin haihuwar ku keda ƴar uwarki, kuma saina ganki haka zingari minki, Anya!, Anya kuwa Fatima"
Loƙaci guda Idanunta suka tara kwalla sai kuma ga ruwan hawaye sharrr ya biyo fuskarta, ƙuri Mama ta mata da Ido aranta tana jinjina irin taurin zuciyar da fatiman take da. Saida taba Ajiyar zuciya mai ɗan qarfi kafin a sanyaye ta shiga mata nasihohi masu ratsa zuciya da kashe jiki, dangane da danne haƙƙin miji akan matarsa, domin bata raba ɗayan biyu ta hana mijinta haƙƙin sane kan wani banzan dalili nata. "Ban san wacce iriyar zuciya ke gareki ba Fatima nasihar nan faɗan nan anyi Miki a tsaye anyi Miki a zaune, amma dammmm kin gaza ɗaukar ƙaddarar ki, haba Fatima sai kace ba musulma ba! Shi wanda kike yi domin nasa yana Cenñnn ƙarƙashin ƙasa ta daɗe da rufe idanunsa, in banda hauka ma shikenan akan wani banzan dalili naki ki hana salihin Allah haƙkinsa, yo mace ma data zauna da miji harda ƴaƴa yana mutuwa kuma ta auri wani mijin harda ƴaƴa, amma ɗan banzan kafiyar tsiya ya miki yawa Fatima, to Wallh ki sani ruhin Aliyu bazai taɓa samun salama idan har haka zakici gaba da danne haƙƙin mijinki, don wannan ba gata kika masa ba, ke kin kuwa ma san tsinuwar Mala'iku akan mace mai danne haƙƙin mijinta, ko macen da miji zai ƙirata shimfidarsa taƙi zuwa ranar tana kwana tsinuwar Mala'ikun Allah ne, bare ke da shafe sama da watanni, to maza idan har hasashe na gaskiya ne kiyi gaggawar Sanja hali domin wannan ɗabi'ar bata Muminina kwarai bace, idan kuma Allah ne bai kawo ba Ubangijii ya baku na gari masu albarka!"
Tunda Maman ta soma mata wannan nasihar ta kife kanta saman ƙafafun Maman take sharɓar ruwan hawaye, so take tayi magana amma bakinta ya mata nauyi, hakan yasa kawai take ta zirarar da ruwan hawaye. Sallama wasu yara ne yaja hankalin Mama hakan ya sa ta fito tsakar gida, ko aikosu akayi, turus kuma ta tsaya ƙerere tana kallon Ikon Allah.
"Sannu Aliyu!, Aliyu ya tafi Aliyu ya dawo, Ikon Allah kai waɗan nan yara babu abinda zamu ce daku acikin duniyar nan sai fatan Alkhairi, Ikon Allah, shekaran jiya jiyar nan saƙon Jawad ma ya riske mu, ikon Allah keñan me yadda yaso"
Tayi maganar wasu zafafan hawaye na zubo mata, jiki a mace queen ta fito jin shirun yayi yawa ne ya sanya ta fito wa tsakar gidan. Sai kuma ta tsaya cakkk ganin Mama tana hawaye, ga yara sai shigo da kayayyakin abinci suke.
"Subhanallahi Mama wai me ke faruwa haka ne?" Tayi maganar da sigar tambaya, Saida ta share hawayen fuskarta kana cikin wani irin rauni ta dubi fatiman....

*BY AMMEY LAYLERH ✍️*

*💘🌺ƘAUNA BIYU 🌺💘*

~Heart touching love, with love a side 🤍🤍~

Page 47&48

*NA Maryam Naseer Ibraheem*
*AMMEY LAYLERH*

✯ *~🌠 OFFICIAL MIRRAH 💫~*

♥️🤍♥️
_____________________________________________

***Sai kuma ta mata nuni da kayan abinci da har yanxun ake ci gaba da shigowa dasu, dangin su shinkafa Æ´ar buhu, taliya, makaroni, katon katon na kiras É—in kwai, kifin gongoni madara peak ta gari data ruwa, sugar, plantain, Kai da dai duk wasu nau'o'in kayan abinci, idonta naci gaba da zubar hawayen ta shiga faÉ—in.
"Fatima bansan dame ne zan sakama waÉ—an nan yara ba wajen biyansu, saidai addu'a tsakanin mu dasu, Ubangijii Allah yaci gaba da wanzar da farin ciki acikin rayuwarsu dama zuriyarsu baki É—aya, Allah ya raba su da dukkan wani sharri na mutum na aljan Ubangijii ya musu kyakkyawarn Sakamako a gidan aljannatul Firdausi"
Chapter 45 · 0% Book details