← Book details Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 53

Sashe 9

Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"
Tace"yana cikine, shine na futo"
Mamaki ya kama liman, yace "a a, ba mijin ki bane dama?"
Tace "Eh baba"
Liman yace "innalillahi wa Inna ilaihirraji'un" yayi Shiru kamar Yana nazarin wani abu, yadago ya kalleta yace "dazu yafadamin sunan ki Amina, 'yata Amina meyasa kuka Bari kuna cudanya da juna bayan kunsan bakuda aure?"
Amina tayi Shiru takasa bashi amsa, Shima Shiru yayi Yana tuno yanda yasamesu a bishiya rungume da juna, dakuma inda zai Fadi tatareshi yafada jikinta"
Kansa ya jinjina yace "taso kishiga d'akin talatu ku kwana tare"
Babu musu tashige d'akin matarsa, shikuma yayi d'akin da Asim yake ciki
Washe garima haka matar gidan tayi musu abubuwan daya dace, jikin Asim kuma da sauqi sosai ba kamar jiya ba,da yamma yasha magani ya kwanta daga Naan yayi bacci, d'akin ta leqa taga Yana bacci, tana juyowa zata koma wajan matar liman saiga liman dinma yashigo gidan, ya kalleta yace " 'yata zo zamuyi magana"
Binsa tayi abaya, suka shiga d'akin matarsa, ya kalleta sannan yafara mata magana cikin fahimta yace, "Amina"
Dago kanta tayi ta kalleshi, tunda suka hadu da mutumin yake mata kwarjini, tana ganinsa kamar mahaifinta, tace "Na'am baba"
Yace "Amina a'ina kuka hadu da wannan bawan Allah?"
"a garinmu, yajima acan" cewar Amina
Liman yace "to ko made a'ina kuka hadu na temaka muku Amina, nafarko jiya yafadamin Lagos zaku tafi, daga nan bai fadamin komai naku ba, Nima ban tambayeshi ba, Amina tafiyar ku tare ni inaganin kamar akwai hatsari a cikinta, tafiya zakuyi doguwa, kuma a hanyar nan bakusan abinda zai faru atsakanin Kuba, ko babu komai akwai shaid'an, yanayin dana ganku jiya ni kaina nayi tunanin mata da miji ne, saboda haka na yanke hukunci dazu dazun nan natara almajirai na dakuma maqotana nadaura miki aure kedashi " (
Dam!

Dam!

Gaban Amina yahau luguden faduwa, meyasa hakane?

Sai yaushe ne masifa zata Dena bibiyar rayuwarta?

Batasan lokacin data fashe da kuka ba, cikinKuka tace "innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, nashiga uku na, Dan girman Allah karaba auren nan, wallahi Allah banaso, ni banason shi, qaddarar dana Bari abaya ba ta isheni, bazan sake auren kowa ba"
"Amina banida ikon Raba muku aure, wannan Yana hannun mijin ki, bansan haka abin yake ba, da banyi gaggawar daura muku aure ba, amma inaso kisani, ni Allah baibani haihuwa ba, yanda kike kirana da suna baba Amina sainakeji kamar yata ce take kirana, ina jiye muku tsoron abinda zai Iya faruwa atsakanin kune shiyasa nayi muku auren, Amina tunda muka hadu daku naji kamar da yan'uwana nahadu, Dan Allah Karki watsamin qasa a'ido, shikuma dan'uwan tafiyar taki zan zauna dashi Gobe da safe in sanar dashi abinda nayi muku "
Gefen dankwalinta taja tana share hawaye dashi, kuka take sosai harda Jan zuciya, liman ya kalleta yace" kiyi hakuri Amina "
Ahankali ta daga kanta tace"to baba"
Liman yace"Allah yayi miki albarka, wannan sadakinki ne danayi miki shi, nera dubu goma "
Ya ajiye mata kudin agefenta sannan yafita daga d'akin, matarsa ce ta shigo d'akin tajanyota jikinta tana Bata hakuri, har dare yayi Amina Bata Dena zubar hawaye ba, idonta har zafi yake saboda kuka, kuma adaren matar liman ta rakata d'akin da Asim yake sannan tayi mata sallama, shikam baisan ma tashigo dakinba Yana bacci, ita kuwa zaune ta kwana
Sai gab da sallar Asuba taji bacci me dadi yafara daukar ta, Akan kunnanta wasu masallatan suka fara Kiran sallar farko, ihun dataji ne yasa tazabura cikin sauri tamiqe tsaye, kamar muryar matar liman takeji tana kuka, cikin sauri tabude kofar d'akin tafuto, qaran Bude kofar da tayi ne yafarkar da Asim daga bacci, Shima yanajin wannan kukan ya futo
Matar liman ta nufesu da gudu tana kuka kamar mahaukaciya, "Amina ku taimaka min, babu Malam yamutu" (
Amina tace "innalillahi wa Inna ilaihirraji'un" tafashe da kuka itama, yanzu liman yamutu?jiya jiya yazaunar da'ita yayi mata magana Akan aure amma yau harya mutu?

Anya kuwa batada nasaba da mutuwarsa?

Gabanta ya tsananta faduwa, idan kuwa hakan ya tabbata haqiqa data shiga ukunta, tazama masifa, tazama annoba kamar yanda su Inna suka fada, Asim kuwa qamewa yayi atsaye, mutuwar tatabashi sosai, Amina kuwa zama tayi a gaban gawar liman tana kuka, ga kukan jiya gana yau, hakan saiya haddasa mata ciwon kai, lokaci daya taji duniyar tafita daga ranta, fatanta daya shi ne Allah yasa itama ta mutu tahuta da wannan masifa, har a kayiwa liman sutura aka kaishi gidansa na gaskiya Amina Bata dawo normal ba
Tundaga mutuwar liman saita dawo Shiru Shiru, saitayi awanni batare da tayi magana ba, Bata jin dadin komai, Bata tunanin tanada Rabon hutawa awannan duniyar, tunani yazama abokin hirarta, Bata damu da magana ba, babbar damuwar ta ma shine wannan auren da liman ya daura mata, batasan Yaya makomar sa zata kasance, tayaya zata tunkareshi da wannan maganar?

Idan tafada masa ma qarshanta ya Musata, koba wannan Bama Bata fatan ace wani ya sake mutuwa Ata dalilin ta
Haka gidan yacika da 'yan'uwa, kuma tunda akai mutuwar Bata sake sakashi a'idonta ba, har akai kwana uku, a kayiwa liman sadakar uku data bakwai, yan'uwan matar suka shirya tafiya da' ita garinsu, gida yafara watsewa, Ana cikin haka kuwa Asim yashigo gidan bayan sun gaisa da 'yan tsirarun mutanan ya kalleta batare daya Kira sunan taba yace "kishirya mu tafi"
Itama batace masa komai ba haka tashige d'akin da'aka saukesu tahada kayanta waje daya tafuto dashi, lokacin da sukai sallama da matar liman saida kowa yazubar musu da qwalla,saboda kowa yayi tunanin yan'uwa ne, Amina tana kuka matar liman tana kuka sukai sallama suka tafi
A hanya ma Yana gaba tana binsa abaya har suka qarasa bakin titi, shine da kansa yafara tare musu Mota zuwa kano, amma duk motar daya tare idan yayi musu Bayanin bashida kudi saisuja motar su suqara gaba, sun Bata lokaci awajan sannan wani bawan Allah yadaukesu suka tafi, suna cikin tafiyama babu wanda yake yiwa dan'uwansa magana (
Amina kam idonta ta lumshe ma tana tunanin wannan baqar rayuwa Tata, abubuwa sun taru sunyi mata yawa, babu iyaye, babu asali, batasan ainashin takamaimai sunanta ba, ga wannan aure da liman ya daura musu, ta wacce hanya zata fada masa andaura musu aure?

Tayaya zata fada masa?Sunyi Nisa cikin tafiya taji ya tambayi Aron wayar direban dayake jansu, itade Bata Bude idonta ba Amma duk abinda yake yi tanaji, number mahafiyarsa yasa ka sannan yakira, saida wayar tayi ringing harta katse ba'a dauka ba, a lokacin kuwa mamy tana zaune da niyya taqi daukar wayar, tasan cewa bazai wuce masu yi mata jaje ba, a kullum haka take amsa kiransu harta fara gajiya,sake Kira yayi a Karo na biyu, Shima saida takusa katsewa sannan ta dauka tare da cikakkiyar sallama abakinta, Shiru yayi yakasa magana duk da kasancewar sa namiji qwalla yaji tana shirin zubo masa, mamy tasake cewa "Salamu alaikum"
Ahankali yace "Mamy"
lokaci daya mamy ta tashi tsaye, tace "Asim,Alhamdulillahi, Allah abin godia, dama nasan baka mutu ba, inaji a jikina zaka dawo gareni Asim"
Murmushin sa mai tsada yasaki yace "ban mutuba mamy, ina nan, mamy Amjad nasan sun kashe shi, kiyi hakuri mamy nakasa tseratar miki da danki" ya qarasa maganar Yana goge qwallar Idonsa
Tuni hawaye yagama wankewa mamy fuska, cikin kuka tace "Amjad Yana nan, yanzu hakama Yana bacci adakinsa, kana ina?"
"mamy kidena kuka mana, bagashi nadawo ba"
Hawayen idonta ta share cikin kuka tace "Allah yakaremin kai dana, Allah yarabaka da sharrin maqiya, kafadamin kana ina saina taho"
Ahankali yace "kano"
Duk firar dayake Amina tana jinsa, da alama da mahaifiyarsa yake magana, wani malulun abu ya tsaya mata awuya, shida yake da maahaifiya har ya kirata, amma ita ba tasan ma ko wacece itaba, batasan me matar tafada masa ba kawai de taji yace "to" daga nan ya kashe wayar yabawa direban, haka taci gaba da tunanin mafita
Har sukazo kano, Bata Dena tunanin mafitaba, tasaqa wannan ta kunce wannan
Kai tsaye ya cewa me motar yakaisu Airport, suna zuwa kuwa yayi masa godia, sannan yace yabashi account number dinsa a takarda, me motar kuwa jikinsa na rawa yarubuta yabashi, Ahankali tabude motar tafuto hannunta dauke da jakar bakko ta kayan ta
Kallanta Asim yayi, shida yake shirin tashin ta daga bacci ashe idonta biyu, me motar yaja abarsa yatafi, ahankli ta matsa kusa dashi ta kalleshi muryarta na rawa tace "Dan Allah...

Ina...

Inaso kakaini gidan Marayu"
Kallan qwayar idonta yayi, tunda yake arayuwarsa bayan mamy wannan ne Karon farko da yaji tausayin wata macen (
Itama dago kanta tayi ta kalleshi tana jiran taji amsar sa, amma Sai taga kawai zuba mata ido yayi Yana kallonta, cikin sauri tayi qasa da kanta, saboda ba qaramin kwarjini yayi mata ba, gashi kuma babban mutum
Dauke Idonsa yayi a kanta batare dayace mata uffan ba, Ajiyar zuciya yasaki shi kadai, tasake kallansa idonta na kawo ruwa tace "Dan Allah..."
sai sharrr hawaye suka zubo mata
Kallanta yasakeyi da tsananin mamaki, koda yaushe kuka kuka ko gajiya batayi?

Kafin yabata amsa yaji anyi masa wata irin runguma daga bayansa
Cikin tsananin murna Amjad yace "YAYA ASIM"
Sai a lokacin Amina taji sunansa, ASIM ta maimaita sunan abakinta
Murmushi yayi yace "Amjad yaushe zaka girma ne?"
Mamy ma ta qaraso wajan sa tajashi jikinta ta rungume shi, Shima tsamm ya rungume ta a jikinsa kamar za'a qwace masa ita
Ahankli ta zare jikinta tafara tattaba jikinsa, murdadden dantsan hannunsa ta riqe tace "babu de abinda yake damunka ko d'ana?"
Yace "babu Mamy, inaso mutafi gida akwai maganganun danake so muyi, ina daddy na da Baby da sauran yan gidan?"
"suna nan kalau Asim, basusan mun taho ba, nafiso kawai saide su ganka, amma kafin muje ya kamata kakira Maman INSAAF karkai laifi awajan ta, Dan nasan idan taji labari kadawo baka fada mataba har gida zatazo kuyi abinda kuka saba, kaima kasan sauran "
Daga mata kai yayi sannan ya kalli Amina data zama 'yar kallo yace "muje"
Sai a lokacin mamy da Amjad suka lura da'ita, Amjad yazuba mata ido Yana kallonta sannan yadubi yayan nasa yace
"Wow....

Yaya Asim wacece wannan?

She's Preety wallahi Yaya"
Wacece maman INSAAF? shin mahaifiyar insaaf tanada alaqa da Asim ne?
Chapter 9 · 0% Book details