Sashe 13
Insaaf Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ransa abace yace"tambaya kike?"
Cikin fishi itama tace "eh, yar gidan uban waye?"
" 'yar gidan ubanki ce Lubna" (
Yana fadar haka ya dauki brief case dinsa yayi dakinsa
Juyawa tayi tana kallon sa, hawaye yazubo Akan fuskarta, tadora hannunta Akan qirjinta tace
"nizaka zaga Akan wannan yar iskar yarinyar?"
Tsugunnawa tayi awajan hannunta a kanta tana gunjin kuka, babu me Bata amsa, domin kuwa shide Asim baya nan, baqin ciki kamar yakashe ta, ada damuwar ta daya itace INSAAF, laptop dinsa insaaf, takardun komai insaaf, insaaf, tarasa gane wacece wannan tsinanniyar insaaf din (
Sotake taganta ido da ido ayita ta qare, to yanzu bayan insaaf din ga wata jarabar tasake samunta, bazata juri ganinsa da kowa ba, wallahi saide duk abinda zai faru ya faru a cikin gidan, cike da masifa ta tashi tabishi cikin d'akin
Labarin su :
Alhaji Abbas da Alhaji Abdullah iyayensu daya, su biyu iyayensu suka Haifa, Abdullah ne babba, Allah yahore masa kadarori dayawa, tun kafin suyi aure yasan zafin nema, har suka kai minzalin aure, da hankalin su iyayensu suka rasu, inda suka damqa amanar Abbas a hannun Abdallah, kuma Alhamdulillahi Abdullah yariqe dan'uwansa amana, raana daya sukai aure Allah ya azurta Abdullah da samun d'a namiji, suka samasa suna ASIM, sun Dade basu sake samun haihuwa ba, Sai bayan wasu shekaru masu yawa Allah ya sake azurta Abdullah da matarsa Hussaina haihuwar 'ya mace suka saka mata sunan mahaifiyar su, amma suna kiranta AMRAH.
har zuwa wannan lokacin Abbas bai samu haihuwa ba, Sai bayan shekara daya Allah yabashi d'a namiji ya sanya masa suna AMJAD
Bayan shekara daya Allah yayiwa matar Abbas Rasuwa, haka mamy tahada Amjad da Asim da Amrah duk ta riqesu, ta riqe Amjad tsakani da Allah, babu wanda zaice ba mamy ce ta haifeshi ba, Shima yashaqu da mamy sosai, kasancewar bai tashi tare da mahafiyarsa ba, Amrah tun tanajin haushi ya qwace mata fada awajan mamy harta zo ta daina, haka mamy zatayi ta rarrashinta tace ai qaninta ne, wannan rashin jituwar shine yake wanzuwa atsakanin su har yanzu,dayake mamy Bata son raini, Bata duba shekara daya Amrah ta bashi ba haka ta koya masa kiranta da Anty Amrah
Tundaga lokacin da matar Abbas ta rasu wato daddy bai sake aure ba, Sai bayan wasu shekaru yayi aure, Zaman nasu babu dadi da matar daga nan suka rabu, Rana daya Allah yayiwa Alhaji Abdullah rasuwa, wato mahaifin su Asim, mutuwar ta jijjigasu sosai, alokacin Asim yanada hankali sosai, yasan komai, suna zuwa makarantar kudi shida qannansa, alokacin ne yahadu da ISHRAQA,a jinsu daya ita dashi, suyi wasa tare, suje suyi lilo tare, hatta toilet din makaranta Asim ne yake raka Ishraqa
Yanda suka shaqu ne yasa yan a jinsu suke tunanin soyaiya suke, su kuma kwata kwata babu wannan a tsakanin su
yanda ake nuna wa su Asim gata Tona Ishraqa yawuce nan, babanta da kansa yake kawo ta makaranta, Sukuwa direban gidansu ne yake kawo su
Kusancinsu da Ishraqa ne yasa iyayenta suka San Iyayen sa, musanman mamy, tasan baban Ishraqa, suna mutunci sosai saboda alaqa dakuma shaquwar datake tsakanin yaransu, wani lokacin suna gaisawa idan tazo daukar su Asim in direban gidan baya Nan
Rana daya su Ishraqa suka koma Sudan wajan danginsu, wannan ne Sanadin rabuwarta da Asim, bayan yayi candy yanunawa Qanin baban sa wato daddy mahaifin Amjad ya nuna masa yanaso a saida kadarorin babansa ko kasuwanci ne yafara, mamy ma tagoyi bayansa, dasukaje wajan daddy da maganar saiyace za'a duba agani, daga nan bai sake tada maganar ba, lokacin jamb yayi, yaje yazana yasamu sakamako mai kyau, nanma yaje masa da maganar karatu, Sai daddy yace yayi hakuri zuwa wata shekarar saiya tafi, saboda yanzu yana harhada kudin gadon mahaifinsa ne
Suna jin haka basu yi masa musu ba, haka yayi hakuri da wannan jamb din, wata shekarar ya sake yin wata nanma yasamu sakamako mai kyau, alokacin dasukaiwa daddy maganar yace su saurareshi, mamy tana jin haka tasaida sarqarta tanema masa makarantar, Sai bayan yafara karatun ne sannan daddy yazo musu dawasu takardu daga cikin takardun mahaifin su Asim da Amrah, Bayan yatafi Asim yanunawa mamy takardun yace ai basu cikaba, mamaki ya kama mamy ganin yanda Allah ya horewa danta basira tun ba'aje ko'ina ba, ita kanta tasan takardun Bahaka sukeba,yariqe kaso mafi yawa aciki, takardun daya basu ko kwatar kudin mahaifin Asim basu yi ba, amma Sai tayi Shiru saboda gudun bacin rai
Rana daya daddy yacire Amrah da Amjad daga makarantar kudi yamai dasu ta government, Abin yayiwa mamy ciwo sosai, amma dataga ba Amrah kadai yayiwa manaqisa ba harda Dansa Amjad Saita share batun,kuma duk wannan abun dayake faruwa mamy bata taba nunawa Amjad komai ba, asalima ko kadan Amjad bai shaqu da mahaifinsa ba kamar yanda ya shaqu da mamy, ita kanta Amrah tun tana kishi dashi harta daina ta saduda
Tundaga lokacin Asim yafara janye jikinsa daga Daddy, ko shawara zaiyi saide yayi da mahaifiyarsa kawai,mamy dataga alamun haka awajan danta, saita nemi shawara awajan qawarta, kuma ta Bata shawara mai kyau, tundaga lokacin da qawarta tabata wannan shawarar tafara nunawa Asim yadena janye jikinsa daga na Daddy, shidin kamar uba yake awajan sa, qanin mahaifinsa ne, shikuma Yaro ne mai jin maganar mahaifiyar sa,tundaga lokacin bai sake nunawa Daddy komai ba, saide tun daga lokacin ya kasance Shiru Shiru,bashida buri illa ya taimaki Amrah dakuma Amjad da Allah yasa ka masa son Yaron a cikin zuciyarsa, kwatsam wata Rana Daddy ya nuna yanason auren mamy, alokacin tasake zuwa wajan qawarta neman shawara, qawarta tabata shawara ta Aureshi kodan saboda yaransu, alokacin da Asim yaji zancen auren qin amincewa yayi, saida tayi da gaske sannan ya yarda, cikin satin aka musu aure, lokacin tafiyar sa University tayi, wannan Karon Shima Daddy baiyi qasa a gwiwa ba ya taimaka wa Asim, kuma har lokacin daga mamy har Asim babu wanda yayiwa Daddy maganar kudin gadon su dayake hannunsa, Shima kuma bai basu ba, saide kuma duk wani haqqi dayake kansa na aure dakuma haqqin Yara Yana Sauke musu shi, tunda Asim ya shiga makaranta Lubna ta Dora ido akansa taji tana sonsa, ita irin matan nan ne masu budaddan ido, Kai tsaye qanin mahaifinta tayiwa maganar, kasancewarsa abokin Daddy , shikuma yasamu Daddy da batun, Kokadan Asim baya qaunar Lubna alokacin, amma haka yayiwa su Daddy biyaiya ya amince, kuma alokacin ne daddy ya basu mamaki, domin kuwa duka kadarorin maahaifinsu daya rage awajan sa ya dauko ya nuna musu, sannan yace tunda Asim ya girma ya karba yaci gaba da ajiyesu a hannun sa, mamy babu wanda yakai ta farin-ciki awannan lokacin, Asim Yana karbar takardun yaga ba original bane, haka yayi Shiru baice da mamy komai ba, saboda bayaso farin cikin datake ciki yayanke.
Bayan yagama makaranta a kayi bikinsu da Lubna, saide abin baqin cikin shine kamar yanda yake ganin ta mai budaddan ido hakane ta tabbata, budewar ta tayi yawan dayasa yagane cewa bai sameta a matsayin budurwa ba, wani yariga shi
Sarai yagane, itama
Tayi tunanin daya gane zaiyi mata magana, amma abin mamakin baice da'ita komai ba, tun tana dari dari harta sake,amma abinda Bata saniba shine abin Yana nan a cikin ransa, har yau Yana kallonta da wannan abun.
Asim yafara fafutukar neman aiki amma babu aiki, mamy ta sashi agaba tace ya saida filayensa dana Amrah yafara kasuwanci da kudin, bai nuna mata takardun wajan nasa fake bane haka ya amsa mata zai saida din, alokacin cikin ikon Allah yasamu aiki awani company suna biyansa albashi mai kyau, tundaga nan kuma yake ganin abubuwa arayuwarsa, sosai wasu mutanan suke neman rayuwar sa daga gefe, muddin yayi dare awajan aiki baidawo gida ba, to haka zaiga mutane suna bin bayansa, tun Yana waiwaye Yana qara sauri harya dawo gudu
Tun Ana masa abu a boye har ya kasance a nayi masa afili, kuma har yau baisan suwaye ba
Daddy ma dayaga abin yayi yawa, shida kansa Ya hanashi fita ko'ina, kuma hukuncin daya yanke din yayi wa kowa dadi
Haka ya hakura da aikinsa domin ceton ransa, adede lokacin su Ishraqa suka dawo Nigeria itada mijinta, Asim yayi murna sosai da ganin ta, itama haka, haka Suka zauna Yana Bata labari Kala Kala itama tana bashi,cikin labarin data bashi harda na aurenta bayan sunyi candy, saide abinda ya lura dashi shine kamar tana cikin damuwa amma kuma Bata sanar dashi ba, Shima bai takura mata da wannan tambayar ba, su Ishraqa sun dauki tsawon lokaci a Nigeria kafin suyi shiri zasu koma Sudan, alokacin ne suka dauki dukiya mai mutuqar Tarun yawa itada mijinta El Hameed suka damqawa Asim yaci gaba da juyata tunda Yana zaune agida babu aikin dayake
Alokcin dasuka Bawa Asim wannan dukiyar tsorata yayi, ganin kudin sunyi yawa, mamy da tayi Shiru tana kallon Ishraqa saita nuna musu cewa ai kudin yayi yawa, alokacin mijin Ishraqa yace musu susai kadarori dashi su ajiye, suma ba kudinsu bane kudin INSAAF ne
Daddy ma da yaji haka duk Sai suka bashi goyon baya, Alokcin Amrah da Amjad suma suna da hankali duk sunsan komaai, Asim ya karbi kudi yasiyo gidaje, filaye, daduk wasu abubuwan kadarori sannan yabude company dawani anan Lagos, bayan wasu shekaru Sai su Ishraqa suka dawo Lagos da zama gaba daya itada mijinta, Asim yanema musu gida mai mutuqar kyau kusa danasu gidan, kuma tsawon wannan lokacin Asim bai taba tambayar Ishraqa wacece INSAAF ba, abinda ya sani shine duk wani kudi dayasan na INSAAF ne Yana kiyayeshi, koda wasa baya taba kudinta, saide ribar dayake samu yake amfani da'ita, saboda kada ya shagala ne yasa hatta laptop dayake amfani da'ita ma wadda da kudinta aka siya bada riba ba yaje aka saka masa sunanta a jiki domin tadinga tuna tar dashi
Shi kansa baisan Yaya akai mamy take Kiran Ishraqa da maman INSAAF ba, kawai de yaji tana fada, yasan kuma bazai wuce a cikin hirarsu ta mata tasani ba, shide abinda ya sani shine Ishraqa bazata haifi wata yarinya ba kuma ace takasa sanar dashi, saide in ko yar dan'uwanta kokuma yar mijinta, amma cikin ransa shi kansa yanason sanin wacece insaaf, domin kuwa tun kafin ya ganta yaji a ransa cewa ita din tabbas ta daban ce.