← Book details Ƙauna Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 56

Sashe 35

Ƙauna Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ita kuwa aunty zeey yau take kallon ikon Allah, ashe haka alieyo ke tsananin ƙaunar queen dama?, shine tambayar data shiga ma kanta da kanta.
Mutsu mutsun ƙwatar kanta ta shiga loƙacin data dawo hayyacin ta, domin da Samm bata a hayyacin nata ne sakamakon sautin sa daya Ringa ratsata yana shigar ta, bata san sanda tayi lufff saman faffaɗan qirjinsa ba, exctly hakan sai ya tuno mata da nurul qalb ɗinta yaya Aliyu shureim. amma da tunani da nutsuwarta suka dawo gangar jikinta Saita shiga ƙoƙarin kwatar kan nata.
Hakan ya sanya ALIEYO kai bakinsa daidai setin kunneta murya can ƙasa ya ce. "Saida kika gama mo re jikin kana kuma shiga wasu fusge fusgen ƙarya, yau dai burinki ya cika kin samu abinda ki daɗe nema, tun da duk loƙacin da zaki ganni sai kinyi duk yacce kikayi kika danganta kanki da jikina, gashi kuma yau kin samu a rabassss"
Yaja sautin yana É—an ja baya kaÉ—an
Fuskashi tsuke .
taɓune fuska tayi irin taga abin ƙenkemin nan cikin muryarn dake ɗan rawa ta furta
“Ni ka sakeni”
Yanayin yanda suke magana ƙus-ƙus ne da yadda suke kallon juna ya sanya ammiey sakin amintaccen murmushinta me taushi cike da jin daɗin ganin yadda abubuwa suka fara dedetuwa tun kamin aje ko ina.
Kallonta yayi da shanyayyun Idanunsa Cikin nuna mata zallar rashin wasa a maganarsa yace " dan Allah ki ƙara taku ɗaya daga inda kike tsayen nm ki gani sai na baki cikakken mamaki domin Tsotse wannan jan bakin naki tare ma dayin abinda baki zata ma idan har baki nutsu min ba"
Tuni Idanunta suka cika da ruwan hawaye, MAH ce ta taso cikin nutsuwa ta janye queen daga jikin alieyo tare da komar da ita wurin zamanta, shima ta komar da shi, Princess Amnah ce ta zame hannuwanta ana ammey ta ruguwa zuwa wurin su, dama tun farko take ta ƙoƙarin kwace wa ammeyn ta hana ta, ai kuwa tana zuwa ta faɗa jikin queen cikin tsananin murna ta maƙalƙaleta, cikin muryarn ta na yarinta ta ce "Na happy New mummy Naaaaaa, ai de shikenan yanxu Finally kin zama mummy na?" Kowa dake wurin idanunsa akan su cikin wani irin yanayi me ratsa jinin jiki queen ta saka hannayenta tana rungumo Amnah zuwa cikin jikinta, kafin ta ɗan shiga taping na gadon bayanta cikin tsananin zallar ƙaunar Amnah ta sake rungumota zuwa cikin jikinta, nan ta shiga faɗa mata wasu abubuwa, ita kuma tana sakin dariya, kowa dake wurin sosae queen ta sake shiga ransa, shi kansa boss ɗin wani irin azababben burgesa hakan yayi, wanda har fararen jerarrun hakwaransa suka ɗan bayyana, domin shi a duniya duk wanda zai so Amnah gudan jinin sa to kuwa tabbas duk tarin ƙiyayyar da yake ma sai dena tane baki ɗaya.
a haka shagalin yaci gaba da wakana inda duk wannan uban abubuwan da alieyn keyi yake a matsayin yana yin hakan ne don Anum ta fita a rayuwarsa.
Su Oum abiddeen ne suka shiga musu kari na dollers, Anan sarki julaideen ya bama queen wasu kyautuka na musamman wanda alqalamin AMMEY LAYLERH ✍️ sammmm bazai iya ɗaukar rubuta suba kawai dai kuyi emage acikin zuciyoyinku, nasan zaku misalta.
11:43pm kwarya kwaryar walimar nasu ya tashi, wanda tuni tun farkon rungumar da alieyo yama queen ta bar wurin a fusace, kai tsaye sashin ammey MAH ta sake bada umarnin a wuce da queen ɗin, su Aunty zeey ma anan ammey tace su kwana kafin zuwa gobe su ƙarasa gyara mata shashinta.
Hakan kuwa akayi suka wuce da queen tare dasu Aunty zeey, shi kuwa Irfan yana gama ɗaukar videon tun a wurin ya yayi send wa YAYA JAY, AK EAGLE, da JALAAL AREEF, da MALEEK TOUFIQ. Manyan abokan yayan nasa keñan.
Tuni suka fara ƙiran alieyo tare da fara masa iya shege shi kuma saiya datse qiran, haka ya ringa bi yana datse musu qiran, sai suka WhatsApp suka ajje masa saƙonnin su. Sai bayan ya nutsu ne wajajen 2:13 na dare ya shiga messages na kowannen su, ya maida musu da amsa daidai wacce suka bashi fassarar.
Washe gari suka sake gyagygyara mata wasu abubuwan nata wanda Abba ya mata fitattun set na kayan daƙi set biyu Abba ya mata na gani na faɗa na nunama Sa'a. ita kuwa queen cikin kwanakin nan biyu da take sashin ammey sosae su MAH suke jiƙata da kayan gyara na musamman, ruwan humra kuwa sune suka zama ruwan wankanta, ga zazzafar madarar nonon sanuwar da kullum da ita take fara yin kalace, haka ma da dare itane ƙarshen kalacinta.
Saida tayi kwanaki biyar cifff a wurin su MAH kana suka miƙata ɓangarenta, suma washegarin ranar suka bar 9j cike da kewarmu LoL 🤩.
Tana zaune kwance saman lafiyayyan gadonta idanunta a É—an Lumshe sakamakon maranta take É—an mata ciwo sama sama, idan kuma ya murÉ—a mata saita tattare waje É—aya ta cure.
Tuni gumi ya shiga keto mata domin ba ƙaramin wahala take ba wajen yin period nata, tuni wani irin zazzafan zazzaɓi ya rufe ta linkif.

A hankali ya murɗa handle ɗin babban parlourn nata ya shiga, daddaɗan ƙamshi da kuma sanyin easyn daya bigeshi ne ya sanya shi lumshe idanunsa, tare da buɗewa cikin tafiyar sassarfa kuma ya ƙarasa gaban gadon ganin yadda take juyi a gadon, wuyanta ya taɓa yaji zafi sosae ga kuma hannunta dafe da setin mararta, Zaune yakai daga gefen gadon tare da ɗago kanta da har yanxun hayewe bai daina zuba ba, hannunta ta sanha ta sake share hawayen da suka ciko mata idanu "What's wrong with you?" ya tambaye hosky voice nashi.

Cikin É—an jujjuya kanta take masa nuni da mararta tare da kuma kamo hannuwansa ta É—ora samar wuyanta take ya fashimci abinda ke damunta cikin É—an hanzari ya bar É—akin, babu jimawa sai gashi ya dawo dakin hannuwansa rike First aid box.
  A gefen gadon ya zauna daf da ita tare da tsuƙe fuska dan ma karta kawo masa wani wargi, tare da buɗe first aid kit box ɗin ya fito da injection gefe guda kuma ga kalaben magunguna,
. Sosai ta zazzaro idanunta waje Ganin abinda ya fito da shi a hannu ne, ya sakata miƙewa zumbur jikinta na rawa Shiko ko kallon inda take bai yiba sai ma ƙoƙarin ɓare syringe ɗin daya shiga dashi yake. Hakan ya sanya ta saurin dafe hannunsa da syringe ɗin ke riƙe.
Sosai zuciyarta ke bugawa da sauri-sauri. a rayuwarta allura na É—aya daga cikin abinda take tsoro fiye da hasashen mai karatu, hakan ya sanya ta fara haÉ—a wata uwar zufa tare da É—an mui-mui da ido alamar zata yi kuka kenan.
A karan farko da abin nata yaso bashi dariya, dan haka ya ɗanyi luuu da idanunsa tamkar zai lumshesu amma ya hana hakan ta hanyar sake ɗaure fuskarsa da yayi, "Fitinanna!" Ya faɗa a cenñnn ƙasar zuciyarsa, tare da ɗan janwota zuwa cikin jikinsa ya miƙe da ita tsaye ƙafafunta saman nashi. Saida ya shammaceta kana ya daidaita inda zai sira mata allurar yana danna mata ita, Wani irin mugun ƙanƙamesa tayi tare da sakin wani raunataccen kuka tana kuma ƙanƙamesa Iskar bakinsa ya shiga hura mata a cikin kunenta, hakan yasa tayi lufff har ya zare allurar tare da ɗan murza mata wajen daya mata ɗin.
Zaunar da ita yayi tare da buɗe kwalaben maganin nan ma ya bata ganin ya yadda yayi kicin kicin da fuska ne ya sanya ta shanye magun gunan babu wani musu. tana gama sha wani irin wahalallen barci yazo yayi awon gaba da ita, zafin zazzaɓin na raguwa Adda'ar bacci ya shiga tofa mata bayan ya kammala mata Adda'ar ya ƙara mata ƙarfin gudun A/cn ganin yadda take gumi, tare da kashe mata hasken ɗakin yana bar mata dum light.
Tare da barin ɗakin yana yin nashi ɓangaren dama AMMEY ce ta ƙira shi a woya loƙacin yana tare da yaya jay take sanar masa fatiman babu lafiya, shine fa ya dawo bayan yaga yanayin jikin nata shine ya mata allurar ciwon mara tare da bata maganin zazzaɓi.

Saida sakarma kansa shower kana yayi Wonka tare da fitowa sanye da bathrobe, lallausar sumar sa sai ɗigar ruwa take kota kan yadda ruwan ke ɗiga bai yiba haka ya sanya wasu pyjams ruwan sararin samaniya, bayan ya feshe jikinsa da ɗaɗan tularukansa masu azabar ƙamshi.
Saida ya ƙara gudun easyn shima kafin yayi adda'oin barci ya kwanta wasu al'amurra masu wuyar misaltuwa na bijiro masa, har barcin wahala yazo yayi awon gaba dashi.
Ƙiran sallar farko tamkar a cikin kunnuwanta ne domin dama wannan ɗabi'ar tace, tashin asuba ɗin alhamdulillah garau ta jita hakan ya sanya ta faɗa bathroom,wanka tayo kana ta shirya kanta cikin riga da wando na pallazo, wanda ya kawo mata har saman ƙugunta rigar kuma ta shige cikin wandon Sosae kayan suka mata wani irin ƙyau bana wasa ba.
Ganin ba zata yi salla bane ya sanya ta zama tare da duba wasu littattafan ta wanda suka shafi addini, tana a zaunen taji motsin za'a shigo saurin kwanciya tayi domin tasan ma shine kadai zai shigo mata a irin wannan loƙacin, bakinsa ya ɗan taɓe domin sarai ya fuskanci idonta biyu saiya daga shoulder nashi tare da barin ɗakin yana ficewa zuwa masallaci, a coumpaund na gidan suka haɗu da Irfan da kuma Abba hakan ya sanya suka ranka ya zuwa masallacin.
Wajajen 9:40 ta kammala duk wasu abubuwa nata hakan yasa ta nufi sashen ammiey, bayan ta ɗora after dress saman riga da wandon tare da baby shimar, tana yin sallama Amnah ta tafi da gudu zuwa wurinta, itama cike da tsananin soyayyarta ta ware mata Hannuwanta, tana zuwa ta faɗa jikin ta ita kuma ta cira ta sama ta soma juyi da ita suna ƙyalƙyalcewa da dariya.
Alieyo dake nutse cikin tattausar caution É—in parlourn ne ya furta (di beta sai kace ba ita ce wacce ta dinga ma mutane kukan allura ba) ya faÉ—a acikin zuciyarsa.

Kai yaseen na gaji

A gimtse 🫰 kawai

To ai shike nan sai mun haÉ—u a next page
Daga taku AMMEY LAYLERH ✍️

Fejin na kune *OUM KHALIL*
Da
*INDO ADO (MOMY)*

Kuyi yadda kuka ga dama dashi aha nidai na baku ƙyautarsa 🤗🤗🤗🤗🤗🤗

*💘🌺ƘAUNA BIYU 🌺💘*
Chapter 35 · 0% Book details