← Book details Ƙauna Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 56

Sashe 19

Ƙauna Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

*ALIEY*
Ahankali ya É—ago kansa wanda ya kwashe sama da 30 min a zaunen da yake, fararen santala santalan sawayensa zube cikin swimming pool É—in.
Ahankali yake karkaÉ—a qafafunsa cikin ruwan. Tuni kaso mafi rinjaye na daga cikin kewa da kuma tunanin Sofeeynshi yaji yana nemar komai yana rasawa na daga cikin abinda ke damunsa.
Aƙalla yafi ƙarfin sama da 40 mints awurin yana jin sassaucin abinda ke son taso mashi, duk da yana qoqarin dannewa tsayin shekaru masu ɗan dama.Cikin yanayin dake bayyana tsantsarn nutsuwar da ƙaton beach ɗin ya bashi, sosea yaji wata iriyar nutsuwa tattare dashi, Idanunsa ya ɗan lumshe kana akasalance ya furta, ”Ya Rahman” loƙacin da yaji mararnsa yayi wani irin bala'in murɗa masa, yana ɗan taune jajayen lips nashi tare da dafe saman mararn. yasa cikin sauƙi zaka fashimci cewar mararsa ne ke ciwo, musamman yanda ya dafe kan marar da tafin hannunsa. sake lumshe tsumammun idanunsa yayi yayin da yaji wasu abubuwa na shirin kassara rayuwarsa, ahankali cikin daure ciwon da yakeji amarar ya taune lips nashi da ɗan ƙarfi tare da nutsa hannuwansa cikin tulin sumar dake kwance luff luff saman kansa.ya shiga chakudawa da duka hannuwansa.
Kafin a wahalce ya miƙe yana tangaɗi tamkar ɗan maye yana nufar parking space na cikin Beach ɗin, cikin sauri ɗaya daga cikin yaran shi ya buɗe masa wata narkyakkiyar motor ƙirar Lexus, wacce ta kasance Black mai Black ting.
Cikin sassarfa ya kutsa kansa cikin lafiyayyar motar. Babu ɓata loqaci ya faɗa cikin motorn yana yin reverse tare da fita aguje yana cilla hancin motar suuuuuu cikin tsakiyar titin na qasar Dubai.
Basu yi wota tafiya mai zurfi ba suka isa haÉ—aÉ—É—en hotel É—in da yayi boking,
ko gama daidaita parking drive'rn baiyi ba motorn Ya fito.
Qafafuwanshi ya fara zirowa kafin ya fito baki É—ayansa.
Eyephone nashi kawai ya iya ɗauka tare da nufar cikin haɗaɗɗen hotel ɗin,baki ɗaya hankalin mafi rinjayen fitsararrun ƴem matan da suke nan tamkar tsura re ne ya dawo kansa, cikin sauri da kuma ƙemƙemin ƴan matan ya kutsa kansa cikin jerin ɗakunan hotel ɗin. Babu zato babu tsammani yaji anyi wani irin faɗo masa jiki, tamkar wanda aka jona ma shocking yayi wata iriyar zabura, tare da juyowa a haukace yana wanke fitsaararriyar fuskar wacce ta iya haɗa ƙazamin jikinta da tsarkakken jikinsa. A zuciye yayi wani irin bala'in buga kanta da ƙarfin masifa.
Wata iriyar razananniyar ƙara sadra ya saki lokacin daya kuma yin cilli da ita, cikin bala'in zafin zuciya ya nufi part 0122 yana haɗe baki ɗaya abubuwansa Yana barin hotel ɗin baki ɗaya. Wannan ƙazamammiyar rayuwar yake ƙamata shi yasa sammm ya dena boking ko wanne hotel yafi gane yayi zamansa cikin jirgi Yayi rayuwarsa shi kaɗai.
A irin wannan masifaffan yanayin da yake ciki ne yaji ina sammm bazai iya ci gaba da zama a wannan ƙasar ba, baki ɗaya yaji komai da komai na sire mishi yana jin wata iriyar tsana da kuma ƙamatar banzaye masu banzan hali irin haka. Shi mutum ne daya kasance mai tsautstsauran ra'ayi, haka shi mutum ne da yake gudun duk wani laifi na saɓa ma mahaliccinsa, yana bin duk wasu ƙa'idojin dake cikin tsarin mahaliccinsa, yana gudun duk wani abu ko duk wani abin ƙi daya saɓama addinin Musulunci.
Hakan ya sanya cikin ƙankanin loƙaci ya buƙaci barin ƙasar duk kuwa da cewar sai nan da 6 days yake da tashi. Baki ɗaya yaji gida kawai yake da buƙatar komawa domin sammm zuciyarsa tana cikin wani irin masifar yanayi mara ƙyan gani, wanda a zahiri da za'a buɗe zuciyarsa da kuwa tabbas kun girgiza da ganin abubuwan dake tanƙare a cikin ta. A loƙacin 1:1pm na dare ne. Amma haka ya keta hazo yana barin kasar masu jajayen kunnuwan Nan, komae da yake cikin jirgin cikin ƙarfin hali da dakewa yake aiwatawa.haka yake sarrafa na'u'rorin jirgin.
Cikin talatainin dare jirgin yayi dirar mikiya a cikin ƙasar sa 9j wanda ya ɗan jima rabonsa da kasar. Domin kuwa ana sallacewa yabar 9j gashi yanxu wajajen watanni bakwai keñan da ƴan sati kai ake magana,kamar ko wanne loƙaci irfan ne yazo ya ɗauke sa, cikin tsaƙiyar daren.

********
Chapter 19 · 0% Book details