← Book details Ƙauna Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 56

Sashe 32

Ƙauna Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

11:55am suka isa babban Masallacin da za'a wakilci dauren, Cenñnn na hango mugu ogan fatimanku yaya Nurien cikin wata rantsatstsiyar getzner fara ƙall sai murmushi yake ta famar saki, har wani sauri yake yaji an shafa fatiha. Motocin su na fakawa baki ɗaya kallo ya dawo kansu

*💘🌺ƘAUNA BIYU 🌺💘*

~Heart touching love, with love aside 🤍🤍~

Page 33&34

*Na Maryam Naseer Ibraheem*
*AMMEY LAYLERH ✍🏻♥️*

✯ *~🌠 OFFICIAL MIRRAH 💫~*

_____________________ ♥️🤍♥️

”Alhamdulillah alhamdulillah alhamdulillah, Allah shine abin godiya Ako mi da komai" suna kalaman da ammey ta shiga faɗa loƙacin da Abba yake sanar mata an ɗaura Alieyon ta, wani irin maɗaukakin farin ciki take jin kanta a ciki, wannan ranar jinta take ta musamman.
"Aiyuriri, aure ya É—auru alieyo saidai ka mutu" sune kalaman da hajjo ta shiga faÉ—a tare da juyi a tsakar parlourn,

Hannuwan MAH! Sama ta shiga faÉ—in,

"Ya rabbi ya mujibud da'awati ka tabbatar da tarin Alkhairukan akan wannan auren, ya Ubangijiin taliƙa ka kaɗe duk wata fitina dake cikin auren nan,

رَبَّنَا وَأَدْخِلْهُمْ جَنَّاتِ عَدْنٍ الَّتِي وَعَدتَّهُم وَمَن صَلَحَ مِنْ آبَائِهِمْ وَأَزْوَاجِهِمْ وَذُرِّيَّاتِهِمْ إِنَّكَ أَنتَ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ وَقِهِمُ السَّيِّئَاتِ وَمَن تَقِ السَّيِّئَاتِ يَوْمَئِذٍ فَقَدْ رَحِمْتَهُ وَذَلِكَ هُوَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُ

Our Lord! and make them enter the gardens of perpetuity which Thou hast promised to them and those who do good of their fathers and their wives and their offspring, surely Thou are the Mighty, the Wise. And keep them from evil deeds, and whom Thou keepest from evil deeds this day, indeed Thou hast mercy on him, and that is the mighty achievement.

Ubangijinmu! Kuma Ka shigar da su gidãjen Aljannar zama waɗanda Ka yi musu wa'adi da waɗanda suka kyautata daga ubanninsu da mãtan aurensu da zurriyarsu, lalle ne Kai, Kai ne Mabuwãyi, Mai hikima"

"Ameern MAH!"
Su Oum Anum da oum abiddeen suka haɗe baki wajen amsata, banda Anum ɗin data chakume fuskarnan yawa irin kunun da yayi barcin nan LoL 🤩🥴🤗.

Amnah ce ta faɗo parlourm da murnanta tana ƙiran "AMMEY! Ammey!! Ammey wai papiey ya samo min new Mommah?, inji uncle Irfan" Sammm ba ma ta kula da cewar ammey bata parlourn ba. Mah! Ce ta ta janyota jikinta cikin jin tsananin ƙaunar amnah a cenñnn tsakiyar zuciyarta ta furta "Insha Allah princess papieynki yayi aure!, ya auro Miki New Mamie da zataci gaba da kulawa dake da papieynki"
Tsalle tsalle ta shiga shi da murna tana cewa "yeeeeeeee My mother is not dead, I will also have a mother like Afnan, I will also tell them that I have a mother!"
Wata kwalla ammey dake tsaye tun farkon ƙiran da taji Amnah nayi mata ta fito, cikin matsanancin tausayin ta taji wahaye na sauƙar mata, Hajjo ce ta gani Idanunta sun cika da kwalla ta janyo Amnah jikinta, cikin karfafa gwiwa tace.
"Sosae babyn papiey mommanki na nan tare dake, kema kina da mama kawar kowa ba”
Mah ce da tun farkon tsaiwar ammien take lure da ita ne ta yafi to ta da hannunta ta mata alama data ƙaraso.
Ƙarasowa tayi tare zama tsakiyar yayyenta.
Ajiyar zuciya ta sauƙe loƙacin da taji MAH ta janyota samar jikinta, Allah Sarki uwa mahaifiyar da baka da kamarta har gaban abada, duk girman ka tabbas haƙiƙa kana buƙatar kulawar mahaifiya. A jejjere taci gaba da sauƙe ajiyar zuciyar, Cikin sanyin murya ta shiga faɗin, "Ma muci gaba dama mae sunan manya adda'a, ina tsoron zafin zuciyarsa, ina tsoron wannan auren kamar wancen karon! Kinsan sanadiyyar ƙunci da zafin zuciyarsa SOFEEYERH ta kamu da Heart at"
Saurin rufe mata baki MAH tayi ta shiga girgiza mata kai.
"Little dooo! Taya kike tunanin cewa ALIEYO shine silar komai daya faru, keñan kin manta da faɗin Allah da yace duk wani abu da zai faru da bawane rubutacce ne tun ran gini tun ran zane, ina tunanin ki?, Ina Ilimin, Ina hankalin da sanin da kike dashi?, Shiiiiiiiiiiiiiii kada na kuma jin wannan maganar a bakinki"

Haka dai MAH ta shiga kwantarma da little dooo nata hankali,tare da hajjo ma da ita harda su share kwalla, "Safiya mutuniyar kirki munyi rashin mace ta gari, amma ba komai inaji a jikina Insha Allah wannan yarinyar Alkhairi ne a cikin zuriyar mu" A fusace Anum ta miƙe tana shirin barin parlourn, da sauri ammey tace "A Ni kuwa Anum taimaka ki kaima Me sunan manya koda coffee na shine, don ina tunanin babu abinda ya zubama cikin sa wayewar yau!" Da harta ɓata fuska jin ammiey ta ambaci alieyo ne ya sanya ta ƙarasowa da rawarn jiki, domin ita sammm ammey tama manta da wani zancen aure ya taɓa shiga tsakanin aliey da kuma ita Anum ɗin, shekaru wajen uku kenan ko huɗu. Plask ɗin haɗaɗɗen coffee ɗin ammiey ta miƙama Anum sai kuma wani plate na tangaran wanda ta zuba masa danbum nama me azabar daɗin gaske.
Yana Sanye cikin wata kasaitaciyar collection na ƙananan kaya ta kamfanin dior hormes white shirt and a very soft black trosers. Tun da garin Allah ya waye dede ƙofar parlour bai sanyo ƙafarsa ba, kuma baya jin zai iya fitar don baki ɗaya yama rasa hasalin abinda ke damunsa. Idanunsa Lumshe zaka ɗauka ma barci yine, amma kawai yana sauraran bugun da zuciyarsa ke masa ne, saida ta ɗanna doorbell wajen sau uku jin shiru ne kuma ya sanya ta tura ɗakin kai tsaye, jin a buɗe ƙofar take kuwa ba ƙaramin sanyaya mata zuciya hakan yayi ba.
Kutsa kanta tayi cikin katafaren parlourn, wata iriyar ajiyar zuciya mai qarfi ta saki, jin wani daddaɗan ƙamshin perfumes da sukayi welcomin nata, Lumshe Idanunta tayi tare da buɗewa tana bin baki ɗaya parlourn da kallo, A nutse ta dubi bangaren damarta da kuma hagu ganin hanyoyin har biyu,kai tsaye ta nufi ɓangaren damarta domin tafi kyautata zaton nan ne ƙofar bedroom nashi take.
Nan ma Saida tayi noking doorbell ɗin still nan ɗin ma dai shiru, ita kuwa hakan yasa ta kutsa kanta cikin tsararren bedroom ɗin da kai tsaye zaka iya ƙiransa da aljannar duniya, domin ya haɗa komi da komae na buƙatun rayuwa.
Kwance luff ta hango shi saman Italian bed nashi, yana kwance ya nutse cikin lallausar katifar gadon dake shimfiɗe cikin wani tsimammen farin duvet ɗin daya masifar ƙawata gadon.
Ganin tayi wajen magana har uku ne bai amsa ta yasa Ahankali takai kanta gaban gadon.
Ƙasa takai dab da setin kansa, cikin wani irin murya mara amo ta furta,

"MY LEEEYO"

Tayi maganar tana sauke Mayun idonta saman kyakkyawar fuskarsa, yana jinta yayi banza da ita hasali ma juya kanshi yayi yana tsime akan lallausan trow pillown sa, kamar da icce take maganar ba tare da ya furta koda E bane. Cikin tsantsarn sauƙin da taji yana ɗibarta akansa ta kuma furta

"LEEEYO! Get up pls"

Tsimewa yayi bai kula taba cikin a Kasar zuciyarsa yaja ƙwafa, yana jin wani masifar haushinta na nemar halaka shi. Bakinta takai daidai setin bakinsa da nufin ta masa kiss 😘

Cikin hargitsatstsen sauti ya kotsa mata wata uwar razananniyar tsawar data kusan sumar da ita,
A kiÉ—ime a kuma gigice take shiga neman hanyar data shigo, tana samun hanyar wucewar kuwa ta fita da É—an gudunta ga wani kuka na kwace mata.

*Queen*

A daskare ta tsaya chak kamar wacce akayi freezing nata dan ko iya juyowa ba tayi ba, Wani rumtse idonta tayi for the moment tana sauraran bugun zuciyarta, sharrr kuma hawayen tashin hankali suka wanke samar kyakkyawar fuskarta,

A karo na biyu ta yaya jay ya kuma furta mata ”Ki haɗe duk wani abu naki da kika san na amfanin kine daga yanxun zuwa dare Fatima idan Allah ya kaimu"

"Yaya meyasa RAYUWA ta zaɓi yin watan gaririya dani ako wanne loqaci? Yaya meyasa RAYUWA take zuwar min da tarin ƙalubale maban banta!? Me ya sa? Meya me yasa hakan!?"
Ta ƙarashe maganar cikin wata irin raunatacciyar murya, tare da fashe wa da kuka irin mai taɓa zuciyar nan, wanda da kaji yadda ta qarashe maganar lallei zaka fashimci akwai abinda ke danƙare cikin zuciyarta, akwai kuma abinda yake matuƙar motsa mata zuciyar nata sai kuma taci gaba da faɗin.
"Yaya sai kace wacce kuka gaji dani da har zaku fara zancen barina gidan?,A barni mana na sai kamar nan da wata biyu loƙacin na gama warware wa, na sami lafiya ta yadda idan ya cuceni zan iya ramawa"

Sosae maganar karshen nata taso bashi dariyar amma saiya basar, yana zama gefenta, a tausashe ya shiga rarrashinta kuma yana faɗin, "In banda abinki Shalele taya kike woni zancen faɗa, keda zakije ki raya sunna ta Ma'aiki ki tsaya ki nutsu nasan kafff halayyar Aliey fiye da tunanin ki, idan har kikace ke kece, to kuwa shima zai ce miki shi shine, amma idan kika nutsu cikin ƙanƙanin loƙaci komai zai yi kamar ba'a taɓa yin saba, Kisa ma ranki yaƙinin cewar zakije bautar Ubangijii ne ta haka ne kaɗai Ubangijii zai duba al'amurranki kinji AUTAR UMMIE"
Acikin zuciyarta ta shiga faÉ—in wasu magungunan da ita kaÉ—ai tasan ma'anonin kayanta.

5:15pm
Wasu rantsatstsun narkakkun motoci guda biyu suka yi Park kofar gidan su queen. Suna gama daidaita parking su Oum Anum suka shiga fitowa cikin shiga ta kamala ta alfarma,wanda kallo É—aya zaka musu kasan cewar ba rainon 9j bane su domin sun fita daban.
Kuma akwai banbanci me tazara tsakanin mu dasu tazara ta kamar yaro ɗan shekaru biyar da kuma ɗan shekaru hamsi haka nisan tazarar dake ƙasar NIGERIA da kuma MADINA yake.
Chapter 32 · 0% Book details