← Book details Ƙauna Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 56

Sashe 33

Ƙauna Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A tsare escort ɗin da suka zo tare dasu suka soma ɗibar Wasu manya manyan haɗaɗɗu kuma ƙayatattu akwatuna suna shiga dasu cikin gidansu queen suna jerewa.
Da kallon mamaki su ummie suka shiga bin uban akwatunan da ake ta famar shigowa dasu tamkar za'a buɗe ɗan ƙaramin boutique clothing store ne,tun ƴan uwan ummie da jama'ar ta na lissafa akwatunan har kowa yaja bakinsa yayi tsimmmm. Sallamar su oum abiddeen itane ta dawo dasu daga duniyar da suka lula don su duk a tunaninsu ɓatan kaine aka yi.
A mutumce a kuma girmame aka ma su oum Anum kyakkyawar karɓa ta musamman duk kuwa da basu san suɗin su waye ba.
Tuni har cika musu gabansu da kayan motsa baki da tarin juice masu ɗan karen sanyi, cike da girmama kara irin nasu ummien su oum abiddeen suka ɗan taɓa abubuwan da aka kawo musu, bayan sun sake gaisawa ne oum Anum ta gabatar da kansu gasu ummie, cike da fara'a ummie baiwar Allah ta ce "haba koda naji wallahi ban magantu bane kawai amma kamarku da Fatima har tayi yawa barin ma ke” ta ƙarashe magamar tare da nuna Oum Anum, ɗan murmushi ta saki tana faɗin "aikuwa dai kowa yace tamkar twins haka muke"
Nan dai suka ɗan taɓa fira kafin suce dama akwatune suka kawo na matar Aliey.
Nan dangin ummie suka shiga yalyala guɗar farin ciki a take suka shiga ƙoƙarin ganin kayan. Ƙayatattun Akwatina ne set goma sha biyu ko wanne da colour nashi daban-daban
Wannan tana wane wancen, wancen tana wane wannan, yehoho zoka ga didima tuni gidan ya Kuma daukar rakaɗin murna, queen dake cikin barcin ta sama sama ta soma jin hayaniya, har tazo ta soma damunta hakan ya sanya ta jan tsoƙi me ɗan ƙarfi, tare da dirowa daga kan gadon tana gyara mayanin blue black ɗin kimono robe ɗin dake jikinta fuskar nan ta kuma yin fayau tayi ɗoɗar abinta sai zabga uban ƙamshi take. A nutse ta nufo parlourn domin ganin mene kuma ake kuma yi haka.
Turus taja ta tsaya loƙacin da taci karo da abinda ba tayi zata ba, hakan yasa ta juya da nufin ta koma.
Cikin sauri oum abiddeen ta tace "wannan ba amaryar mu bace take shirin juyawa?" Baki É—aya mutanen parlourn sai hankalinsu ya koma kan queen, harda Anum da tun suka shigo gidan kala bata furta ba, sai yanxu ne ta dago jin an ambaci amarya hakan yasa ta É—ago da shirin ganin amaryar itama, sai kuma Idanunta suka mata tozali da kyakkyawar halittar queen.
Wacce take tsaye kanta ƙasss ta gaza yin gaba ta gaza yin baya, da ido ummie ta mata alamun tazo su gaisa a kunyace ta ƙaraso har gabansu tana gaida su, cikin tsananin ƙaunarta me zurfi suka shiga amsata cikin sakin fuska harda ɗan tsokanar tama suka yi. Ita dai murmushi ne naga tsamm ta miƙe tana farin parlourn kai tsaye tayi waje tana nufar hanyar balcony domin ta ɗan shawo iska.
Sun jima a gidan kafin su tafi dab da magrib, cike da tarin abin arzikin da su ummie suka haɗa musu da kuma tukuwcin lefen da suka sanya musu masu nauyi. da tarin wasuwasai haka Anum ta fice dasu,itafa bata taɓa zatan ana samun kyawawa irin haka a 9j ba, domin koshi kansa alieyon tasha jinin ammeyne ke yawo a jikin sa har ya ratsa shi LoL 🤩 kunji fa.
(To Wllh kizooooooo 9j idan kika haɗu da irinsu ya Al-ameern Naaaaaa ai kin gama dace ƴen mata🤗🥰)

Bayan anyi sallar isha'i su Aunty zeey suka shiga kimtsa amarya Fatima, cikin ƙayatacciyar shiga ta alfarma, banda kuka babu abinda take famar yi duk ta faɗa kolliyar nata da ruwan hawaye, tana faɗin ita dai baza a kaita ba LoL 🤗 Ni kuwa nace ku bar mana queen ɗinmu ta huta haka nan mana.
Hajjo da MAH sai kuma su oum Anum oum abiddeen da sauran wasu ƴan uwan na jikine suka zo ɗaukar amarya, loƙacin da sukaji irin nasihohin dasu ummie suka shiga yima queen ɗin masu ratsa jiki ba ƙaramin burgesu suka ji sun ƙara yiba.
Motocin kusan goma sha biyu ne suka zo ɗaukar Allah Sarki dake ita bama mai yawan ƙawayen barkatai bane ya sanya babu ƙawar data mata rakiya duka ƴan uwaan ummie dana abbansu ne suka mata rakiyar, wacce ma zata yin itama yau ɗin dai zata tashi wato fareedah haka suna ji suna gani babu wacce tama wata rakiya a cikin su.
Ita tuni ma har an kaita gidanta dake malali Quarters, tana daga ɓangaren mah da hajjo sun sanya ta tsaƙiyarsu. Haka tana ji tana gani motocin suka ɗauki hanyar barin anguwarsu, iya ƙarfin ta ta saki wani azababben kuka faɗi take
"Don Allah kada ku rabani da iyayena!, don Allah ku barni bana son auren wallh bana son wannan auren"
Mah ce ta shiga lallashinta ita kuwa me girma hajjo kanta ta É—an dungure mata tana faÉ—in.
"Banza raguwa wacce ta rako mata duniya auren?, gidan mijin kike ma kuka, nifa ƴaƴan yanxu mamaki ma kuke bani ku gama shan soyayyarku da mutan amma idan za'a kaiku ku wani ɓare kuna mana kuka munafukan nan kawai! Kin wani daga kina kuka da an dangantaki da mijin kuma shikenan se a buɗe babin soyayya asha Love, yanxu da za'a ce an fasa baki ɗaya sai kin tashi hankalinmu anan!"

Cikin kuka tace "wllh a fasa, wa yace miki son sa nake to wllh AUREN DOLE aka min, wannan auren da kike gani auren biyayyar iyayece kawai, amma wllh da baxan yi auren ba kara nasan Nima mutuwar nayi nabi yaya Aliyu Naaaaaa ” sai kuma kukan yaci ƙarfin ta haka dai suka Ringa fafatawa har suka shigo fitacciyar anguwar *SHARAƊA PHASE 01* Ajere motocin suka dinga kutsa kansu zuwa parking space na gidan.
A nutse suka fara fitowa ɗaya bayan ɗaya har zuwa loƙacin da aka zo kan queen, wacce taki yarda ya fita a motar yin duniya amma taƙi fita, don dole suka ƙira ammiey, aikuwa sai gata baiwar Allah nan ta rarraso abarta, aikuwa sai gashi ta yarda cikin tsananin so ammey tace
"Ki fito da ƙafar dama kana ki fito da Bismillah" kamar yadda ammey ta umarta hakan tayi.

Cikin girmamawa ammiey ta tarɓi ƴan kawo amarya, kai tsaye ɓangarenta suka wuce da queen ɗin.
Rantsatstsiyar walima su oum Anum suka shirya iyaka su yasu, me ƘWALLIYAR da suka tanaja ta musamman ce tazo ta fara aikinta wato zeey Abba, taƙyar da lallashi ammey ta lallashi abarta kana ta yarda wacce za'a yi a coumpaund na gidan.
Haka shima bangaren ango suka tisa shi gaba don dole ya shirya kansa cikin wasu rantsatstsun shiga na musamman, kuma tunawa da Anum ne yasa yaji yana da kwarin gwiwar hakan, kodan ta fita a harkar sa zai nunama wannan yarinyar kulawa in yaso taga yana son matarsa ai zata fita a harkar sa, ita kuma daga baya yayi maganinta ta hanya mafi sauƙi kafin itama ya sallame ta LoL 🤩 amma fa inji ALIEYON ku ba AMMEY LAYLERH ba aha.

To naɗan yi ƙoƙari gaskiya don da banma yi tunanin zan yi TYPING ɗin ba ku ɗan huta da wannan.

* SHIN YAZA'AYI⁉️*

Kudai kubi taku

*AMMEY LAYLERH ✍️*
Don jin yacce zata kaya 🤗 uhummmmm a gimtse 🫰 🙃 ba

LOVE YOU All MASOYA NA💘♥️

*💘🌺ƘAUNA BIYU 🌺💘*

~Heart touching love, with love aside 🤍🤍~

Page 35&36

*Na Maryam Naseer Ibraheem*
*AMMEY LAYLERH ✍🏻♥️*

✯ *~🌠 OFFICIAL MIRRAH 💫~*

_____________________ ♥️🤍♥️

Su Oum abiddeen ne suka sanyo alieyo a gaba tamkar shine amaryar,yana takun nan na ƙasaita da kuma izza, a gaban wata narkyakkiyar farar Ferrari suka tsaya suna buɗe masa, fuskar nashi yau ita ba a ɗaure ba ita ba asake ba haka nan dai take kadaran kada han, kyawawan fararen ƙafafunsa ya fara da yawa ciki kafin ya shige baki ɗayansa, wani irin zuƙar Numfashi yayi jin wani irin daddaɗan ƙamshim daya bune hancinsa, yana tsimewa acikin kujerar motar tare da jan lumsassun Idanunsa ya lumshe su lufff.
Ahaka har suka isa coumpaund ɗin inda family's nasu suke Zazzaune, a bangaren queen teemah kuma akwai Aunty zeey sai kuma lalla Khadijah tare da iya mooh kaka a wajenta keñan. Tsarin yadda suke gudanar da walimar bikin su na Madina, haka suka tsara wannan ma.
Amarya tana zaune cikin wata rantsatstsiyar kujera irin mai kama da gadon nan, sai wasu manyan fulawowin da suka ma wajan ƙawanya, gefe da gefen inda take zaune kuwa wasu tsumammun humrace me azabar ƙamshin mai juya tunanin mutum da hargitsawa. dama kuma already oum abiddeen ta mata wanka da wasu fitunannun sinadaran kamshi masu tsuma jinin jiki da narka zuciya, A nutse a kuma tsare MAH taje har gaban motar da akayi parking nata, da kanta ta buɗe masa murfin tare da kamo hannuwansa cikin nata, da idonta ta tsare shi tare da masa wasu magungunan da idon.
A hankali a kuma nutse suka fara takowa cikin keɓantancen wurin hannunsa cikin na MAH, suna zuwa tsaƙiyar taron aka saki wasu irin furanni, tare da sakin haske irin mai kalolin nan.
Chapter 33 · 0% Book details