← Book details Ƙauna Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 56

Sashe 21

Ƙauna Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Da tarin tunanin nika fall zuciyar ammiey a haka har tayi parking motarta a coumpaund na gidan, zuciyarta naci gaba da saƙa abubuwawa maban banta masu ɗan dama,ga kuma kukan da queen ke faman yi har zuwa yanzun kuwa, idanu ta zuba mata yayinda kukan queen ke ratsa jiki da zuciyar ammien.
Domin kai tsaye ta fashimci ko kukan mene queen ɗin keyi tsananin tausayinshi ne ya ƙara kama zuciyarta sosae fiye da tunanin duk yacce kuke tunani.
Hannuwanta Ammiey ta kamo tana fitowa da ita waje tare da É—an jingina ta da jikin ta, tuni dama yaya jay da aunty zeey sukayi nasu gidan directly.
Cikin gidan suka nufa suna tafe tunani ya cunkushe ma
Queen tarasa wane kalar ma tunani zatayi dan gane da wannan mugun abokin yayan nata, ahankali take taka ƙafadunta har suka kai main Parlourn Gidansu dab da gaban ummien ta ta tazauna. Ganin queen tare da ammiey kuma yasa ummie tambayar ammiey ko lafiya?, ɗan murmushi irin mai ciwon nan Ammiey ta saki tare da zama kan ɗaya daga cikin kujerun parlourn, tana sauƙe ajiyar zuciya. Kafin cikin yanayin damuwa tace. "Ita da wannan ɗan uban zafin ran ne mana ALIEYO!, daga haɗuwarsu a cikin plaza ya kama makarta haka nan kawai”.
”baki bibiyi yadda abin ya faru bane Mom ALIEY! Amma tabbas ni nasan haka takanas ba tare da laifin komai ba alieyo bazai kama Fatima ya dake taba, tunda dama ba xuwan kanki bane, ƙarar ɗana kika kawo kinga tafiyana” ummie tayi maganar tare da miƙewa, da kallo irin na burgewar nan Ammiey tabi ummie dashi.
Tabbas bata ma aliey zaɓen tumun dare ba ita kanta tasan da hakan, hankalinta ta dawo dashi kan queen da
tunda suka shigo take sakin ajiyar zuciya, duban Fatiman tayi tare da kama hannuwanta cikin sigar lallashi tace ”kiyi haƙuri kinji Fateemerh Ni! da kaina zan sanya ALIEYO Naaaaaa ya baki haƙuri har ƙasa kuma zai turkusa Miki, na Miki alƙawarin hakan koda ba yanxu bane kuwa Fateemerh kinji daughter Naaaaaa” wani irin matsanancin farin ciki ne ya kama Fatima jin abinda Ammiey tace da ita, hakan ya sanya t jin wani irin azababben daɗi mamaye ta har batasan loƙacin data ƙanƙame Ammieyn bama, cike da matsananciyar murna ta furta.

”Da gaske kike Loli Ammiey Naaaaaah”
lumshe idanu Ammiey tayi duk Duniya babu me gaya mata wannan sunan face mutum É—aya.
”ALIEYO!” Ammiey ta faɗa tare da sauƙe Idanunta kan fatima (tabbas kin chanchanta Fateemerh ke kika dace!) aceñnn ƙasar zuciyarta Ammiey tayi zancen.
”Ko zamu tafi tare xuwa dare saina dawo dake” muryarn Ammiey ya daki kunnuwanta a matuƙa firgice ta ɗago tare da duban Ammieyn, tuni Idanunta harya tara ƙwalla kanta ta shiga jujjuyawa kafin cikin danne kukanta dake son kubcewa tace. ”zai kuma duka nane fa Ammiey”
”inji waye yace zai kuma dukanki?, ai yayi na farko yayi na ƙarshe kisa hakan a ranki kinji daughter Naaaaaa”
(Na biyu dai ammey) Ta faɗi a zuciyarta. Jin kamar tayi magana ya sanya ammiey faɗin. ”mene kika ce Fateemerh?” .
”bance komi ba ammey” ta faɗa tana ɗan murza hannuwanta, "Okk " ammiey ta miƙe tana faɗin "Ni zan wuce gida na bar Amnah ita kaɗai sai babanta shi kuma a wannan murɗaɗɗen halin nasa nasan ita kaɗai zai barta, tayi ta watan gaririya a cikin gida" jin an ambaci Amnah yasa Fatima miƙewa da sauri tana cewa "ammiey na fasa ƙin xuwan, yanxu zan bikin mu tafiiiiiiiiiii" murmushi ammiey tayi daidai loƙacin kuma ummie ke sanyo kanta cikin parlourn.
”yawwa kin fito a daidai zan tafi da Fatima tunda kema bayan ɗanki kikabi, Nima nabi bayan ƴata” indai Fatima ce ma zamuji ku a rana ne domin mai iya zama da Fatima saiya daure, ita ɗin zuma ce Saida wuta!, a sauƙa lafiya ga saƙon yarona ya kwana biyu baizo shan mutuminsa ba” da farin ciki shimfiɗe saman kyakkyawar fuskar ammiey ta amshi plask ɗin, wanda ta tabbatar kunun gyaɗa ne a ciki. "Uyummmmm kema ai haƙuri kawai kike da wannan uban ƴan miskilancin, ga bauɗaɗɗen hali ga kuma shegen miskilancin tsiya da ɗacin rai"
"Zan rama" shine kaÉ—ai abinda ummie tace domin harsun fice a parlourn baki É—aya ma.

Ahankali ammiey ke driving tamkar ɗazu a haka har suka ƙaraso shashararriyar anguwar sharaɗa phase 01, Ammiey ce ta fara fita kafin Queen ɗan murmushi ammiey ta saki ganin duka motocin da gidan wanɗanda Abba da Irfan suka hau a fake daga cikin parking lot. dake ita a coumpaund ne tayi parking motar ta a nufin ta idan za'a maida Fateemerh gida basai ana shan wahalar fiddo da wata motar ba.

Abba Irfan sai Amnah duka suna zaune a main Parlourn gidan,da sallama ammiey ta shigo Fatima biye a bayanta, da wani irin bala'in gudu Amnah ta nufi wurin queen.
Ai ita kanta batasan loƙacin da wani irin murmushi ya kwace mata ba, hannuwanta ta ware mata tare da tsugunnawa, exctly irin yacce papieyn ta ke mata. Tana xuwa ta shige cikin jikinta ita kuma ta miƙe da ita tare da fara juyi da suna ƙyalkyala dariya tamkar wasu taɓaɓɓu. Cikin tsananin farin ciki Amnah tace "new Mamie Naaaaaa kin dawo gidanmu wurin papiey Naaaaaa!" Abba, Irfan, Ammiey baki ɗaya da wani irin kallon $0 Ƙaúna suka shiga bin Fatima dashi, mai cike da birgewa da shiga rai ina nan farat ɗaya.

Hannuwansa sarƙe akan shoulder nashi daga upstairs nashi yake kallon komai dake wakana a cikin parlourn. Wani irin rumtse idanunsa yayi da ƙarfin masifa loƙacin da maganar Amnah ta doki kunnuwansa. Hakan yasa cikin wani irin mugun zafin rai yabar wurin a hanzarce.
Saida yaya Irfan yama Amnah magana kana ta nutsu amma taƙi barin jikin queen ɗin.
Ahankali ta risinar da kanta ƙasa loƙacin data fuskanci ba iyaka su kaɗai bane a parlourn, a nutse ta shiga gaida Abba wanda ya amsata cikin a mutunce da sakin fuska sosae, shima yaya Irfan ta gaida shi cikin wani irin yanayin dashi kansa Irfan ɗin ya gaza tantance wane irin yanayi ne ya amsata, yanayin daya fi kama da irin shauƙin SO haka.
(LoL 🤩🥰🤩🤫 🤗)

Akan lausassan carpet É—in dake malale a tsakiyar parlourn ta zauna duk kuwa da yadda ammiey ta hana ta amma ganin manya yasa mutuniyarku nutsewa tamkar ba queen É—in yaya Nurien ba.
Da ido Abba yama ammiey alamun itace keñan, da idon ita ma ta masa alamun ka bari ba yanxu ba tukunna, babu yacce Abba ya iya don haka ya ƙyale ammiey. dake weekend ne kowa yau Ranar hutun sane yasa haka suka wuni a parlourn, inda baki ɗaya queen take a taƙure, daɗinta ma ɗaya queen na tare da ita.
ƙiran sallah zuhr da akayi ne ya sanya Abba tare da Irfan fita zuwa Masallaci,a gaban sink ɗin dake jere daga wurin plawer suka tsaya sukayi alwularsu, suna fita xuwa masallacin dake manne da ƙofar gidan su. Cikin takun nan na ƙasaita yake tunkaro parlourn tare kuma da tsaraban sassanyan ƙamshin mayen tularensa. loƙacin da ALIEY ya ratso tsakiyar parlourn, shiɗin kyakkyawane na gaban kwatance cikakken bazaraten mutum ne sosae Lallai babu ƙarya, ƙyawun sa na musamman ne a nutse yake tafiyar tare da soma nannaɗe hannuwan rigarsa. Lokaci ammiey itama bada parlourn ko inda muke bai kalla ba, duk kuwa da yadda Amnah keta famar ƙiran mahaifin nata. Amma haka ya share mu tamkar ma bai san anyi ruwan mu a cikin parlourn ba.
Amnah naja ta kaini ɗakinta anan na shashantar da wunin nawa, wurin yima Amnah kitso domin na fashimci Amnah irin yaran nan ne da samm basu son kitso. Haka na tashi na yarfa mata kitsonta mai ƙyau, ga Amnah nada robar gashi ba laifi gashinta war wajen gadon bayanta.
dinner ma Nan ammiey ta kawo mana abinmu, sai wajajen yamma liss kana muka dawo parlourn a shirye tsaff muka fito domin nayi wankana a ɗakin Amnah ita ma na mata. na sanya mata wasu haɗaɗɗun riga da wando masu masifar ƙyau irin trouser in Nan na yara masu taushin gaske, wandon pitch color ne yayinda rigar ta kasance milk color ita kuma sa pitch ban dana saka mata. Ya Ilahi zan iya rantsewa tunda nake ban taɓa ganin yarinya kyakkyawa kamar amnah ba.

(Ni kuwa AMMEY LAYLERH nace LoL 🤩 yachin kowa kanca ya sacani 🤗 na tabba ko My LAYLERH Naaaaaa tafi Amnah kyau😳🚵🤫 ahaaaaaaa)
Chapter 21 · 0% Book details