Sashe 10
Ƙauna Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin matsanancin ɓacin rai yake sheƙe uban gudu tamkar ya tashi sama, gaba ɗaya zuciyarsa wani irin hautsinin bala'i take masa, wani irin raɗaɗi yakeji acen ƙasar zuciyarsa.
Kasancewar sa mutan mai tsananin zuciyar bala'i da ɗaukar abu da zafine ya sanya a take tsananin tashin hankali ya sashi tsats-tsafo da zufa, sabida yadda zuciyarsa ke bugawa da Masifaffen ƙarfi yayin da numfashinsa ke fusga tamkar zai bar ganganar jikinsa, cikin tsanananin tashin hankali da wani irin masifaffen juyi da kansa keyi ya ƙara matse kansa da hannu bibbiyu, da ƙyar ya iya taka birki daga gefen shimfiɗeɗen titin.
Wani irin tsanar yarinyar yake ji yana
ratsa ilahirin gangar jikinsa da kuma zuciyarsa baki É—aya, idanunsa sun juye sun kaÉ—a sunyi Jawur, kab ilahirin jikinsa rawa yake kar-kar-kar tamkar mazari haka jikinsa ya shiga kakkarwar cikin wani irin sauri zuciyarsa ke bugawa da kaso Cassa'in da tara cikin É—ari, tana mai wanzar da tsantsarn tsanar yarinyar. Samm shi mutum ne daya tsani rashin kamun kai, in banda rashin kamun kai taya zata masa uban wannan rungumar, duk da kuwa cewar yayantane jinin tane amma aibe kamata ta masa uban iriyar wannan rungumar ba.
A take zuciyarsa tayi masa wani irin nauyi, kafin yaji duk wata kafa ta jikinsa na sagewa, da ƙarfin masifa yaja motar ko ganin gabansa baya yi, ikon Allah ne kawai ya kaishi gida lafiya, wani irin mahaukacin hong daya danna kuwa kai kace baya a hayyacin sa ne. Su kansu soldier's ɗin dake tsaron get ɗin Saida suka tsorata da irin hong ɗin ɗaya ringa bugawa.
Cikin azama da rawar jiki suka buɗe get ɗin, yana qara cilla kansa asalin get ɗin gidan. A tsakiyar coumpaund ya faka motar ko gama daidaita tsayuwar motar baiyi ba haka ya fice a zuciye, idan yace yana raɗaɗi ko zafi zuciyarsa yake to yayi ƙarya. Wani irin bugu zuciyarsa ke masa bibbiyu ya shiga taka step na benen, da ƙarfi ya mirza handle na qofar yana tura kansa jikin babban parlourn sa, sa'ar sa ɗaya ma babu wanda ya haɗu dashi.
yana shiga falonsa ya maida ƙofar ya rufe, kana ya zame tare da zama aƙasan tiles na parlourn ya jingina bayansa da jikin ƙofan parlourn lokaci ɗaya yashiga kokuwa da numfashinsa dake ƙoƙarin ɗauke wa.
Atake ya shiga faɗin, “Allahumma Ajirni fii musibati wa'ahkifli lu Khairan minha , Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n, innalillahi wa'inna ilair raji'un"
Cikin wani irin tashin hankali ya cigaba da karanta duk wata adda'ar da tazo bakinsa.
wani irin zazzafan zazzaɓi mai zafin gaskene ya lulluɓe sa wanda gaba ɗaya ilahirin jikinsa ke rawa.
Samm Alie bai iya ɗaukar abu da zafi ba tsananta ma kansa da yayi ne ya sanya wannan zazzafan zazzaɓin rufe shi a take. Amma ɗan bala'in mai makon ya saduda saima wani irin turirin da zuciyarsa yaci gaba dayi. A haka wani irin wahalallen barci yazo yayi awon gaba dashi.
(Kada ku manta a baya nace ALIEY mutum ne da baiya kin abu ba, haka kuma bai iya son abu ba, idan ya tashi da dukkanin zuciyarsa,jikinsa dama komai nashi yake so ko ƙi, fatar kun fashimta dai🤗)
★★★
★★★
Haka al'amurra suka ci gaba da wakana tare da shuÉ—ewa tuni suka suka shiga watan azumi, inda suke gudanar da ibadarsu cikin kwanciyar hankali. Tuni an sanya ranar auren Fatima da Aliyu shureim É—inta inda za'a yi bikin su bayan sallah da sati biyu.
Kullum aliey tare da yaya jay yake shan ruwa ko a gidan ummie ko kuma gidan ammiey inda kullum kuma kunun gyaɗar aliey babu fashi, bayan yasha a gidan haka ummie zata kuma bashi wani ya tafi dashi. Shi yasa aliey yake tsananin ƙaunar ummien fiye da tunanin mai tunani, kuma duk xuwan da yake basa taɓa haɗuwa da Fatima kasancewar yawanci data gama ayyukanta gidansu Aliyunta take tafiyarta, kasancewar baba mariya ƙanwa take ga mahaifinta.
Yauma kamar kullum tun wajajen huɗu da mintoci aliey yake gidan, inda suke tare da yaya jay tare da Nurien a main Parlour na gidan baki ɗaya. Shi Alqur'ani mai girma ne a hannunsa yana raira kyakkyawar ƙira'arsa cikin daddaɗan sautin daya karaɗe parlourn, 6:34pm aka ƙira sallar magrib, rufe Alqur'anin yayi tare da ɗaurayo bakinsa dabinon ajjuwa ya ɗiba kwara uku yana ci, suma duk shima yaya jay dabinon yaci. Shi kuwa yaya Nurien tuba yaci tare da kankana, suna ida ci suka miƙe xuwa masjid, ko ka fin su dawo tuni ummie ta jere musu komai inda lafiyayyan kunun gyaɗar da teemah ta dama kafin ta tafi already ummie dama ta juye masa cikin plask na shayi in banda turiri da ƙamshim daɗi babu abinda yake tashi a cikin parlourn.
A jere suka shigo parlourn dukan su Abba yaya jay yaya Nurien sai kuma aliey dake gefen Abba inda da dukkan alamu wata maganar suke taunawa mai muhimmanci. Ummie da itama idar da sallar kenen ne ta amsa su, zama suka yi baki É—ayansu, a nutse aliey yaÉ—an É—ukar da kansa tare da cewa.
"Barka da shan ruwa ummiena"
"Barka alieyo ykk fatar kasha ruwa Lafiya kaima" tayi maganar cike da kulawa tana tura masa plask na kunun gyaÉ—ar, kasancewar tasan shine abinda yake fara sha, a nutsen sa yaja plask É—in gabansa cike da kamun kai tamkar wata mace, a junan su suka shiga gaisawa tare da yima kowansu Barka dashan ruwan.
Kurr idanun yaya Nurien akan aliey, wani irin lumshe ƙyawawan idanunsa yayi loƙacin daya kai cup na kunun gyaɗar nan bakinsa. Murmushine ya subcewa Nurien da sauri ya kawar da kansa, tare da zancen zuci acen cikin zuciyarsa ya shiga faɗin.
(Shi kuma babban yaya da irin abokin da Allah ya haɗa shi kenan, ga tsananin ƙyau tamkar ɗan ƙasar indiyawa ko kuma Balarabe nema oho?)
KafaÉ—unsa ya daga irin bai sani É—in nan ba. Daga kunun bai kuma cin komai ba har sallar isha'i, inda daga nan bai koma gidan ba daga masallacin suka wuce tare da jay, inda shine ya maida shi gidan tare da kunun gyaÉ—ar sa.
Daidai ta parkin na motar yayi a tare suka fice suna ƴar fira sama-sama kuma duka akan kasuwancin da alieyn ke taɓa ne, da sallama suka shiga qayataccen palon ammiey, ammiey dake zaune tare dasu Abba da kuma Irfan ne suka amsa sallamar, Amnah dake jikin Irfan ta sake shi tana yin kan jay aguje, tare da cewa, "oyoyo uncle jay"
"Oyoyo my princess Naaaaaa"
Shima ya gaɗa tare da cirata sama yana juyi da ita. Ido yarinyar ta haɗa da papieyn ta. Da ido ya mata alama data zo, maƙe kafaɗa tayi tare da masa Gwalo Ahankali tace masa. "Bana xuwa wurin ka tunda kaƙi bani New Mamie, zanbi uncle jay gidan sane kawai nifa"
Da sauri shida ammiey suka dubeta domin a tare maganar Amnan ta doke su, murmushin manya kawai Abba yayi yana barin parlourn bayan sun gaisa da jay. Zama yayi gefin ammiey cikin ladabi da kuma nutsuwa jay ya shiga gaida ammien. Amsa shi tayi tana tambayar shi ummiensa da kuma iyalansa. Cike da girmamawa yake bata amsa, sosai suka shiga fira ammien wanda yawanci akan alieyon ne. Irfan kuwa sai aikin kare É—an uwansa yake. Sai wajajen goma da rabi kana jay ya musu sallama yana komawa gida.
Wata iriyar soyayya mai qarfin gaske ta sake shiga tsakanin Aliyu shureim da queen teemah, sosae yake ririta abarsa yake ji da ita fiye da duk wani tunanin mai tunani.
Haka rayuwar taci gaba tafiya cikin aminci na Ubangijii har ana yau sauran kwanaki uku sallah, daidai sunkai azimi na ashirin da bakwai keñan, wanda wannan rana tazo musu da tsananin farin ciki, na samun aikin da Aliyu shureim yayi a babban birnin tarayyar Abuja. Haka familyn Aliyu dana Fatima suka cika da tsananin murnarn wannan aiki nashi, Fatima kusan zance tafi kowa murnarn samun wannan aikin nashi, domin dama samm taƙi jinin waƙar da yake yi, kasancewar ya fara in joining da mata suna harkar videon tare.
Ana ya gobe sallah again Alie ya kuma jibgewa gidan su jay uban kayayyakin sallah, tare da kuɗaɗe masu yawan gaske in banda albarka da addu'a babu abinda ummie da Abba suke bin alieyn dashi. Masallatan da gidajen marayun daya ɗauki nauyin sa kuwa acikin watan azumin Allah ne kaɗai yasan iyakar su. Banda taimakon mara ƙarfi da yake yi, hutu sosae ya ɗauka wannan karon domin shi kansa harya manta irin loƙacin daya ɗauka hutu kamar haka. Gaba ɗaya kowa ka gani sabgogin sa yake, babu ruwan wani da wani haka kowa ke gabatar da shirye-shiryen sallah, inda wasu ke ɗebo kansu da zafi, wasu kuwa zama kaga samm babu ruwansa da irin wannan ƙaryayyakin irin na masu manyan buruka.
Washe garin ranar aka tashi cikin annushuwa na ƙaramar salla, inda aka hau idi lafiya aka saƙƙo lafiya. A wani ɓangaren kuma zaka sami yara suna ta murnar fita yawon Barka da sallah, Suna zaune tamkar yadda suka saba suna firansu cikin tsantsar farin ciki, kallo ɗaya zaka musu kasan cewa Yes lallei ana zuba wata iriyar tsabtatacciyar soyayya a wurin nan. Wata narkyakkiyar Baƙar motar ce ƙiran Toyota Avalon,bugun 2024 ta sanyo kanta cikin gidan. Ji tayi kawai zuciyarta ya bada wani irin sautin bugu amma ta danne hakan, taƙi bari tsoranta muraran bayyanuwa. ALIEY dake driving na motar ne ya Parker a ɗan madaidaicin parking lot na gidan, Ammiey da Amnah ne suka fito domin dama duk shekara sukan ziyarci juna ne tsakanin ammien da kuma ummien. Shi kuwa cikin motar ya koma ran nan haɗe tare dayin reverse yaja motar yana barin gidan, kai tsaye ya shiga zaga garin Kano haka taka nas baima san abinda ya sanya shi haka ba.
Cikin farin ciki queen ta shiga gaida ammiey, cike da matsanancin ƙaunar teeman ammiey ta shiga amsa ta tare da ƴar tsokanarta ashe sun kusa shan biki,ita dai kunya ta hana ta yin magana sai Aliyu ne ke amsa ammien da ameern ameern.