Sashe 21
Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wacce yarinya?"
Dan qaramin tsaki yayi yace "Minal"
Amrah tadauki littafi da biro takaiwa Minal da suke falo itada mamy da widad, Amjad baya nan, tafada mata saqon Yaya Asim, sannan tajuya Takoma cikin daki
Gabanta ne yafara faduwa haka de ta nufi hanyar d'akin nasa duk jikinta yayi sanyi
Muhsin yadubi Asim bayan ya zauna acikin kujerun falon nasa launin Ash, yace "baban widad yagida ya ayyuka"
"Alhamdulillahi, ya iyali"
"normal, ina hajiya Lubna"
"taje gida, Bata nan"
"kace yau gwauro ne"
Kafin Asim yabashi amsa ta shigo falon, bakinta dauke da sallama, Muhsin ne ya amsa mata, tazauna a qasan kafet din falon tare bashi littafin tace "Yaya gashi"
Karba yayi ya ajiye a gabansa, sannna yafara yimata yan tambayoyi dangane da science,dakuma wasu na English tana bashi amsa kadan kadan, Muhsin Yana gefe Yana kallonsu
Da karatu yayi Nisa saita saita fara yin Shiru, yayi tambaya yayi tambaya yaji Shiru, gaba ya lura Bata fahimtar komai, haka yayi Shiru yaci gaba dayi mata Bayani, saida yagama tass sannan yafara jefo mata tambayoyi,da farko yace ta karanto masa part of speech, takawo guda bakwai kalau, Sai Ana qarshan ne maimakon tace interjection saitace injection, dariya takama Muhsin amma saiya danne beyiba, kawai qarfin hali yake gani irinna Asim, karatun yayi mata yawa a matsayin ta na wadda tayi karatu a qauye, kamata yayi yafara yimata da kadan kadan ahankali harta saba
Zuba mata ido yayi Yana kallonta, jiyake kamar ya ranqwashe mata kai, yace "gyara na qarshen dakika fada"
Amina tayi Shiru, gashi gabanta Sai faduwa yake, taqaici yakama Asim, ya kalli Muhsin yace "see, yarinyar danake cewa medicine zatayi itace takasa bani amsa"
Kafin Muhsin yabashi amsa yadaka mata tsawa "badake nake ba!!"
Zabura tayi Takoma gefe, jitake dukanta zaiyi, Ahankali murya na rawa tamkar mai shirin yin kuka tace "Yaya ni.... ni nafison...
Arabic"
Cikin sauri yace "what?
To bazaki Arabic dinba, boko zakiyi, kuma bokonma medicine"
Hawaye ne ya zubo daga idanuwanta, cikin kukan shagwaba tace "Allah nide Arabic nakeso"
Littafin ya wulla mata yace "Kinga tashi, tashi tashi kibani waje tun kafin na zaneki anan, ina fad'ar abinda nakeso kema kina fada, now.... band'ora hannu na ajikin kiba kin zauna kina min kuka, oya tashi kiban waje"
Hawayen idonta ta share, babu musu ta yunqura tatashi, ta dauki littafinta tafice daga falon
Kansa ya dafe da hannunsa
,ya tuna yanzu wannan takaicin Amjad zai dauka yakai gidansa, cikin damuwa yace "ka auri qaramar yarinya ma koka auri wahala"
Muhsin ya kwashe da dariya harda sunkuya wa, cikin haushi yajuya Yana kallonsa
Sharhi
Amnah El~Yaqoub
[2/13, 12:02 AM] El~Yaqoub: INSAAF
Writing by:Amnah El~Yaqoub
21&22
Like my page on Facebook
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493
"menene abin dariya anan?"
Muhsin ya qyaleshi saida yagama cin dariyarsa sannan ya kalleshi "nifa Ina ganin al'amarin ta kamar akwai aljannu aciki, why not kakaita wajan malamai, ayi mata ruqiyya ko za'a dace?"
"aljannu kuma Muhsin?"
"of course Asim, saboda babu yanda za'ayi ace dazaran yarinya tayi aure Sai miji yamutu, ai kaima kasan akwai alamar tambaya"
Jinjina kansa yayi "amma tayaya zan kaita wajan malamai Muhsin?
Kamar da cin fuska aciki..."
"bawani cin fuska Malam, ka taambayeta mana, ai zata iya sani, bazai iyu ace tanada aljannu amma Bata sani ba"
"OK, zanyi mata"
"yawwa ni ina ganin hakan zaifi"
*** ****** ***
Daga d'akin tafuto tana goge guntun hawayenta, Amrah tana falo tana kallo ita kadai.
Tadubeta "har kun gama karatun?"
"eh mungama Anty Amrah"
"to yanaga kina goge ido? kode dukanki yayi?"
Kafin tabata amsa Amjad ya shigo falon, ya kallesu yace "Amrah, kushirya muje musha ice cream"
Banza tayi ta rabu dashi, ya kalli yanda ta6ata fuskarta, shi kam mamy ta hadashi da aiki, takowa yayi yadawo dab'da'ita yazauna, ya kalleta yace " ai yanzu nadena cemiki Anty, tunda na kusa aure"
Amina ta kalleshi, ashe aure zaiyi shiyasa dazu suke maganar aure shida mamy, Amrah tace "to Ina ruwana kuma, saide kuje, nikam babu inda zani"
Murmushi yayi "haba Anty Amrah tah, Anty na takaina, aini dake kinsan Bama haka ko, nadena, I am sorry nadena"
Murmushi tasaki "to naji, tashi muje"
Tashi sukai, ta kalli Amina, " idan kin shirya muna jiranki amota "
Daga mata kai tayi, sannan tashige dakinsu tana tunanin wanne irin shiri kuma bayan na jikinta?
Haka de ta sauya shiga zuwa doguwar riga, takama gashin kanta ta daure, amma duk da haka bai dauru sosai ba,tashiga toilet Dasauri ta wanke fuskarta, Bata shafa komai ba, tayafa mayafin rigar tafuto daga d'akin
Tana futowa taga Widad a falon tace "Widad yaushe kuka dawo?Ina Momynki?"
Dariya Widad tayi, batare data Bata amsa ba, tazari mayafinta tafice daga falon da gudu
Amina ta dafe kanta tace "kai! yau nashigesu"
Cikin sauri tabita da gudu, gudun datake yasa gashin kanta dabai Gama dauruwa ba yake tsalle Yana kad'awa, alokacin su Asim suka futo daga d'akin sa shida Muhsin,suna kallonta tafita da gudu kai babu dankwali, Amina batama San sun futo ba, tana zuwa harabar gidan taga babu Widad, tajuya tana Zagaya gidan anan taci Karo da Anty Lubna tajuya bayan ta tana waya qasa-qasa, cak taja ta tsaya awajan gabanta yafara lugudan faduwa, Ahankali tajuya zata tafi saboda kada tajuyo ta ganta, saita tsinci muryarta tana cewa "Kayi hakuri, karka tonamin Asiri, zanyi abinda kasani, amma karkazo gidan aure na ka tonamin asiri, wallahi zanyi duk abinda ka Umar Eni dashi, to Amma fa matsalar Shima computer yake nema, bai ganta ba, bai San inda take ba, amma insha Allah inde ya ganta, zansa flash na dauke komai dayake ciki, duk takardun da suke ciki da komai da komai zanturo su zuwa flash din, Nima fa Abin Yana batamin rai, komai Insaaf komai Insaaf, nida nake matarsa baisa sunana kodaya acikin harkar dukiyar sa ba "
Kan Amina yayi dummm haka, saita fara jin kunnanta yanason daina aiki, Ahankali ta d'ora hannunta tadafe kanta
computer? to ai shaf ta manta computer tana wajan ta, dama nema yake?
Innalillah......
Yanzu Yaya zatayi?
Ta zalunceshi, ta sashi a halin tashin hankali Yana neman abunsa ta hanashi, to Amma ita Insaaf din ba'ita ce Anty Amrah tace mata yar gidan Anty Ishraqa bace?
To inhakane menene hadinta da Yaya Asim dazaisa sunan ta Akan komai, gashi har matarsa tana kishi akaan haka, yanzu daama Anty Lubna saboda kudi take zaune da Yaya Asim?
Kokuma saboda taga bayansa ne?
To ita da waye suke shirya wannan maqarqashiyar?
Dole tanada wanda yake Bata umarni, tunda koda yaushe awaya take jinta tana maganar, wani bala'in tausayin sa ya kama Amina, Anty Lubna kuwa sake gyara mayafin kanta tayi taci gaba da wayarta hankalinta kwance "wallahi Allah nasaka masa wannan maganin, wannan shegiyar yarinyar dayazo da'ita ne tamin Sanadin sa, amma da yanzu yaci, yanzu haka saboda ita nafasa kwana nadawo, Dan bansan meze faru ba, idan Bana nan,Kwanaki kamasu nayi cikin dare ita dashi, amma babu matsala kuwa idan nasaka masa gubar wadda zata karya garkuwar jikinsa? bazata kashe shi ba?
"
Amina na jin haka tajuya tabar wajan, wannan al'amarin yafi qarfin ta, Gara tafada masa kawai ya dauki mataki da kansa, Abin yafi karfin ta, yafi karfin tunanin ta, bazata iya ita kadai ba, dole ne tasameshi tafada masa gaskiyar abinda take ji awajan matarsa
Compound din gidan tadawo, anan taga Widad, tare dasu Asim da Muhsin, Sai wasa take da mayafinta
Qarasawa tayi duk hankalinta atashe, sakamakon maganar dataji su Lubna sunayi, banda gabanta dayake faduwa, ko sallama bata musu ba ta miqawa Widad hannu tace "Bani mayafin"
Widad tasaki murmushi takama qafar Asim tariqe shi gam tana buya tace "nide wasa zanyi dashi, bazan baki ba"
Asim da Muhsin duk suna kallonsu, haushi yaci zuciyar Asim, danme zata futo haka kanta babu dankwali, kowanne kare da doki suna kallonta
Amina kuwa bataga bacin ran nasa ba, saboda tashin hankalin datake ciki ma ya'isheta, hannu tasa zata kamo widad a jikinsa, yarinyar tasake komawa daya bangaren, itama tabita suka fara zagaye jikin Asim, yanda take kokarin kama yarinyar ne yasa jikinta Sai haduwa yake da nasa, yanajin yanda take goga masa abubuwanta a jikinsa, tana nema ta haddasa masa fitina kuma Yaga alama ita ko kadan kamar babu abinda hakan yake haifar mata, yarasa meyasa wani lokacin Bata tsoron ta'bashi kamar wata matarsa, ko tana tunanin shidin Amjad ne dayake shirin aurenta?kokuma saboda tayi mu'amular aure da mazaje dayawa ne?
Wata irin tsawa ya daka musu "Wai miye hakane?!!"
Cikin shagwaba tace "to Yaya kace ta bani mayafi na, su Anty Amrah jirana suke"
Kallonta yayi yace "ohhh itama Widad din kukan zaki mata?" ya qarasa maganar Yana nuna mata Widad, aikuwa Widad tana jin haka tasaki dariya
Yajuya yace "ke Bata abunta"
Babu musu Widad tabata, sannan tayi mata gwalo, hararar widad tayi tace "zan kamaki ne yarinya"
Sannan tawuce tabarsu awajan, ko sake kallonsu batayi ba, Asim yabi bayanta da kallo yace "gaskiya na yarda da maganar ka Muhsin, yarinyar nan tanada aljannu, kaduba kaga fa da widad take fada"
Muhsin yayi murmushi "wannan aiba aljannu bane Asim, harda yarinta ma, yarinta ce kawai, shiyasa tabiyewa yarinyar suke wata yarintar"
Widad ta hango Anty Lubna, tatafi da gudu zuwa wajan ta
*** ****** ***
Washe Gari lahdi, kowa Yana gida, haka ta tashi sukuku tana tunanin hanyar zata da fada masa maganar dataji Anty Lubna ta nayi awaya, tarasa yanda zatayi ta ganshi bare suyi maganar, Amrah ta kalleta "kalau kike kuwa Minal?"
"lafiya kalau Anty Amrah, mekika gani?"
"Naga kina ta tunani ne"
Murmushi ta qirqiro tace "a a, babu damuwa"
Wayar Amrah tahau qara, tana dubawa taga Yaya Asim ne yake Kira, dauka tayi tana sauraronsa, daga baya tace "to Yaya"
Ajiye wayar tayi tadubi Amina, tace "kije falo, Yaya yana kiranki"
Hamdala tayi a ranta, cikin sauri ta miqe tatafi, har hakan yabawa Amrah mamaki
Tana zuwa falon ta ganshi Yana karanta jarida, sallama tayi masa sannan ta zauna aqasa, jaridar ya ajiye sannan ya nuna mata gefensa "tashi ki zauna"
Ahankali tadago idanuwanta ta kalleshi tayaya zata zauna agefensa?